May 09, 2017 17:36 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,A cikin Alkur'ani Allah tabaraka wa ta'ala ya ambata cewa Hakika Allah ya aiko cikamakin Annabawa domin bayyana Addinin Gaskiya a kan dukkanin Addinai, ta yaya zai kasance hakan, alhali Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya rasu kuma musulinci bai yi galaba a kan dukkanin Addinai ba?kafin amsar tambayar sai a dakace mu da wannan.

*********************Musuc*************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, Hakika wannan wa'adi na Allah ya zo cikin Alku'ani mai girma a wurare guda uku, na farko a cikin Suratu Tauba, inda Allah madaukaki sarki ya ce:(Suna So ne su dusashe hasken Allah da bajunansu, Allah kuwa ba zai yarda ba sai Ya cika hashensa ko da kuwa Kafirai sun ki* Shi ne wanda ya aiko Manzonsa da shiriya da kuma Addini na gaskiya don ya dora shi a kan dukkanin Addini,ko da kuwa mushrikai sun ki) suratu Tauba Aya ta 32 da 33.Hakika wannan alkawari ya zo a matsayin yin Bara'a ga Mushrikai na tsibirin kasashen Larabawa bayan bude garin Makka da kuma kafuwar Daular Musulinci ta Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah ya tabbata gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, da kuma umarnin amsar haraji daga wajen Ahlil-Kitab Yahudu da Nasara, wuri na biyu kuma it ace Ayar da aka saukar kafin saukar kafin wannan Aya wato a yayin sulhun Hudaibiya, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Hakika Allah ya gaskata wa Manzonsa gaskiyar mafarkin cewa lallai za ku shiga masallacin Harami,Idan Allah ya so,(kuma)amintattu masu askakken kawunanku masu kuma saisayen kanku ba kwa tsoron (komai) sannan ya san abin da ba ku sani ba sai Ya sanya budi makusanci, koma bayan wancan*Shi ne Wanda ya aiko manzonsa da shiriya da kuma addinin gaskiya don ya dora shi a kan addini dukansa.Allah kuwa ya isa mai Shaida) Suratu Fatahi Aya ta 27 da kuma ta 28., wuri na uku kuma sune Ayoyin da suka kama da da Ayoyin da suka gabata na cikin Suratu Tauba, yayin da Allah madaukakin sarki yake bawa Mumunai karfin gwiwa wajen zuwa Jihadi a Yakin Uhudu, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Suna nufin su disashe hasken Allah da bakunansu, Allah kuwa zai cika haskensa ko da kuma kafirai ba sa So* Shi ne wanda ya aiko manzansa da Shiriya da kuma Addinin gaskiya don ya rinjayar da Shi a kan addini dukkansa Ko da kuwa mushrikai sun ki (haka)). To a nan mi za mu fahimta daga wadannan Nassosi na Alkur'ani mai girma dangane da amsar tambayarmu?Hakika Masu saurare idan muka yi Nazari da kyau dangane da wadannan Nassosi masu albarka da kuma musababin saukar su za mu samu amsar tambayarmu da cewa bayyanar Addinin Annabi Muhamdu (s.a.w.a) bisa sauran Addini wani bangare ne na wa'adin Ubangiji na cika haskensa, ma'ana cika Ni'imarsa wajen wanzar da dalilan Shiriya ga Talikai, kuma wannan Al'amari ya nada alaka da rayuwar Annabi Muhamadu(s.a.w.a) da kuma abinda Allah madaukakin sarki ya tabbatar a hanun sa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka daga Nasarori.shi h kuma hakan na a matsayin matakin farko na budin kusa, kamar yadda ya zo cikin Suratu Fatahi, kuma Budin kusa na a matsayin mataki na cikekkiyar nasarar Ubangiji da kuma tabbatar da alkawarin Ubangiji, Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya shaida wannan Wa'adi na Ubangiji a Yakin Uhudu.Hakika cikin Tafsirin Ayyashi an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) y ace:(yayin da aka ci musulmi da yaki a Uhudu, Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya yi kira yana mai cewa Hakika Allah ya yi mini alkawari zai bayyana Addini ne a kan dukkanin addini, sai wasu daga Munafikai suka ce bayan an ci mu da yaki yanzu kuma ka ke masa Izgili). Wa'iyazu billah.

*********************Musuc****************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo maka kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, idan muka koma  hasken Shiriya na biyu wato tafarkin Iyalan gidan Anabta tsarkaka za mu samu Nassosi da dama da suke bayyani dangane da wannan alkawarin gaskiya na Ubangiji da zai  kasance a zamanin bayyanar cikamakin  wasiyan Annabi Muhamad (s.a.w.a) wato Imami na 12 daga cikin iyalan gidan Anabta Imam Mahdi wanda ake jira Allah ya gaggauta bayyanarsa. Misali cikin Tafsiril-Ayyashi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) yayin da yake tafsirin fadar Allah madaukakin sarki (don ya rinjayar da Shi a kan addini dukkansa Ko da kuwa mushrikai sun ki (haka)) sai ya ce zai kasance babu wanda za yi saura face wadanda suka tabbatar da wulayar Annabi Muhamadu (s.a.w.a) kuma Allah ya bayyana su a Raja'a), har ila yau an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) yayin da yake fassara Ayar  da ta gabata y ace:(Idan Imam Mahadi (a.s) ya bayyana babu wani Mushriki ga Allah mai girma da zai saura face ya bayyana kiyayyarsa a zuhurinsa), Shekh Sharaf-Husaini cikin Littafin Ta'awulin Ayyat ya ruwaito wani Hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) yayin da ya karanta Ayar da ta gabata sai ya ce:( Shin hakan zai bayyana ? bari Na rantse da wanda rai na ke hanunka, har lokacin da zai sora babu wani gari da ba a ambaton Kalmar shahada ba dare da rana wato fadar cewa Na shaida babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah kuma Muhamdu Ma'aikin Allah ne) da wannan ma'ana aka ruwaito Hadisi daga Mujahid daga ibn Abas, kuma bayan Hakan, Hafiz Kanji Ashafi'I cikin Littafin Albayan, ya ruwaito hadisi daga Saeed bn Jubair dangane da tafsirin Aya da ta gabata ya ce:(Shi ne Mahdi daya zuriyar Fatima diyar Ma'aikin Allah (s.a).

Masu Saurare takaicecciyar amsar da za mu iya fahimta daga wadannan Ayoyi masu girma da Hadisan da suka gabata shi ne Hakika Alkawari na bayyanae Cikamakin Annabawa (s.a.w.a) da kuma Addinin san a gaskiya a kan dukkanin Addini ya tabbatu a zamanin rayuwar sa dake kuma a matsayin fuskar fatahi na kusa, wanda ya fara domin cimma kamilin wa'adi ko alkawarin da Allah madaukakin sarki ya yi wa Annabinsa, kuma wannan kamilin wa'adi yana tabbatuwa ne ta hanyar wulayar wasiyansa 12 daga na farkon su Imam Ali har zuwa cikamakin su Imam Mahdi da ake jira Allah ya gaggauta bayyanarsa amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya, Hakika Musulinci zai bayyana cikin ko wata Alkarya a yayin bayyanarsa(a.s).

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.