Mar 06, 2016 19:14 UTC
  • karamin Sani kukumi-Amfanuwa Da Ni'imar Duniya(2)

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau minene Alakar anfanuwa da ni’imar da Allah  a duniya da kuma Ibadar Allah madaukakin sarki? Shin ni’imar Allah madaukakin sarki ya saukarwa bayinsa ta kan iya  kasancewa  taimako wajen gudanar da ibadar Allah madaukakin sarki?(masu  saurare abinda ake nufi da ni’imar duniya a nan dukiya , arzikin, sarauta, iko da sauransu wanda Allah madaukakin sarki ya horewa wasu bayinsa da su a nan duniya) wannan ita ce tambayar mu a yau, amma kafin amsa tambayar bari mu saurari wannan.


*****************************Musuc*******************************


Masu saurare kamar yadda shirin ya saba, a yau zai fara da littafin Allah mai tsarki wato Alkur’ani mai girma, a cikin suratu Muminun Aya ta 51 Allah madaukakin sarki ya ce :( Ya Ku Manzanni ku ci daga abubuwa Halal, kuma ku aikata aikin kwarai, lallai Ni,ga abinda kuke aikatawa,Masani ne) a cikin tafsiru Majma’ul  bayan  tafsirin wannan Aya an ruwaito hadisi daga Annabin rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, wannan hadisi ya shafi dukkanin mumunai inda ya ce:(hakika Allah madaukakin sarki tsarkakekke ne baya kuma karbar  wani aiki sai mai tsarki, kuma ba shakka Allah ta’ala ya umarci mumunai da abinda ya umarci mursalai) sannan sai ya karanto wannan Aya (Ya Ku Manzanni ku ci daga abubuwa Halal, kuma ku aikata aikin kwarai) sannan kuma ya karanto wannan Aya (Ya Ku Mumunai ku ci daga ababe na halal daga abinda muka arzutaku) a Ayar farko Allah madaukakin sarki ya hada anfanuwa da ni’imar duniya da aiyuka na kwarai, a Aya ta biyu kwa Allah madaukakin sarki ya hada anfanuwa da ni’imar duniya tare da godiya da kuma bautar Allah kamar yadda Ayar ta ce:(Ya ku wadanda suka yi Imani ku ci daga tsarkakan abubuwan da muka arzuta ku (da su) ku gode wa Allah idan kun kasance shi kadai kuke bauta wa) suratu Bakara Aya ta 172, masu saurare idan mu kayi nazari a kan ayoyin nan  guda  biyu za mu fahimci cewa duk ni’imar ubangijin da aka yi amfani da ita bisa godiyarsa ibada ce kuma a fili yake  godiyar Allah a aikace ita ce anfanuwar da ni’imar wajen aikata aiyuka na kwarai kuma yin hakan shine ma’anar Ibada.


A cikin suratu A’araf  aya ta 31 Allah madaukakin sarki ya ce: ( Ya ku diyan Adam ku riki kawarku a gurin ko wani masallaci, ku ci ku kuma sha, amma kada ku yi barna,lalle ne shi (Allah) ba ya son barna.) a wannan Aya Allah madaukakin sarki ya hada anfanuwa da ni’imarsa da  Ado, ci da sha ba tare da yin israfi ba sannan ya bayyana daya daga cikin alamar ibada wato masallaci, domin yin israfi wajen ado da cin abinci gami da sha ya kan shagartar  da bawa ga Ibada.Imam Kazim (a.s) ya ce (ku sanyawa  zukantanku  rabo  na duniya wajen basu  abinda suke bukata na halal da babu barna ko israfi a cikinsa ku yi dogaro da su wajen al’amuranku na Addini).


