Mar 06, 2016 19:21 UTC
  • karamin Sani kukumi-Ma’anar Basira

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau ita ce minene ma’anar Basira, kuma minene mahimancinta a rayuwar Dan Adam? Kafin amsar tambayar  ga wannan?


*****************************Musuc******************************


Masu saurare Kalmar Basira a yaran Larabci shine  haske mai karfi a cikin zukata ko hankulan Mutane wanda yake saukin  gano gaskiya, kamar kana ganinta da idanu kamar yadda ake kiran Basar da wannan ido na zahiri wanda muke ganin abubuwa a zahiri da shi, wannan ma’ana ta Basira ita ce wacce ta zo cikin  alkur’ani mai tsarki da  hadisai ma’aikin Allah tsira da amincin su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin Suratu Hajji Aya ta 46 Allah madaukakin sarki ya ce:(Yanzu ba za su yi tafiya a bayan kasa ba don su samu zukata da za su rika tunani  da su, ko kuwa kunuwa da za su rika ji da su? To hakika idanuwa bas a makancewa sai dai zukatan da suke cikin Kiraza sune su ke makancewa). A cikin suratu A’arafi Aya ta 179 Allah madaukakin sarki ya ce:(hakika  kuma mun samar wa Jahannama tari mai yawa na aljanu da mutane, suna da zukata wadanda bas a fahimta da su,kuma suna da idanuwa wadanda bas a gani da su,kuma suna da kunnuwa wadanda ba sa ji da su, kai wadancan kamar dabbobi suke, kai sun fi su ma rashin fahimta, wadancan su ne gafallalu) har ila yau a cikin suratu Muhammadu Aya ta 24 Allah madaukakin sarki ya ce:(Yanzu ba za su yi tunani ba (game da Ayoyin ) Alkur’ani ko kuwa a zukata a kwai makullai). Masu saurare wannan Aya da ma makamantanta ta na bayyani kan cewa gabobin Mutune a zahiri sune hanyar isa ga sanin farko wanda mutune ke samu,  daga cikinsu a kwai basirar zuciya bisa hakikanin ilimi wanda ta hanyar haske ilimi ne dan yake samu, har ila yau ta hanyar Basira Mutune yak e isa ga kamala ya zamanto daga cikin ahlin Aljanna , idan kuma ya rasa wannan basira ya kasance daga ahlin wuta, ya fi dabobbi bacewa ga hanya.


Masu saurare hakika, Basira na da mahimancin gaske domin ita ce ke tabbatar da mahimancin rayuwar mutune, kuma Nasossi da dama sun tabbatar da cewa tana daga cikin siffofin waliyan Allah madaukakin sarki a dukkanin Al’amuransu, a cikin suratu Yusufu Aya ta 108 Allah madaukakin sarki ya ce:( ka ce wannan ce hanyata in yi kira zuwa ga Allah , bisa  Basira (hujja),ni da wanda ya bi ni, tsarki kuma ya tabbata ga Allah, ni kuwa ban a cikin masu shirka ) domin haka basira tafarkin mabiya Annabi Muhamad (S.A.W) ne .kuma ta hanyar ta ce suke tsira daga bata , yayin da yake bayyana sifoffin waliyan Allah masu gaskiya, a cikin Littafin Nahjul Balaga Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s)ya ce:(sun cimma ilimi, gaskiya da Basira  kuma sun tunkari ruhin yakini, kuma duk abinda wasu ke ganinsa  da wuya , su a gurun su mai sauki ne, su na tare da abunda ke tunzura jahilai, gangar jikinsu ne kawai ke rayuwa a duniya amma ruhinsu ya na tare da Allah madaukakin sarki, wadannan sune khaslifofin Allah a doron kasa, kuma sune masu kira zuwa ga addininsa). A cikin littafin Kashful Mahajja na Sayyid bn Tawus an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa daga wasikun da shugaban mumunai Aliyu bn abi talib (a.s) ke rubutawa manyan sahabansa, a nan iman sadik (a.s) yana ishara ne kan girman matsayin wasikun ya ce a farkon wasikun Imam Ali(a.s) ya ce:(zuwa ga makusanta cikin inuwar dake tattare da ibtila’I,masu gaggawa wajen amsa da’ar ubangiji, wadanda suka samu tabbaci da yakini na dawowar wasu bayin Allah wannan duniya a lokacin bayyanar cikamakin wasiyai Mahdi,ajalar lahu farajahu, gaisuwata zuwa gareku, amincin Allah ya tabbata a gareku, hakika hasken basira shine ruhin rayuwa kuma imanin bay a amfanar wa sai da shi (wato hasken basira) tare da bin Kalmar ubangiji da kuma gasgantar da shi,kalamar Allah daga ruhi ne, kuma ruhi daga haske ne, hasken samai da kasai).


