karamin Sani kukumi-Neman ilimin Addini
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin neman ilimin Addini da kuma matsayin a addini da raywar dan adam, tambayarmu ta yau ita ce a iya ne ya kamata mu dauki wannan ilimi ? sai a biyo mu domin jin amsa wannan tambaya.
*******************************musuc*****************************
Masu a wani littafi ne ya kamata mune ilimin addinin ba shakka ko wani mai hankali zai amsa da cewa mune wannan ilimi cikin littafin da babu gurbata na kari ko raki a cikinci kuma barn a ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa kuma wannan littafi shine Alkur’ani mai girma kamar yadda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Ya Ku ma’abota littafi, Hakika Manzonmu ya zo muku yana bayyana muku abu mai yawa daga abin da kuka kasance kuna boyewa daga Littafi (Attaura da Linjila)yana kuma rangwame daga abu mai yawa,Hakika haske ya zo muku daga Allah (shine ne Annabi) da kuma Alkur’ani mabayyani*Da shi Allah yake shiryar da wanda ya bi yardarsa zuwa ga hanyoyin kubuta da aminci, yak an fitar da su daga duffan (kafirci) zuwa hasken imani da izininsa, yake kuma shiryar da su zuwa tafarki madaidaici)suratu Ma’ida Aya ta 15 da kuma ta 16. Hakika masu saurare Alkur’ani mai girma shine farko da kuma asalin Littafin da duk wani dan Adam ya kamata ya nemi saninsa domin a cikinsa a kwai dukkanin buktun dan adam, saidai bayyaninsa yak an zuwa ne daga bakin Annabin Rahama Muhamad Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka domin shi ba ya wata magana face daga wajen Allah madaukakin sarki kamar wadannan Ayoyi ke cewa:(Allah yana rantsuwa da Tauraro yayin da ya fadi*Mutumunku bai bat aba kuma bai ketara haddi ba ko kuma kauce hanya ba*kuma ba ya yin magana bisa son zuciyarsa* ba wani abu ba ne shi face wahayi da aka yiwo(masa)*mai tsananin karfi ne ya sanar da shi*ma’abocin karfi da kwarjini,sa’anan ya daidaita* alhali kuwa yana a sararin sama mafi daukaka) suratu Najami daga Aya ta 1 zuwa ta 6, a cikin suratu nahl Aya ta 43 da kuma ta 44 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ba mu taba aiko (wasu Manzanni)ba a gabaninka in ban da mazaje wadanda muke yi wa wahayi. Sai ku tambayi ma’abota ilimi idan ya zama ba ku sani ba*Da Hujjoji bayannanu da Litattafai, mun kuma saukar maka da Alkur’ani don ka bayyana wa mutane abin da aka saukar musu don su yi tunani), har ila yau a cikin wannan Surat mai albarka Aya ta 63 da kuma ta 64 Allah madaukakin sarki ya ce:(Wallahi hakikia Mun aiko (manzanni) zuwa ga al’ummomin da suke gabaninka, sai shaidan ya kawata musu aiyukansu, kuma shi ne majibbincin al’amuransu a yau, kana kuma suna da (sakamakon azaba mai radadi*lallai ba Mu saukar Littafi ba a gareka ba , face ka bayyana musu abin da suka saba wa juna a cikinsa,kuma domin shiriya da Rahama ga Mutane wadanda suke yin Imani) domin haka, neman ilimin addinin Allah da kuma koyi da Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbatar a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka shi zai kasance kariya da kuma tsira daga kurbatar bin hanyar shaidan domin haka ne ma, Allah madaukakin sarki ya ce :(kuma duk abinda Manzo ya zo muku da shi ku rike shi, kuma duk abinda ya hane ku ku hanu,ku kuma ji tsoron Allah, Hakika Allah mai tsananin Ukuba ne) Suratu hashari Aya ta 7.
