Mar 06, 2016 19:30 UTC
  • karamin Sani kukumi-Wani Ilimin Addini Ne Za A Koya

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,tambayar mu ta yau ita ce wani ilimin Addinin ne ya kamata Mutane su kowa?wannan tambaya tanada mahimanci haka zalika amsarta tanada mafimancin gaske a wajen mutane baki daya,  amma kafin mu shiga shirin, bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.


****************************Musuc***************************


Masu saurare,kamar yadda shirin ya saba zai fara da Alkur’ani mai girma, inda yake kiran Mutane baki daya da su koyi ababen da za su tabbatar musu da rayuwa mai kyau wacce za ta sanya su samu sa’ada da karama a duniya da Lahira, wannan ilimi shine  ilimin sanin ubangiji da kuma yadda za a bauta masa wanda ta hanyarsa ce dukkanin wani Alheri ke rayuwa da wujudin mutune, A cikin Suratu Anfali Aya ta 24 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya Ku Wadanda Kuka Ba Da Gaskiya,Ku amsa Kiran Allah da na Manzo idan ya yi kiran Ku ga Abin da zai kyauta rayuwarku, Kuma Ku Sani cewa Allah yana Kange tsakanin Mutum da Zuciyarsa, Kuma Hakika wurinsa ne za a tattara ku) a cikin Suratu Juma’a Aya ta 2 Allah madaukakin sarki ya ce:(shi ne wanda ya aiko Manzo cikin mutanen da ba sa karatu da rubutu daga gare su, yana karanta ayoyinsa a gare su yana kuma tsarkake su, kuma yana sanar da su  littafi da hikima  ko da yake da can sun kasance lallai cikin bata mabayyani) wadannan Ayoyi masu albarka sun amsa wannan tambaya a yayin suka bayyana mana  shashin ilimin da yake raya mutune, domin haka wajibi ne ga ko wani mutum ya nemi sanin Littafin mai girma i mai girma biya koyarwa da kuma bayyanan Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare  kuma da na iyalan gidansa tsarkaka, kazalika,wajibi ne Mutune ya koyi ilimin zarkake zuciya wato ilimin Akhlaqi da kuma ilimin fikhu na sanin hukunce-hukuncen Addini da kuma ilimin Hikma wanda Allah madaukakin sarki ke cewa duk wanda ya baiwa wannan ilimi hakika ya bashi Alheri mai yawa.


Masu saurare, idan muka koma hadisan Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma na iyalan gidansa  tsarkaka za mu samu karin bayyani kan amsar wannan tambaya, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Kazim (a.s)  ya ce wata Rana Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiga cikin Masallaci sai ya tarar da Mutane sun kewaye wani Mutune sai ya ce minene wannan? Sai suka ce masa Allama ne, sai ya tambayesu ma’anar Allama? Sai suka ce masa wanda ya fi kowa sanin nasabi da kuma tarihi na tsatson Kabilar Larabawa da kuma ababen da suka faru da su gami da zamanin jahiliya da kuma  shi’iri ko kuma rubutattun wakokin Larabawa , sai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce :(wannan ilimi ba zai cutar da wanda bai sanshi ba kuma ba zai amfanar da wanda ya sanshi  ba, domin shi  ilimi kashi uku ne, sanin Ayoyi bayanannu da kuma sanin Sunna da ake bi, sai kuma sanin farillai ma’ana ilimin Fikhu, kuma mallakar wadannan ilimi Al’amuranmu ne). hakika masu saurare maluma sun fassara wannan hadisi da cewa bayyananun Ayoyi shine koyar ilimin Akida ma’ana na sanin Ubangiji, sunar bi ita ce koyi da hallayen Manzon Allah da kuma wasiyansa tsarkaka sai kuma farillai da kuma hukunce-hukunce na ilimin Fikhu , shine ko wani musulmi ya kamata ya koyi ilimin da yake bukata na sanin Allah, hukunce-hukunce da ya rataya a kansa gami da sanin kyawawen halaye da dabi’u domin ya yi koyi da su) amma kaolin ma’aikin Allah na cewa dukkaninsu mallakarmu ne malumai sun fassara hakan da su dukkanin wadannan ilmomi masu albarka daga wajen Ma’aikin Allah da kuma iyalan gidansa tsarkaka ne ya kamata a koye su.