Shahararen malamin tafsirin nan  Ayashi ya ruwaito hadisi tare da sanadinsa,inda aka ce Imam hasan Mujtaba (a.s) ya kasance idan ya tashi yin salla ya kan saka mafi kyau daga cikin suturarsa, sai aka tambayeshi ya Dan Ma’aikin Allah (s.a.w) minene ya sanya kake saka mafi kyau daga cikin suturarka yayin da ka dauki niyar  Ibada, Imam (a.s) ya amsa da cewa  :(hakika Allah madaukakin sarki mai kyau ne kuma yana son mai kyau ina yin ado saboda Ubangijina domin shine ya ce:( ku riki kawarku  ko adonku a gurin ko wani masallaci) don  haka ni ke so in saka mafi kyau daga cikin suturata a lakacin da zan yi salla). Har ila yau a cikin Littafin Khisal an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:( hakika Allah madaukakin sarki mai kyau ne kuma yana son mai kyau sannan ya na son ya ga tasirin ni’imarsa a kan bayinsa). Wadannan hadisai guda biyu na shugaban muwahidai tare da Dansa shugaban samarin gidan Aljanna sun tabbatar mana da wata  Ni’imar Allah madaukakin sarki wato yin abinda Allah ke so da kuma tasirin bayyanar ni’imar sa a wajen bayinsa.


*************************Musuc*****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da littafin kafi na sikatu islam Kulaini, inda a cikinsa aka ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Imam sadik (a.s), wata rana  Imam(a.s)  ya hadu da ubad bn Kasir Albasari wanda ya kasance daya ne daga cikin shugabanin malumar dagutu, a lokacin Imam (a.s) na sanye da kyawawen sutturarsa , sai  Ubad ya tuhumesa a kan hakan, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa:Ya Ubad wanene ya haramta kawa ko  kuma kyawawen ababen ado  na Allah, wadanda ya hallita don bayinsa da kuma tsarkakku na daga arzikinsa? Hakika Allah madaukakin sarki idan  ya arzuta bawansa da ni’imarsa ya na son ya ga tasirinta a jikinsa hakan kuwa babu wani laifi, kaiconka Ya Ubad  hakika ni shashe ne daga jikin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kada ka cutar da ni).masu saurare wannan hadisi yayi ishara kan cewa amsar kiran  ubangiji shine bawa ya ni’imtu da ni’imar da Allah madaukakin sarki ya yi masa ma’ana ni’imar da aka basa ta hanyar halal a ga tasirinta a jikinsa. Kuma amsar kiran ubangiji yin da’a ne wanda kuma hakan shine  misdakin Ibada. Masu saurare da farko mun karanto hadisin dake bayyani kan tsarkakekken abu inda Ma’aikin Allah ke cewa:(hakika Allah madaukakin sarki tsarkakekke ne kuma ba ya karbar wani aiki idan ba tsarkakekke ba) domin haka Ma’aikin Allah (s.a.w) ke yi mana ishara bisa umarnin Allah madaukakin sarki na dukkanin abin ci da sha na mursalai da mumunai suka kasance tsarkaka, a cikin littafin usulu sittata ashara an ruwaito hadisi daga shugabanmu  Imam Bakir (a.s) ya ce:(duk wanda yak e son Allah ya tsarkake jikinsa, to kadda ya ci ko kuma ya sha wani abu idan ba tsarkakekke ba, domin Allah madaukakin sarki a littafinsa mai girma ya ce: (Ya Ku Manzanni ku ci daga abubuwa Halal, kuma ku aikata aikin kwarai, lallai Ni,ga abinda kuke aikatawa,Masani ne )


Masu saurare a karshe bari mu karanto muku wani Hadisi daga shugabanmu Imam Kazim (a.s) wanda aka ruwaito a cikin littafin Tuhuful Ukul, Imam (a.s) ya ce :( ku yi kokarin raba lokutanku zuwa gida hudu, lakacin Munajati wato na ganawa da Ubangiji, lokacin neman abinci,lokacin ganawa da ‘yan uwa da kuma wadanda kuka amince da su masu bayyana maku aibinku da gaya maku gaskiya da kuma lokacin kebewa da iyalanku), da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon koyi da irin wadannan kyawawen dabi’u, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.