karamin Sani kukumi-Rawar da Hankali ke takawa
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin hankali da matsayinsa a rayuwar dan adam, tmabayarmu ta yau kwa ita ce wata raw ace hankali ke takawa wajen samun sanin addinin da kuma sanin Allah madaukakin sarki? Amma kafin mu koma ga nauyaya biyu domin samun amsar wannan tambaya bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai
*********************Musuc****************************
Masu saurare kamar yadda shirin ya saba za mu fara da nauyi na farko wata Alkur’ani mai tsarki , a cikin suratu Rumu daga Aya ta 28 zuwa 30 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya buga muku misali daga kawunanku, shin kuna da wasu abokan tarayya daga bayinku da hannayenku suka mallaka game da abin da Muka arzutaku da (shi), ku da su ku zama daidai kuke game da wannan, kuna kuma jin tsoron su kamar yanda kuke tsoron junanku? Kamar haka muke rarrabe ayoyin(filla-filla) ga mutanen da suke hankalta*Ba haka ba ne,wadanda suka yi zalunci dai sun bi son ransu ne ba tare da wani ilimi ba, to wane ne zai shiryar da wanda Allah ya batar? Kuma ba su da wani macecci* sannan kuma ka tsayar da fuskarka ga Addini madaidaici (wanda shi ne) dabi’ar da Allah ya halicci mutane a kai. Ba wani canji ga addinin Allah. Wannan shi ne, addini mikekke, sai dai kuma yawaicin mutane ba su san (haka) ba).masu saurare idan muka yi nazari dangane da wadannan ayoyi masu albarka, za mu fahimci ababe guda uku dangane da matsayin hankali a wajen sanin addini, abu na farko dai shine fitirar dan adam ita ce ke aifar da hankali na gari ma’ana asalin halittar mutune domin sanin Allah madaukakin sarki, kuma dogaro da tunani mai kyau a cikin ayoyinsa da kuma halitunsa na zahiri wanda dan adam ke gani a bayan kasa,abu na biyu shine son zuciya asalinsa jahilci ne kuma shike lullube hankalin mutune ya kasa gane gaskiya da kuma sanin hakikanin ilimin Addini wanda zai kai dan Adam zuwa ga Kamala. Abu na uku shine hankali shi ke gane a inane Dan adam ya kamata ya dauki ilimin addininsa, kuma a cikin wasu littatafai ne ba shakka ko wani tunani mai kyau zai koma ne zuwa ga Alkur’ani mai tsarki wanda gurbata na raki ko kari ba ta zuwa masa kuma saukekke ne shi daga ubangijin Talikai sai kuma bayyanan Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.
Masu saurare bayan wannan amsa ta Kur’ani mai girma , an ruwaito hadisan da dama daga iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka wadanda suke bayyanin cewa ma’anar fitirar da Allah madaukakin sarki ya ambato cikin littafinsa mai tsarki shine sanin addinin islama, addinin gaskiya da kuma tauhidi da wailaya ma’ana biyayya ga shugabanin iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka.a cikin littafin Mahasin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yayin da yake fassara ayar da ta gabata ya ce :(ya haliccesu a kan saninsa lalle shine ubangijinsu, kuma ba dan haka ba, da ba za su san cewa wanene ubangijinsu, yayin da aka tambayesu wanene ubangijinsu da kuma mai arzutar da su) har ila yau a cikin Littafin Basa’iru Darajat an ruwaito hadisi daga iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka a yayin da suke fassara Ayar da ta gabata inda suka ce :(an halicce su bisa Tauhidi da kuma cewa Muhamad Ma’aikin Allah, Aliyu bn abi talib kuma shugaban mumunai ne,amincin Allah ya tabbata a garesu tare da iyalan gidansu tsarkaka har zuwa ranar Alkiyama).
**************************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da Littafin Kafi, a cikin Littafin Kafi na shek Kulaini an ruwaito hadisi Zuraratu bn A’ayan daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) na cewa:(madaidaiciyar hanyar da Allah madaukakin sarki ya halarci mutane a kanta ita ce sanin tauhidi) sai Zurara ya tambayi imam (a.s) minene ma’anar fadar Allah madaukakin sarki :( kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka ya fiddo zuriyar Dan adam daga Tsatsonsu, ya kuma sa su suka yi wa kanku shaida, (ya ce da su) Yanzu ba ni ba ne ubangijinku ba? sai suka ce Ba ja, (kai ne Ubangijinmu), mun shaida (mun yi haka ne) don kada ku ce a ranar Alkiyama Hakika Mu ba mu da masaniya da wannan) suratu A’arafi Aya ta 172 sai imam (a.s) ya ce aka fitar da zuriyar Annabi Adama daga tsatsonsa har zuwa ranar alkiyama sai suka fito kamar zurra sai aka kwada masu kanunsu, kuma bad an haka b aba wanda zai san ubangijinsa ba). har ila yau a wata riwayar kwa Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce ko wani Mutune ana aifuwarsa bisa fitira, ma’ana bisa sanin cewa hakika Allah madaukakin sarki shine ya halicesa, kuma don haka Allah madaukakin sarki ke cewa:(wallahi da z aka tambaye su wanda ya halicci sammai da Kassai, lallai za su ce Allah ne…) suratu zumari aya ta 38, masu saurare hakika Hankalin mutune na gumshe ne da hakikanin sanin addini a cikinsa, ma’ana shi wani guri ne na sanin ubangiji tun daga lokacin da aka halicce shi,amma bayyanar wannan ilimi ya na bukatar koyarwar Annabawa da waliyai amincin Allah ya tabbata a garesu, wannan shine matsayin hankali ga sanin addini. A cikin littafin Tuhuful Ukul, an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce ( ilimi abokin mumini ne, hankali kwa hujjar sa ne) har ila yau awata riwayar kwa ma’aikin Allah ya ce:( ba a neman Bawa ya cika Falilar musulinci sai an bashi hankali), a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya ce:( hakika Allah madaukakin sarki ya cikawa Mutane hujojjinsu da hankali sannan daukaka annabawansa da bayyani. Hakika duk wand aba ya tsoron Allah ba ya tutanin Allah, kuma duk wanda ba ya tunanin Allah bai daurawa zuciyarsa ba hakikanin sani wanda zai sanya shi ya samu Basira da kuma gaskiya a zuciyarsa).domin haka ne Aminru mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) yak e cewa aiki annabawa (A.S) shine farfado da aiyukan hankali domin fitar da taskar ilimin Tauhidin da aka halicce shi da shit un farko a cikin littafin Nahjul Balaga Imam (a.s) ya ce :( sai ya aiko ma’aikansa daga cikinsu sannan ya tayar da Annabawansa daya bayan daya daga cikinsu domin su tunatar da Mutane alkawarukan da suka dauka da ni’imar da ta zamanto mantatta a garesu, kuma suka kafa masu hujja a yayin da suke kiransu ga tauhidi kuma su farfado da abinda yake abinne cikin hankula), da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon amfani da hankulanmu ta yadda ya dace.
*********************Musuc********************************
Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.