Mar 06, 2016 19:15 UTC
  • karamin Sani kukumi-Mahimancin sanin Addini

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau ita ce minene mahimancin sanin Addini ga rayuwar dan Adam. Kafin amsar wannan tambaya bari mu saurare abinda aka yi mana tanadi a kan faifai


********************Musuc********************************


Kamar yadda shirin ya saba za mu fara da Ayoyin  littafin Allah mai tsarki wadanda suke bayyanin cewa sanin hukunce-hukuncen addini wata ni’imar ubangiji ce wacce ta ke kai bawa zuwa ga kamala tare da ceto shi daga duhun bata, A cikin suratu Al ‘imrana  Aya ta 164 Allah madaukakin sarki ya ce:(lalle ne hakika Allah ya yi babbar falala ga mumunai,yayin da ya aiko musu Manzo daga cikin su, yana karanta musu ayoyinsa, yana kuma tsarkake su, yana sanar da su  Littafi wato Alkur’ani  da kuma hikma,ko da yake sun kasance gabanin haka suna cikin bata mabayyani). Masu saurare sanin addini wani haske ne da yake budewa dan adam udanuwarsa  wajen gane hakikanin samuwa tare da yi masa jagora wajen isa ga hanya madaidaiciya ma’ana sanin addini shi ke tseratar da dan adam daga bata, a cikin suratu Ra’ad  Aya ta 16 Allah madaukakin sarki ya ce:(ka ce da su wanene Ubangijin samai da Kasai ? Ka ce Allah ne. ka ce(da su) Amma yaya kuka rike wasu iyayen giji ba shi ba suka zama masoya, wadanda ba sa mallakawa kansu wani amfani ba kuma haka ba sa turewa cuta ba? ka ce shin makaho da maigani suna daidaita? Ko kuma shin duhu da haske suna daidaita? Ko kun sanya wa Allah wasu abokan tarayya ne wadanda suka yi halitta kamar halittarsa, sai hallitun suka yi kama da juna a gare su? Ka ce Allah ne mai hallita komai, kuma shine madaukaki marinjayi) har ila yau a cikin suratu Ra’ad din Aya ta 19 Allah madaukakin sarki ya ce: (Yanzu wanda ya san cewa abin da aka saukar maka daga Ubangijinka gaskiya ne (zai zama) kamar wanda yake shi makaho ne. hakika ma’abota hankali ne kadai ke wa’anzutuwa) wannan Aya mai albarka ta yi isharar cewa ma’abota  cikakkun hankula  sune suke fahimtar wajibcin neman sanin ilimin Addini  kamar yadda wata Ayar ta daban ke tabbatar da hakan a cikin suratu Zumari Aya ta 9 Allah madaukakin sarki ya ce:(shin wanda yake ta biyayya a cikin sa’o’In dare yana sujada yana kuma tsayuwa, yana tsoron ranar lahira yana kuma kaunar rahamar Ubangijijnsa(zai yi daidai da wanda ba ya yi?) Ka ce “yanzu wadanda suke da sani za su yi daidai da wadanda bas u sani ba? ma’abota hankula hankula ne kawai suke tunanin haka), a cikin suratu An’ami Aya ta 50 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce (da su ) Ban ce da Ku taskokin Allah suna gurina ba.kuma ban ce da ku ni mala’ika ba ne,ba abin da nake bi face abin da ako yiwo wahayi zuwa gare ni. Ka ce (da su) “yanzu makaho da mai gani sa ko zama daidai? To me ya sa ba kwa tunani ne?) wannan Aya ta karshe ta yi kyakkyawar ishara da cewa kyakkyawen tunani shi ke shiryar da Dan Adam wajen cimma samun manifofinsa na cira, rabo da kuma gyara aiyukansu wajen neman sanin  addininsa.


****************************Musuc*******************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi dubi ne ga tafarkin  Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, hadisai da dama sun bayyana  neman ilimin addini a matsayin kofar rabauta da alkhairan duniya da Lahira kamar yadda Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya bayyana a riwayar da Limamen shiriya suka ruwaito wacce aka nakalto a cikin Littafin Raudatu Wa’izin, ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(shin ba ka san cewa ana bin umarnin Allah ne da ilimi ba,kuma ana bauta masa da ilimi ba, dukkanin alheri duniya da lahira na tare da ilimi, kuma duk sharrin duniya da lahira yana tattare da Jahilci).


A cikin littafin Tuhuful Ukul an ruwaito hadisi daga shugaban wasiyai Imam Ali (a.s) yayin da yake yiwa sahabinsa Kumail bn Ziyad wasiya ya ce:(Ya Kumail babu wani abu da za ka yi face kana bukatar sani a cikinsa), wannan  hadisi ya yi ishara da cewa duk wani motsi  ko kuma aiyukan da dan adam zai yi yana bukatar hukuncin addininsa a cikinsa , yin hakan shi zai sanya ya samu rabauta a rayuwarsa ta duniya da Lahira.a bangare guda kuma ya  kan korewa kansa Sharri jahilci da albarka sanin ilimin addini, kuma ta hanyarsa kawai zai samu cira daga dimuwa , da kuma bata shekarunsa a banza. An ruwaito hadisi a cikin littafin tuhuful Ukul daga shugabanmu  Imam Bakir (a.s) ya ce : (ka kare kanka daga duhun sharri zuwa hasken ilimi, ka yi amfani da hasken ilimi wajen gudanar da kyawawen aiyuka, kuma ka bayyana kyawawen aiyuka wajen kore girman gafala da kuma yin taka can can wajen gudanar da aiyukanka). Masu saurare ya kamata   dan adam ya tashi kuma ya dukufa wajen neman ilimin Addini domin amfanuwa da rayuwarsa kamar yadda ake bukata, shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce (ka kasance  tare da malumai ko kuma masu neman sani , kuma na haneka da ka  kasance  mai shagaltuwa da bin dadin duniya). Sanin ilimin addini shine mabudin Alkheri ga ko wani Mutune, kuma  ta hanyarsa ce Bawa yake samu kyakyawar rayuwa, kamar yadda shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik(a.s) ya yi ishara a cikin riwayar da shek Saduk ya kawo cikin Littafinsa mai  Amaly shek saduk:Imam (a.s) ya ce:(ku nemi ilimin addininku, domin nemam abu ne mai kyau,karantunsa na a matsayin tasbihi ga ubangiji, kuma Bahasi a cikinsa Jihadi, shi dan uwana ne yayin da Mutune ke cikin kadaita, abokine kuma yayin da Bawa ke shi kadai,makami ne ga makiya, kuma shi adone ga bayin Allah, Allah madaukakin sarki yak an daukaka wasu bayi ta sanadiyarsa sannan ya sanya su mafi alheri na shugabanin da ake koyi da kuma biyayya da su, domin shi ilimi rayuwar zukata ne, kuma ya na karfafa raunin jiki, da ilimi ake yiwa Ubangiji biyayya kuma da shi ake bauta masa).


Masu saurare, abinda za mu iya fahimta a wadannan ayoyi masu albarka da kuma hadisan iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka, shine  neman ilimi wajibi ko wani Mutune kuma ta hanyarsa Dan Adam yak an cimma duk wani Alheri da kuma rabo a duniya da Lahira, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon ci gaban da neman ilimi domin samun rabauta a rayuwar duniya da Lahira.


****************************Musuc*******************************


Masu saurare a nan za mu dakata