****************************Musuc***************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai fara da littafin Umdastul Talib inda a cikinsa  Imam Sadik (a.s) ke siffanta abi Fadl Abas dan Amiru mumunin (amincin Allah ya tabbata a garesu)inda ya ce:(baffa na  Abas dan Ali ya kasance wundon Basira, garkuwar imani, yayi yaki daimam husain (a.s) kuma ya jarabtu da ibtila’I mai kyau har yayi shahada).


A bangare guda kuma imam (a.s) ya yi bayyani dangane da mutanan da bas u aiki da Basirarsu, a cikin littatafan Bikhu Rida (a.s),Amaly na shek Tusy, da kuma Almahasin na shek Barki an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) na cewa :( wanda yake aiki ba tare da basira, kamar direban da yake tafiya ba kan hanya ba, saukinsa ba zai amfanar da shi komai ba zai dai ma ya kara masa nisan hanya).


A cikin littafin Almahasin an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk wanda yake wani aiki ba da ilimi ba zai kasance barnarsa ta fi gyaransa yawa) har ila yau a cikin littafin Khisal, Ma’aikin Allah (S A W) ya rarraba hankali gida uku, ya ce duk wanda ya kasance yana cikinsa to hankalinsa ya kamala, kuma duk wanda ya kasance bay a cikinsa  babu hankali a tare da shi) sannan Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ci gaba da cewa Basira na daga cikin Lamuran da suke cika kamalar  hankali inda ya ce kyakkyawar sani ga Allah madaukakin sarki, kyakkyawar da’a da biyayya ga Allah, kyakkyawar basira a kan al’amuransa wato Allah madaukakin sarki).wannan abebe guda uku sune ma’aikin Allah (S A W) ya ke nufi da duk wanda ya kasance a cikinsa wato kyakkyawan sani ga Allah, kyakkyawar biyayya da kuma kyakkyawar basira ga al’ummar ubangiji duk wanda ya kasance ya na cikin hakan to hakika hankalinsa ya kamala. Har ila yau a cikin littafin fikhu Rida an ruwaito hadisi daga Ma’aikin allah tsira da amincin allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(ka dubi wanda yak e kasa da kai wajen karfi ko arziki, kadda ka dubi wanda yake sama da kai,domin yin hakan shi zai sanya maka dangane da kuma godiya ga Allah madaukakin sarki kuma yay i maka sanadiyar gari, ka sani dawwama a kan aiki kadan tare da tabbaci da kuma Basira ya fi aiki mai yawa da babu yakini a tare da shi).


Masu saurare takaicecciyar amsar da za su fahimta a wannan shiri, shine Basira ta na nufin sanin cikin zuciya tabbatace wanda yake tare da hasken hankali, kuma ita Basira ta na daga cikin Sififin waliyan Allah masu gaskiya kuma da ita ne aiyuka mutane ke samun karbuwa kuma ake isa zuwa ga kamala.


*********************Musuc*************************************


Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.