**********************Musuc****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa,hadisai da dama sun yi umarni tare ta’akidi na cewa wajibi ko wani musulmi ya koyi  ilimin sanin Allah madaukakin sarki da kuma siffofinsa , umarnisa da kuma hanisa haka zalika ya san abinda zai nisantar da shi bin madaidaiciyar hanya domin ya kauce masu.a cikin Littafin Sharhul Usuli Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce :( yadda na samu ilimin Mutane dukkaninsu sun kashi ,kashi hudu, na farkonsa  ka san ubangijinka, na biyunsa ka san yadda ya halicceka, na uku ka san minene ya ke so da kai ma’ana saboda minene ya halicceka, na hudu ka san ababen da za su fitar da kai daga Addininka). Masu saurare hadisai da dama sun yi ishara gami da ta’akidi a kan cewa ko wani musulimi ya kamata ya san abinda zai gyara masa zucuyarsa da kuma abinda zai bata ta wanda ta hakan ne kawai zai iya samun rayuwa mai kyau tare kuma da kaucewa duk wata rashin lafiya ta zuciya, a cikin Mausu’a ta Biharul Anwar juzi’I na 78 an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya ce:( ilimin da ko wani musulmi ya kamata ya sani wanda ta hanyarsa ne aiyukan mutun za su gyaru, kuma abinda kake da shugabanci a kansa shine wajibi a gareka).masu saurare wannan hadisi yana ishara ne kan mahimancin koyan ilimin hukunce-hukuncen Addinin musaman ma abinda aka wajabtawa dan adan da kuma abinda aka haramta masa.har ila yau a cikin wata riwayar Imam (a.s) ya ce: (ka koyi ilimin da zai shiryar da  zuciyarka ta tsarkaka kuma ta kyaru sannan kuma ya  bayyana maka abinda zai bata ta (wato zuciyar) ka kodeita da ilimin da zai kara maka guzirin Lahira, kadda ka shagaltu da ilimin da rashin koyarsa bai zai rageka da komai ba, kuma saninsa ba zai amfanar da kai komai ba) masu me yuyuwa abinda Imam (a.s) yake nufi da ilimin da rashin koyarsa bai zai rageka da komai ba, kuma saninsa ba zai amfanar da kai komai ba shine ilimin da kan iya jefa bawa cikin batan Basira kamar ilimin son duniya, da kuma bin son rai, da kuma zama a majalisin malalata da masu sabon ubangiji , Allah yak are mu da irin wannan ilimi da kuma zama a majalisin fasikai.


Masu saurare a karshen abinda za mu bayyana dangane da amsar wannan tambaya bisa fahimtar mu na Ayoyin da suka gabata gami da hadisan Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma na iyalan gidansa tsarkaka shine ilimin  ya kamata ko wani musulmi ya sani na addini, ilimin sanin Ubangijinsa, ilimin hukunce-hukunce ma’ana ilimin fikhu da a cikinsa zai gane minene aka umarcesa da aikiatawa kuma minene aka haneshi da aikatawa sai kuma ilimin da zai tsarkake zuciyarsa da kuma ilimin da zai masa shamaki wajen bin hanyar ubangiji domin ya kauce masa, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon koyon ilimin Addini  mai albarka wanda zai mana jagora zuwa sanin ubangiji da kuma rabauta a Duniya Da Lahira.


***************************Musuc******************************Masu saurare anan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki sai a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin da yardar Allah, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala musaman ma A I K ni da