karamin Sani kukumi-Ilimin Ilhami
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau minene ilimin Ilhami ko kuma Ladunni kuma ta yaya ake cimma wannan ilimi?kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari a kayi mana tanadi a kan faifai.
*********************Musuc****************************
Masu saurare a cikin Alkur’ani mai girma ayoyi da dama sun yi ishara kan ilmin Ladunni,misali a cikin suratu Kahfi Allah madaukakin sarki ya ambato kissar Annabi Musa(a.s) tare da salihin bawan Allah nan Hadru (a.s), inda Allah madaukakin sarki ya umarci Annabi Musa (a.s) da ya nemi sani a wajen salihin bawan Allah nan Hadru (a.s),Allah madaukakin sarki ya ce :(To sai suka sami wani Bawa daga bayinmu wanda muka bai wa Rahama daga gare Mu,kuma muka sanar da shi wani ilimi daga wajenmu) suratu kahafi Aya ta 65.masu saurare hakika ko wani ilimi da bawa zai samu karshensa yana komawa ne zuwa ga Allah madaukakin sarki, amma cikin wannan Aya mai albarka Allah y ace wannan ilimi daga wajen kai tsaye ba tare wasida ba kuma duk wanda aka bashi wannan ilimi yayi fice a cikin mutane da wasu nau’o’I na Albarkar ubangiji domin haka ne ma nasossi da dama suke bayyana nau’in wannan ilimi da haske ko kuma hakikanin ilimi, a cikin Suratu An’am Aya ta 122 Allah madaukakin sarki ya ce:(shin wanda ya kasance matacce(cikin kafirci)sannan Muka raya shi (da shiriya) Muka kuma sanya masa haske (na shiriya) yana tafiya da shi cikin Mutane (yanzu) ya yi daidai da wanda yake cikin duhun (kafirci) kuma ba zai fita daga cikinsa, kamar haka ne aka kawata wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa) Imam Bakir (a.s) ya fasarra ma’anar haske a wannan aya mai albarka da yulawa da kuma shugaban gaskiya domin ilimin ilhami na zuwa ga mumuni ne yayin da ya yi ruko da wulayar gaskiya kuma ta wannan hanya ce zai ni’imtu da ni’imar Allah madaukakin sarki kuma ya yi rayuwa ta gaskiya mai inganci. Dangane da wannan ilimi na ilhami shugaban mumnai Aliyu bn Abi Talib(a.s) na cewa:(hakika ya rayar da hankalinsa sannan ya hashe zuciyarsa ya haskakashi da haske mai yawa, sannan ya hango masa sahihiyar hanya kuma ya dora shi a kan hanya sannan kofofi suka yi ta bode masa har zuwa kofar aminci da kuma gidan zama).wannan hadisi mai albarka na Amiru mumunin (a.s) ya yi bayyani kan cewa wannan Ilimi na ilhami wani nau’in ilimi ne daga Allah madaukakin sarki da ya horewa bayinsa wadanda suka yi ikhlasi wajen neman yardarsa, kamar yadda wasu Nasossin masu yawa daga iyalan gidan ma’aikin allah tsarkaka suka yi ishara da hakan, a cikin littafin Ayyashi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce :(yayin da sarki ya bada umarni da a daure Annabi Yusuf (a.s) a gidan Yari , sai Allah madaukakin sarki yayi wa Annabi yusuf (a.s) ilhamin Ilimin Tawili ko kuma fassarar mafalki).a cikin litattafan kafi, Uyunul Akhbaru Rida da saurensu, an ruwaito hadisi daga shugabanmu babban hasan Imam Rida (a.s) yayin da yake siffanta shugaban gaskiya-hadisin na tsahon gaske- saidai mun dauko wani bangare ne domin bayyana kadan daga sifoffin shugabanin gaskiya Imam (a.s) ya ce:( idan Allah madaukakin sarki ya zabi bawa domin al’amuran bayinsa sai ya buda masa kirjansa sannan a zubuwa zuciyarsa hikma, a kuma fasahantar da halshensa sannan a yi masa ilhami da ilimin ladunni babu wata tambaya da za a yi masa face ya bayar da amsawarta kuma duk amsawar da ya bayar gaskiya ce kuma ita ce hakikanin amsar wannan tambaya,mai wannan siffa shine ma’asumi wanda ba ya sabo tabbacecce daga wajen allah madaukakin sarki).masu saurare wannan shine ilimin ilhami wanda Allah madaukakin sarki ya horewa Annabansa da waliyansa tsarkaka sannan ya horewa wasu daga cikin mumunan bayinsa ya babantasu bisa matsayinsu na imani da kuma Ikhlasi.an ruwaito wani hadisi daga ma’aikin allah tsira da amincin allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa: (mumuni yana kallo da hasken Allah). A cikin littafin uyunul hikam wal mawa’iz an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) na cewa (idan Allah ya so bawansa sai ya yi masa ilhami da ilimi).har ila yau Imam (a.s) ya ce:(idan Allah madaukakin sarki ya so Bawa sai ya yi masa ilhami da kyakkyawen aiyuka na Ibada).
***********************Musuc***************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da littafin Gurarur hikam na shek Wahidi Al’amidi inda a cikinsa aka ruwaito hadisi shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce (idan Allah madaukakin sarki ya shiryar da bawansa sai yayi masa ihami na karamcin zance , ma’ana Dan Adam zai bar duk wata maganar da bata da fa’ida cin abinci da kuma rage yawan barci).A cikin littafin Ma’adanul Jawahir na Abil Fathil Karaji an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(idan Allah madaukakin sarki ya so bawansa sai ya yi masa ilhami da aiyuka guda takwas, rufe idanunsa daga kallaon abinda yake muharami a garesa, tsoron allah madaukakin sarki, kunya, hakuri , zirfin hakuri, rikon Amana, rikon gaskiya da kuma kauta) har ila yau a cikin littafin Mustadarakul wasa’il an ruwaito hadisi daga Imam (a.s) na cewa:(idan allah madaukakin sarki ya so bawa sai ya yi masa ilhami da yin biyayya a gareshi ya kuma bashi dangana, da kuma zurfafa a cikin ilimin Addini, ya kuma karfafa shi da tabbaci gami da yakini) A cikin littafin Gurar an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce (idan Allah madaukakin sarki ya so bawa da alheri sai yayi masa ilhami na tattalin arziki da kyakkyawan tafiyar da al’amuransa, sannan kuma ya kare shi daga mumunar tafiyar da Al’amuransa da kuma yin barna ko Israfi).
Bayan wadannan hadisai masu albarka a kwai riwayoyi da dama wadanda suke dauke da irin wannan ma’ana na cewa Allah madaukakin sarki yana yiwa bayinsa mumunai ilhami da kebebben ilimi daga gareshi wadanda suke taimaka masu wajen cimma maslaharsu da kuma kyakkyawar hanya na yin bauta a gareshi da kuma kyakkyawen dabi’u tare kuma da aikata abinda yake alheri a garesu duniya da Lahira.
Masu saurare,idan muka yi la’akari da wadannan nasossi masu albarka, za mu samu amsar tamabayrmu kamar haka,Ilimin Ilhami ko kuma ilmin Ladunni ilimi ne mai haske da Allah madaukakin sarki ya kan sanya shi a zukatan Annabawa, imaman na iyalan gidan ma’aikin Allah, waliyai da kuma mumunai daidai kwolkwadon tsanin imaninsu.kuma wannan wani nau’in karfin gwina ne daga Allah madaukakin sarki ga bayinsa na gari domin su isar ga yaunin da ya rataya a kansu da kuma kai wani matsayi na hakikanin rayuwa.
***************************Musuc*********************************
Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.