karamin Sani kukumi-Cimma Ilimin Laduni (2)
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare Assalama Alkum barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayyani dangane da ilimin Ilhami ko kuma ilmu Ladduni,a shirin namu na yau za mu dora daga inda muka tsaya inda za mu kawo muku wasu muhiman batutuwan da za su taimaka wajen cimma wannan ilimi mai albarka, amma kafin mu shiga shirin, bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.
****************************Musuc***************************
Masu saurare a shirin da ya gabata mun bayyana cewa Takwa, tsoron Allah gami da rikon wulayar Iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka na daga cikin ababen da suke sanya dan Adam ya cimmawa Ilmu Laduni, a shirin na yau za mu yi dubu a kan wasu ababen da suke yin sanadiyar cimma wannan ilimi mai albarka, masu saurare Jihadi saboda Allah na daga cikin muhiman ababen da suke sanya Dan Adam ya rabauta da wannan ilimi mai haske,a cikin karshen Suratu Ankabutu Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma wadannan da suka yi kokari ga neman yardarmu, lalle Muna shiryar da su ga HanyoyinMu, kuma lalle Allah, tabbas yana tare da masu kyautatawa)suratu Ankabut Aya ta 69 ma’anar masu jihadi saboda da Allah shine masu kokari wajen bautar Allah domin samun kusanci da shi da kuma yardarsa ko kuma masu yaki da makiyansa, duk mai wannan kokari Allah madaukakin sarki zai hore masa ilimin da zai shiryar da shi zuwa saninsa da kuma kusanci da shi, masu saurare bayan wannan, imani ga Allah madaukakin sarki na gaskiya na daga cikin ababen da suke sanya Dan Adam ya samu rabauta da hasken hikma da shiriya kamar yadda Alkur’ani mai girma ya ambata, a cikin Suratu Tagabun Aya ta 11 Allah madaukakin sarki ya ce:(wata masifa ba za ta samu ba face da izinin Allah.kuma wanda ya yi imani da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa, kuma Allah, ga dukan kome, Masani ne), masana fassarar Alkur’ani sun fassara ma’arnar Allah zai shiryar da Zuciyarsa da cewa Allah zai sanya hasken hikima da kuma bashi ilmin da zai kusantar da shi zuwa ga Allah madaukakin sarki, masu saurare kamar yadda yin da’a ko kuma biyayya ga umarnin Allah madaukakin sarki tare kuma da aiki da abinda mutune ya sani na umarnin ubangiji na daga cikin ababen da suke sanya Dan Adam ya samu rabauta da hasken shiriya ta musaman. A cikin Suratu Nur Aya ta 54 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce Ku yi da’a ga Allah ku yi da’a ga Manzo to, idan kuka ba da baya, to hakika ba abinda ya hau a kansa sai abinda aka dora masa, kuma ba abin da ya hau a kanku sai abinda aka dora muku. Idan kuwa kuka ki masa da’a za ku shiriya, ba kuwa abin da yake kan Manzo sai Isar da aike mabayyani) ma’ana suna shiryuwa da Albarkar hasken da ake sanyawa a zukutan mumunai zuwa shiriyar ubangiji ta musaman.A cikin Littafin Alfusulul Mukhtarat na sayyid Murtada an ruwaito hadisi daga bangarori biyu wato sunna da shi’a, ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda ya yi aiki da abinda ya sani Allah zai kara masa ilimin da bai sani ba) a cikin littafin Biharu Anwar an ruwaito hadisi daga Imam Ja’afaru Sadik (a.s) na cewa :( duk wanda ya yi aiki da abinda ya sani Allah madaukakin sarki zai sanar da shi abinda bai sani ba), masu saurare Ikhlasi acikin aiki saboda Allah na daga mahiman ababen da suke sanya dan adam ya samu rabauta da hasken hikma, hakika bangarorin sunna da shi’a sun ruwaito wani hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(babu bawan da zai bautawa Allah da ikhlasi na tsahon safiya arba’in sai Allah ya sanya hikma a zuciyarsa tana gudana a harshensa), a cikin littafin Guraru Hikam an ruwaito hadisi daga shugaban mumnai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(ya shiriya wanda kyautata imaninsa ya zamanto mai ikhlasi a aiyukansa).
*****************************Musuc***************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, hadisai da dama suna shiryar da mu cewa ‘yantar da kai daga kurkukun duniya da kuma tabbatar da gaskiya wajen amfani da ni’imomin duniya na daga cikin ababen da suke yin sanadiyar samun hasken hikma da ilimi na ilhami.a cikin littafen hilyatu Auliya na Tuhuful Ukul an ruwaito hadisi daga Imam Ali(a.s) ya ce:(duk wanda ya kauda kai da rudun duniya kuma ya kauda kai da kaskancin zahiri da mutane ke ganinsa da shi na rashi ko kuma rashin shiga cikin wani aiki na sabo sannan kuma bai damu da neman daukaka daga duniyar ba, Allah madaukakin sarki zai shiryar da shi ba tare da shiryarwar wani mahluki ba, kuma zai koyar da shi ba tare da koyarwar wani mahluki ba, za ta tabbatar masa da hikma a zuciyarsa sannan a sanyata a dinga gudana a harshansa), har ila yau masu saurare daga cikin ababen da ke sanya dan Adam ya rabauta da ilimu Laduni, kaucewa cin haram tare da cin abinci na halal wanda ya nisanta daga wata shubuha, a cikin Littatafen Uddatu Da’I na Ahya’ul Ulum da saurensu an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk wanda ya ci halal na kwana Arba’in Allah madaukakin sarki zai haskaka zuciyarsa sannan ya sanya hikma tana gudana a zuciyarsa) har ila yau a cikin littafin Majma’ul Bahren an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah ya na cewa:(duk wanda ya ci abinci daga Halal zuciyarsa za ta zarkaka sannan idanuwansa su bude kuma babu shinge ko hijabi daga da’awarsa) a cikin littafin Musnad na Zaid bn Ali daga kakansa Amiru mumunin (a.s) ya ce:(duk wanda ya zamanto yana aiki da ikhlasi kwanaki 40 yana cin abincin halal, kuma ya azumci wadannan kwanuka, ya na sallar dare, Allah madaukakin sarki ya sanya hikma ta dinga gudana daga cikin zuciyarsa zuwa harshensa). Har ila yau masu saurare Azumi na daga cikin ababen da suke yin sanadiyar samun rabauta da ilmu Ilhami, a cikin hadisu Mi’iraj an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayin da ya tambayi mahalicinsa ya ce Ya Ubangiji kuma minene kadon Azumi? Sai Allah madaukakin sarki ya ce:(Azumi yak an kadar da Hikma, ita kuma Hikma ta kan kadar da sani, shi kuma Sani yak an kadar da Yakini) daga karshe masu saurare Addu’a na daga cikin muhiman ababen da ke yin sanadiyar samun rabauta daga ilimin Ilhami, hakika nassosi da dama sun yi mana ishara da hakan kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma K ace :Ya Ubangina !ka kara mini Ilimi) suratu Taha Aya ta 114 kuma ga shaharariyar Addu’ar nan ta ma’aikin Allah inda yake cewa :(Ya Ubangiji ka kwada mini gaskiya kamar yadda ta ke) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu damar aiyuka da umarninsa da kuma hanuwa daga haninsa domin samun rabuta da hasken hikma gami da ilimin Ilhami wanda zai shiryar da mu zuwa samun rabauta a nan duniya da Lahira.
******************************Musuc*******************************
Masu saurare a nan za mu dasa Aya saboda lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala , ni da nagabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.