Mar 06, 2016 19:23 UTC
  • karamin Sani kukumi-Mike Katange Hasken Basira

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin  Basira, da kuma  mahimancinta a rayuwar Dan Adam, tambayarmu ta yau ita ce wasu ababe ne ke hana dan Adam samun hasken Basira ? Kafin amsar tambayar  ga wannan


*****************************Musuc******************************


Masu saurare, a shirin da ya gabata Ayoyi da daman a cikin  kur’ani mai tsarki tare da hadisan ma’aikin allah tsira da amincin allah su tabbata a gareshi sun bayyana mana cewa hakika hasken Basira shi ke sanya dan Adam ya shiryu bisa tafarki madaidaici wanda babu kokonto a cikinsa. Kuma ta hanyarsa ne Mutune yake gane al’amuran gaskiya wadanda za su ya cimma gurinsa na samun dukkanin alherin duniya da lahira kuma ya kai ga kamala da kuma kare kansa daga duk wani sharri na makiyi.domin haka sanin ababen dake hana dan Adam samun wannan haske nada mahimancin gaske, domin sai ya sansu zai ya kesu, kamar yadda  shiri ya saba za mu fara da Littafin allah mai tsarki wato Alkur’ani.a cikin suratu Mudaffifina daga Aya ta 7 zuwa ta 17 allah madaukakin sarki y ace:(tabbas hakika Littafin Fajirai yana cikin Sijjinu*Kai ba san mene ne Sijjinu ba* Litattafi ne rubutacce*tsananin Azaba a wannan Rana ya tabbata ga masu karyatawa* wadanda suke karyata ranar sakamako*Babu mai karyata ta sai mai shisshigi da yawan sabo*idan aka karanta masa ayoyinmu sai ya ce wannan tatsuniyoyi ne na mutanan farko* ku shiga taitayinku!abi ai ba haka ba ne, abinda suke aikatawa ne ya yi tsatsa a zukatansu* Tabbas ! hakika su lallai ababen kangewa ne daga (ganin) Ubangijinsu a wannan Rana*sannan hakika su lallai masu shigar wutar Jahima ne* sannan za a ce wannan ne abin da ku ka kasance kuna karyata shi).masu saurare wadannan ayoyi masu albarka sun bayyana cewa sanadiyar da ya sanya Fujjar  rashin samun basira da kuma Rahamar Ubangiji shine karyata ayoyin allah madaukakin sarki, da kuma aiyukan da suka aikata da hanunsu, wannan shine ya hana su samun hasken Basira kuma ya lullube masu hasken Rahamar Ubangiji madaukakin sarki.domin haka aikata zunubi na daga mahiman ababen da ke hanawa dan adam hasken basira da kuma samun duk wani alheri,wannan shine abinda shugabanmu imam Bakir (a.s) ya yi ishara  cikin hadisin da aka ruwaito a littafin Kafi na Sikkatu Islam Kulainy.(ko wani Bawa a cikin zuciyarsa a kwai wani farin digo, duk lokacin da ya aikata zunubi sai wani digo na baki ya shiga cikin wannan haske,idan ya tuba sai digon bakin ya gushe,  idan kuma ya ci gaba da aikata zunubi digo baki  na zunubin zai ci gaba da shiga cikin digon hasken  ya lullube shi  har ya  kawar da  shi baki daya, matukar hasken ya kawar, to mutume ba zai koma bisa aikata alheri har abada ba kuma wannan shine kaolin allah madaukakin sarki:( Tabbas ! hakika su lallai ababen kangewa ne daga (ganin) Ubangijinsu a wannan Rana).suratu Mudaffifina Aya ta 15.


Masu saurare abu na biyu dake yin sanadiyar haramtawa Bawa samun hasken Basira , shine son rai ko bin son zuciya tare da bin ra’ayin da bai dace ba,gami da ta’asubanci ba tare da tunani mai kyau ba.a cikin suratu Jasiya Aya ta 23 Allah madaukakin sarki ya ce:( shin yanzu ba ka ganin wanda ya riki Ubangijinsa, son ransa,Allah kuma  ya batar da shi a kan sani ya kuma rufe jinsa da kuma zuciyarsa kuma ya sanya rufi a ganinsa, to waye zai shiryar da shi bayan Allah! Me ya sa ba kwa wa’azanta ne) a cikin suratu fusilat Aya ta 17 Allah madaukakin sarki ya ce :(Samudawa kuma sai muka nuna musu hanyar shiriya, sai suka zabi hanar bata a kan ta shiriya, sai tsawar Azabar wulakanci ta kama su saboda abin da suka kasance suna tsuwurwutawa) domin haka ne Amiri mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ke cewa:(ina muku wasici da ku kuji son zuciya domin son zuciya ya kan kai ga Mutune zuwa makabtar ganin gaskiya ita kuma wannan makabta bata ce a duniya da lahira)


******************************Musuc**************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara  zai fara da Littafin Gurarul Hikam inda a cikinsa Imam Ali(a.s) ke cewa:( Hikma ta ba zama a cikin zuciyar dake dauke da sha’awa) har ila yau a wata riwayar ya na cewa:(haramun ne bisa hankalin dake tare da sha’awa ya amfanu da hikma) an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya ce:( hakika Allah madaukakin sarki yayi wa Annabi Dawuda (a.s) wahayi Ya Dawud ka kiyaye kuma ka tsoratar da sahabanka dga son sha’awa domin zukatan da suka tattare da sha’awa katangaggu ne daga ni), a cikin littafin Uyunul Hikama wal mawa’iz an ruwaito hadisi daga Amiru muminin Aliyu bn Abi Talib (a.s) y ace:(dawwama a kan gafala ko kuma shagaltuwa daga son duniya ya kan makabtar da Basira, rashin gani ya fi makabtar basira zama alheri ga dan Adam), a cikin littafin Biharu Anwar an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Kazim (a.s) na cewa (duk wanda ya dora abu uku bisa uku kamar ya taimaka wajen rusa hankalinsa ne, duk wanda ya dirshashe hasken tunanisa da dogon fatansa, kuma ya shafe hikimarsa da yawan zance, sannan kuma ya  kashe hasken abinda ya kasance darasi a gareshi da bin sha’awar zuciyarsa kamar ya taimakawa son zuciyarsa ne wajen rusa hankalinsa, kuma duk wanda ya rusa hankalinsa ya bata Addininsa da Duniyarsa).


Masu saurtare, a bangare guda hadisai da dama sun bayyana ababen da suke karfafa hasken Basira ga Adam,daga ciki kwa a kwai yin tunani cikin kalmomin shiriya da kuma daukan darasi kan abinda ya gabata.Amuru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) y ace:(mai Basira shine wanda ya ji kuma ya yi tunani kan abinda ya jin, ya gani kuma yay i nazari kan abinda ya ganin sannan ya amfanu da irin darusan da ja ji daga magabata, da kuma ta hanyar shiriya ce basira ke kara karuwa).a cikin littafin Tuhuful Ukul an ruwaito hadisi daga Imam Kazim (a.s) na cewa:(ku nemi sani cikin Addinin Allah domin sani mabudin basira ne kuma cikamakin addini ne kuma shi ke mai shi zuwa gidaje masu girma tare da babban matsayi a duniya da Lahira)


*******************Musuc*******************************


Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.