Mar 06, 2016 19:18 UTC
  • karamin Sani kukumi-Hankali da kuma matsayinsa a rayuwar dan adam

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayarmu ta yau ita ce minene hankali da kuma matsayinsa a rayuwar dan adam? Sai abi yomu sanu a hankali domin jim amsar wannan tambaya.


***********************Musuc*************************


Masu saurare, hakika wannan tambaya tanada mahimancin gaske, domin samun amsar  wannan tambaya za ta taimaka mana sosai wajen gane hanyar  shiriya da kuma ta bata, har ila yau zai taimaka mana wajen gane tunani mai kyau da kuma wasawasin shaidan,kamar yadda shirin ya saba zai fara da Littafin Allah wato Alkur’ani mai tsarki,a cikin Suratu Bakara Aya ta 242 Allah madaukakin sarki ya ce:(kamar haka Allah yake bayyana muku ayoyinsa don ku hankalta) a cikin suratu Ra’ad aya ta 4 Allah madaukakin sarki ya ce:(hakika a game da wannan a kwai ayoyi ga mutanen da suke da hankali) har ila ya a cikin surat mai albarka aya ta 19 Allah madaukakin sarki ya ce:(hakika ma’abota hankali ne kadai ke wa’azantuwa) masu saurare idan muka yi nazari ga wadannan Ayoyi masu albarka da ma makamatansu wadanda suke bayyani kan mahimancin amfani da hankali a cikin alkur’ani mai girma za mu fahimci cewa  shi hankali wani karfi ne da Allah madaukaki sarki ya sanya a cikin fitirar dan adam domin ya yi amfani da shi wajen gano gaskiya da kuma rarrabe ta da karya. Kuma ta hanyarsa kawai Dan adam zai iya samun sanin da kuma  gaskiyar da yake bukata a rayuwarsa da kuma bin hanyar da za ta kaishi ga kamala,   wannan shine ma’anar hankali  kamar yadda littatafan sanin Yaren   larabci  suka bayyana cewa ma’anar hankaliriko da wani abu. a cikin littafin Awalil Aly an ruwaito hadisi daga shugaban halittu muhamad dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa (hankali wani haske ne da Allah madaukakin sarki ya hallitawa mutune kuma ya sanya shi yake haskaka zukata domin gane banbancin abinda ake gani a zahiri da wanda yake boye) har ila yau a cikin wata riwayar Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce :(hankali haske ne a cikin zukata ana banbance  tsakanin gaskiya da karya da shi).har ila yau Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce:(misalin hankali a cikin zuciya kamar misalin fitula ce a tsakiyar gida). Masu saurare, hakika hankali wata kauta ce da Allah madaukakin sarki ya baiwa bayinsa saboda irin soyayyar da yake yi masu, domin haka  ya hore masu  na’uar mai karfi wacce za su iya bantata karya da gaskiya kuma su fahimci hanyar da ta fi dacewa da su), a cikin littafin Awalil Aly an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa ( hankali kyauta ce daga Allah madaukakin sarki) har ila yau an ruwaito wani hadisi daga iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka cewa ya zo a cikin sunanu  nabiyullahi Idrisa (a.s) ya ce :( hakika Allah madaukakin da ya so bayinsa sai ya hore masu hankali sannan ya kebantar da Ruhul Kudus ga Annabawansa da waliyansa)


A cikin littafin gurarul Hikam an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(idan Allah madaukakin sarki ya nufi bawansa da Alheri sai yah ore masa hankali da kuma aiki madaidaici, hakika duk wanda Allah madaukakin sarki ya arzuta shi da hankali mai karfi da kuma aiki madaidaici  ba shakka ya bayyana ni’ima a gareshi kuma ya girmama kyautatawa a gareshi) a cikin littafin Khisal an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir(a.s) ya ce (ba a bautawa Allah da komai ba wanda ya fi da hankali) har ila yau a wata riwayar da aka ruwaito daga gareshi cikin littafin Tuhuful ukul ya ce :( babu wata musiba a duniya wacce tafi rashin hankali), a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Rida (a.s) ya ce:(abokin ko wani Mutune hankalinsa kuma makiyinsa  shine jahilci), a cikin littafin Ilalu Sara’I’I an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce:(gimshikin ko wani dan Adam hankali ne, da hankali zai cimma kamala kuma shi hankali hujjar dan adam ce kuma mabudin al’amuransa ne)


***********************Musuc*************************


 Masu saurare barkanmu da sake saduwa ci gaban shirin zai fara da littafin Kafi na sikkatu Islam Kulaini, A cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s), wannan hadisi shahararen hadisi ne wanda aka fi saninsa da hadisin Rundunar hankali da jahilci  a kansa Imam Khumaini (R T A) ya wallafa littafi guda inda ya yi sharhi a kansa ga wani bangare na wannan hadisi, imam (a.s) ya ce:( ku sani cewa hankali da rundunarsa da kuma jahilici da rundunarsa za ku shiryu, hakika Allah madaukakin sarki ya halicci hankali kuma shine farko abinda ya hallita daga ruhi na damar Al’arshi daga cikn haskensa, sannan yace masa juwa baya sai ya juwa, ya kuma cewa masa ya juwo gaba sai ya juyo, sai Allah madaukakin sarki ya ce na halicceka hallita mai girma kuma na girmama ka ga dukkanin halittu na).masu saurare a wannan hadisi za mu fahimci cewa hankali shine musababin girmama dan adam a kan sauren halittu, kuma shine hujjar boye ga Allah a kan bayinsa, ma’ana hankali zai kasance hujja ga Allah madaukakin sarki ga bayinsa domin ya  hore masu shine don su banbance karya da gaskiya  kuma shi hankali na’urar shiriya ce.


A cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu imam kazim (a.s) na cewa:(hakika Allah madaukakin sarki ya nada hujjoji guda biyu a kan bayinsa , hujjar Zahiri da ta badini, hujjar zahiri ita ce aiko manzanni da Annabawa da kuma shugabanin shiriya iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka, hujjar badini shine hankali da ya horewa bayinsa da shi ) har ila yau a cikin littafin Kafin an ruwaito Hadisi daga Imam Sadik(a.s)  yayin da yake amsa tambayar minene hankali sai ya ce:( hankali shine wanda aka bautawa Allah mai rahama da shi kuma aka samu Aljanna da shi), har ila yau a cikin littafin Kafi an ruwaito wani hadisi inda a cikinsa aka ce wani malami kuma masanin adabin larabci mai suna ibnu Sukait Al’ahwazi ya tambayi Imam Hadi (a.s) minie hujja  kan hallitu a yau? Sai Imam (a.s) ya masa masa da cewa :( hankali shike gane mai gaskiya ga Allah sai ya gasgantar da shi mai karya ya karyatar da shi). Daga karshe masu saurare hadisan iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka suna shiryar da mu cewa abinda ke karfafa hasken hankali gad an adam shine intar da kai daga kason sha’awa da kuma fishi da dukkanin nau’o’insa.Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce :(ka yaki sha’awarka kuma ka yi galaba a kan fishinka, sannan ka sabawa muguwar Al’adarka sai  zuciyarka ta tsarkaka kuma hankalin ya cika kuma ka cika ladan ubangijinka) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yakar sha’awarmu da kuma munanan halayanmu tare da rinjawar zuciya wajen aikata abinda bai dace ba a yayin muka yi fishi don kirman Ma’aikin Allah tsira da amincin  Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.


**************Musuc***********************


Masu saurare a nan za mu dakata ganin lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe sai kuma a maku nag aba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala ni da shirya kuma