**********************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara bayyani ne kan shahararen hadisin na Saklain wanda aka ruwaito a cikin litattafan suna da shi’a tare da kyakkyawan sanadi inda a cikinsa Ma’aikin Allah (S.A.W) yayi wa Al’ummar musulmi tare da barmasu nauyaya guda biyu Littafin Allah shine Alkur’ani mai tsarki da kuma tafarkin wasiyansa 12 daga cikin gidan iyalan gidansa tsarkaka domin haka ne ma riko da wadannan nauyaya biyu shi ne zai kasance tsira daga Bata da kuma isa zuwa ga samun hakikanin ilimin addini da Allah madaukakin zai amince wa bayinsa da shi.a cikin littafin Jami’u Ahadisi Shai’a an ruwaito hadisi da jabir Ansari ya ce na cewa babban ja’afar imam Bakir (a.s) idan na ji wani hadisi daga gareku ina zan meda sanadinsa sai Imam (a.s) ya ce duk abinda na fada hakika na same shi daga babana kuma daga kakana shi Ma’aikin Allah (s.a.w) shi kuma daga Mala’ika jibrilu (a.s) shi kuma daga Allah madaukakin sarki kuma duk abinda zan fada bisa wannan sanadi ne,ya jabir Hadisi daya ga dauke shi daga mai gaskiya ya fiye maka alherin duniya da Lahira).
A cikin Littafin Rijjal wato littafin sanin wadanda suka ruwaito hadisi na Kashi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu imam sadik (a.s) ya cewa sahabansa (duk amsar da baku kan wata tambaya to daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ne babu wani abu da muke fada da ra’ayinmu).har ila yau a wata riwayar yace:(hadisi na, hadisin baba na ne, hadisin babana, hadisin kaka na ne, hadisin kakana hadisin Husain ne kuma hadisin Husain hadisin Hasan, hadisin Hasan, Hadisin Amiri mumunin Aliyu bn Abi Talib ne, hadisin amiru mumuni hadisin ma’aikin Allah (S.A.W), hadisin Ma’aikin Allah fadar Allah madaukakin sarki ne).masu karbar hadisi daga wasunsu yak an iya jefa dan adam ya ga wasu hadisan sun yi sabani da Alkur’ani mai tsarki da kuma hakikanin sunar Manzon Allah (s.a.w) kuma hakan yak an iya jefa Mutune cikin rudu ya kasa gane hakikanin ilimin Addinin Islama.a cikin littafin Basa’iru Darajat an ruwaito hadisi daga Muhamad bn hasan Safar daga Habli ya ce hakika wani mutune yace wa imam Bakir (a.s) ya dan Ma’aikin Allah hakika Hasanu Basri ya ce Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce duk wanda ya boye ilimi zai tashi ranar Alkiyama an yi masa lizzami da wuta, sai Imam (a.s) kai consa hakika ya yi wa Ma’aikin Allah karya to idan fadar Allah madaukakin Sarki(Kuma wani mutum mumuni wanda ya boye imaninsa daga mutanan fir’auna ya ce shin yanzu kwa kashe mutune don ya ce Allah ne Ubangijinsa) suratu Gafiri Aya ta 28, sai Imam (a.s) duk inda suke so su je amma wallahi ba za su sami ilimi ba in ba nan ba, ma’ana wajen iyalan gidan ma’aikin Allah) har ila yau Imam (a.s) ya cewa Salma bn kuhail da Hakam bn Utaibatu (gabas da yamma har abada ba za ku samu sahihin ilimi matukar ba daga wajenmu iyalan gidan Ma’aikin Allah ba).a cikin wannan Littafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika malumai magada Annabawa ne kuma Annabawa bas u bar gadon dirhami ko dinari ba sai dai sun bar gadon ilimi da hadisai duk wanda ya dauki wani abu daga cikinsa hakika ya samu babban rabo, sai ku dibi iliminku daga ina kuka dauke shi, idan kun dauki shi daga wajenmu iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka ,kun tsira daga duk wata dimuwa da kurbata gami da tawilin jahilai).har ila yau a wani hadisin kuwa, yayin da Iman (a.s) ke fassara fadar Allah madaukakin sarki(ba kuwa wanda ya fi bacewa kamar wanda ya bi son ransa ba tare da wata shiriya daga Allah ba) sai Imam (a.s) ya ce ma’ana wanda ya riki addininsa ba tare da shiriya shugabani daga shugabanin shiriya ba, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon bin yardarsa da kuma daukan ilimin ga shugabanin shiriya iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka.