karamin Sani kukumi-Samun Ilimin Ilhami
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan ma’anar ilimin Ilhami ko kuma ilmu Ladduni,tambayarmu ta yau kwa ta yaya mutune zai iya samun wannan ilimi ?sai a kasance tare da mu domin jin amsar wannan tambaya.
*******************************Musuc******************************
Masu saurare idan muka yi nazari a cikin wasu Ayoyi na Alkur’ani mai girma za mu fahimci cewa tsoron Allah shine shugaban duk wata hanya na cimma hasken ilimin ilhami ko kuma ilmu Ladduni,a cikin suratul Anfal Aya ta 29 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya, idan kuka ji tsoron Allah to zai sanya muku (hanyar) tsira ya kuma karkare muku munanan ayyukanku kuma ya gafarta muku.Allah kuwa ma’abocin falala ne Mai girma) Acikin Tafsirin Aliyu bn Ibrahim Alkummi an fasarra kalmar Furkan (ma’ana hanyar tsira) da hasken ilimi ko kuma ilmu ladduni wanda yake babbancewa mumuni tsakanin karya da gaskiya, ya bi gaskiya kuma ya nisanci ko kuma ya kaucewa karya wanda kuma hakan shi zai bashi damar samun babban rabo a duniya da Lahira.A cikin Suratu Hadid Aya ta28 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya ku ji tsoron Allah ku kuma ba da gaskiya da Manzonsa, ya ba ku rahamarsa ya kuma sanya muku haske ku rika tafiya da shi, kuma ya gafarta muku, domin kuwa Allah mai gafara ne Mai Rahama). Maluman tafsiri sun fasarra kalmar Nur ma’ana haske da shugaban Gaskiya domin kasancewar shugaba ma’asumi daga cikin iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka ma’anar ma’asumi shine wanda Allah madaukakin sarki ya kiyaye shi daga duk wata dauda ta aikata sabo, kasancewarsa a tsakanin Al’umma shine wasilar isar ilimin ubangiji a tsakanin mumunai. Hakika a cikin Littafin Kafi na sikatu islam kulaini an ruwaito hadisi daga Ibn Jarud ya ce:wata rana na je wajen babban Ja’afar Imam Bakir (a.s) sai na ce masa hakika Allah madaukakin sarki ya baiwa Ahlil Kitab Alheri mai yawa Sai Imam (a.s) ya ce da ni wani alheri ne? sai nace masa fadar Allah madaukakin sarki:(wadanda muka bai wa Littfi a gabaninsa (wato Alkur’ani)su suna bada gaskiya da shi). Zuwa fadar Allah cewa:(wadancan za a ba su ladansu ninki biyu saboda hakurin da su kayi ,kuma suna kawar da mumunan aiki da kyakkyawa, suna kuma ciyar wa daga abin da Muka arzuta su (da shi)) suratu K’asasi daga Aya ta 52 zuwa ta 54 sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa hakika Allah madaukakin sarki ya baku makamancin abinda ya basu sannan sai ya karanto wannan Aya(Ya Ku wadanda kuka yi Imani ! ku bi Allah da Takawa, ku yi Imani da Manzonsa ya ba ku rabo biyu daga rahamarsa kuma ya sanya Muku wani hasken wanda kuke yin tafiya da shi,kuma ya gafarta muku, kuma Allah mai gafara ne, Mai Rahama)suratu Hadid Aya ta 28. Sannan ya ce (ma’ana shugaban da za ku yi koyi da shi) a cikin wata riwaya ta daban wacce aka ruwaito cikin Littafin Kafi , Imam Bakir (a.s) ya ce:( riko da wilayar imami ma’asumi shine hanyar da mumuni zai rabauta da hasken wannan ilimi, wato Ilmin Ladunni).masu saurare a wani hadisi na daban an ruwaito cewa Aba Khalid Kabili ya ce na tambayi Babban Ja’afar Imam Bakir (a.s) ma’anar haske a fadar Allah madaukakin sarki:(saboda haka, ku ba da gaskiya da Allah da Manzonsa da kuma hasken da Muka saukar, Allah kuma Masani ne da abin da kuke aikata wa) sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa (Ya Aba Khalid, Haske wallahi sune shugabani daga cikin iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka, Ya Aba Khalid hasken Imami na iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka a cikin zukatan mumunai ya fi hasken Rana da take haskakawa a ko wata Ranar ubangiji, hakika Imamai sune masu haskaka zukatan mumunai, kuma Allah yana lulube haskensu ga wanda ya so, wadanda aka lullube haskensu daga haskensu sun zalinci kawunansu).domin haka masu saurare tsoron Allah madaukakin sarki wanda yake a tattare da rikon wulayar Imamai Iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka ita ce muhimiyar hanyar samun rabauta da hasken ilimin Ilhami ko kuma Ilmu Ladunni.
**************************Musuc********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, hadisai da dama sun bayyana cewa soyayyar Ahlul bait (a.s) na daga cikin mahiman hanyar samun rabauta na ilimin Ladduni da kuma hikmar ubangiji, domin haka wannan soyayya ita ce bayyanar riko da wulayarsu amincin Allah ya tabbata a garesu.hakika an ruwaito hadisai da dama cikin litattafan Ahlu sunna wadanda suke bayyani dangane da hakan, misali a cikin Littafin Fara’id samtin na Hafiz Hamawi Ashafi’I da kuma Littafin Maktalul Husain (a.s) na Hafiz khawarizmi Alkhanafi an ruwaito hadisi daga bn Umar daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:( duk wanda ya ke son ya samu Hikma to ya so Ahlu Baity wato iyalan gidana), a cikin Littafin Bisharatul Mustapha) da kuma littafin Mi’a Munakaba da saurensu an ruwaito hadisi daga Ibn Umar daga Ma’aikin Allah (s.a.w.s) ya ce:( ku saurara! Duk wanda yake son Aliyu, Allah madaukakin sarki zai tabbatar masa da hikima a cikin zuciyarsa kuma ya sanya duk abinda zai fitar daga harshensa gaskiya ce).Masu saurare kamar yadda Hadisai da dama sun tabbatar da matsayin takawa da tsoron Allah wajen shiryar da mumunai samun rabauta da hasken Hikma da kuma Ilmu Ladduni. Hakika an ruwaito hadisi daga Littafin Awalil Aly daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:( da za ku ji tsoron Allah kamar yadda ya kamata, da an sanar muku da ku ilimin da babu jahilci a cikinsa, kuma da kun san Allah hakikanin Sani, da Duwatsu sun kau albarkacin Addu’arku). Kamar yadda Shek Tusy ya ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) a cilin Littafinsa Amaly ya ce:(tsoron Allah shine mabudin dukkanin Hikma). A cikin Littafin Gurar an ruwaito hadisi daga wasiyin ma'aikin Allah Murtada Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(duk wanda ya ji tsoron Allah iliminsa ya cika).har ila yau a cikin Littafin Nahjul Balaga Iman Ali (a.s) ya ce:(bayin Allah! Fiyayyen masoyin Allah a gurinsa shine bawan da Allah ya taimakesa ya fi karfin zuciyarsa, wanda yayi shu’urin bacin rai kuma ya lulluba da tsoron azaba, sai hasken shiriya ya bayyana a zuciyarsa).masu saurare abinda muka fahimta daga cikin wadannan Nassosi masu albarka shine, Takwa, tsoron Allah da kuma riko da wulayar Annabi Muhamad Tsira da amincin allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na daga cikin mahiman batutuwan da suke sanyawa Bawa ya rabauta da hasken Ilimin Ilhami ko kuma ilmin Ladduni, a cikin shirinmu na gaba za mu kawo muku wasu abubuwan bayan wadannan da yardar Allah, da fatan allah madaukin sarkin ya sanyamu daga cikin bayinsa masu takawa da tsoron Allah , masu kuma riko da da wulayar Annabi Muhamad Tsira da amincin allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka domin mu rabauta da hasken ilimi mai albarka wanda zai sanya mu sami kyakkyawan rabo a duniya da Lahira.
*****************************Musuc*****************************
Masu saurare anan a mu dasa Aya…………………………………………