Mar 06, 2016 19:32 UTC
  • karamin Sani kukumi-Mahimancin Taklidi

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,shirin na yau zai bayyana kan mahimancin Akida ga rayuwar musulmi, kamar yadda aka sani babu taklidi ga Usuludin kamar yadda ko wani marja’I yake rubutawa a farkon risalarsa, wajibi be ga ko wani mumuni ya kasance imaninsa na sanin Allah da Akida bisa bincike da yakini, shin ko minene sirrin yin haka? Wannan ita ce tambayar ta yau, amma neman amsar ga wannan?


************************Musuc********************************


Masu saurare kamar yadda shirin ya saba, za mu fara da Littafin Allah mai girma, a cikin Hajji Aya 54, Allah madaukakin sarki ya ce:(Don kuwa Wadanda Aka bai wa ilimi su san cewa shi (Alkur’ani) gaskiya ne daga Ubangijinka yake,sai su ba da gaskiya da shi sannan Zukatansu su nutsu da shi.Kuma hakika Allah lallai Mai shiryar da wadanda suka ba da gaskiya ne zuwa ga tafarki madaidaici) domin haka, giniwar Akidar kirki shi ke sanya zuciyar mumuni ta nutsu tare da kasancewa shiryayya wajen aiki da umarnin ubangiji da kuma tafiya zuwa tafarki madaidaici, kamar yadda imani na gaskiya da Asalin Akida shi ke mutune ga cikka duk wani nauyi na Addini da aka dora masa wanda hakan zai sanya ya samu lada mai girma daga wajen Ubangiji, a cikin suratu Nisa’I Aya ta 164 Allah madaukakin sarki ya ce:(Amma Masu Ilimi na Gaskiya daga cikinsu (watau ma’abuta Littafi) da Mumunai sun ba da gaskiya Da abin da aka saukar maka da kuma abin da aka saukar gabaninka, da kuma masu tsai da Salla da masu ba da zakka da kuma masu ba da gaskiya da Allah da ranar Lahira. Wadancan ba da dadewa ba za Mu ba su lada mai girma (watau Aljanna)). Masu saurare asasin akida ta gaskiya ita ce ke kai mutune zuwa martabar meka wuya zuwa ga al’amarin Allah wanda kuma hakan shi ke tseto mutune daga Bata da kuma tabbatar da kiran Ubangiji, a cikin Suratu Rumu Aya ta 52 da kuma ta 53 Allah madaukakin sarki ya ce:(Sannan Hakika ba kai ba ka iya jiyar da matattu, kuma ba ka iya jiyar da kurame kira lokacin da suka juya suna masu  ba da baya.*kuma  kai ba mai iya shiryar da makafi(watau batattu)ba ne daga batansu , ba wadanda kake iya jiwarwa sai masu ba da gaskiya da Ayoyinmu, suna Musulmi) masu saurare bayan wadannan bayanai na Alkur’ani mai girma, hadisai da dama sun bayyana cewa Asasin Akida ta gaskiya ita ke shiryar da mutune ya cika taklifinsa na shari’a kamar yadda aka bukata daga bisani kuma ya samu yardar Allah madaukakin sarki, a cikin litattafen Amaly da Almahasin na shek Saduk an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s)ya ce:(Allah madaukakin sarki ba ya karbar aiki sai da sani,kuma ba ya karbar sani sai da aiki,wanda kuma ya sani  saninsa kuma  ya yi masa jagora zuwa ga aiki, kuma duk wanda bai yi aiki ba, babu sani a gareshi, domin shi Imani yana tare da aiki). A cikin littafin Wasa’il an ruwaito hadisi daga Muhamad bn Marid ya ce:na cewa Abi Abdullah Imam Sadik (a.s) a wani hadisi da aka ruwaito an ce ka ce idan mutune ya sani ya aikata abinda yake so. Sai imam (a.s) ya amsa masa da cewa hakika na fadi wannan magana. Sai Rawin ya ce ko da sun yi zina, sun yi sata ko kuma sun sha giya? Sai Imam (a.s) ya ce: إنا الله وإنا إليه راجعون، ma’ana Mu mallakar Allah ne  kuma mu wurunsa za mu koma , wallahi ba su yi mani adalci ba, abinda na fada shine idan ka sani to ka yi aikata yadda kake so  kadan ko diyawa na Alheri daga abinda ka sani)


************************Musuc*********************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, yin aiki ba a bisa ka’idar gaskiya ba, ba za ta amfani Mutune ba wajen samun kamala, kuma ba za ta sanya shi ba cikin aminci na fadawa cikin fitittunu, domin Asasin Akida ta gaskiya ita ce tabbacin tsira daga fititunu da kuwa waswasin shaidanu.A cikin Littafin Ikhtisas na shek Mufid an ruwaito hadisi daga shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce: (mai yin ibada  ba tare da sani ba, kamar  aikin babban giwa ne ma’ana mutune ya dinga yin aiki ba tare da lad aba, raka biyu ta malami ta fi raka’a saba’in ta jahili) ma’anar malami a wannan hadisi shine masani da ainafin  Akida ta gaskiya kuma jahili, wanda ya jahilce ta.a karshen hadisin imam Ali (a.s) ya yi ta’aliki ga maganarsa inda ya ce domin shi Malami masanin Akida ta gaskiya , idan wasu fitintunu suka tunkareshi zai fita ya kuma tsira sanadiyar amfani da iliminsa, shi kuma Jahili idan ta tunkare shi zata tafi da shi . har ilayau Imam (a.s) ya ci gaba da cewa aiki kadan tare da ilimi mai yawa ya fi aiki mai yawa tare da ilimi kadan da kuma kokonto gami shubuha).


Masu saurare,hadisai da dama sun bayyana mana cewa amfanuwa da  sani da asalin Akida gaskiya shike arzuta mutune ya samu tsoron Allah madaukakin sarki daga bisani kuma yay i kokari wajen samun yardarsa madaukakin sarki.A cikin Suratu Fadir Aya ta 28 Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika malamai ne kawai suke tsoron Allah daga bayinsa) a cikin Littafin Kafi , daga cikin wani bangare da wasiyarsa ga salihin bawan nan Hisham bn Hakam, shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya ce: (Ya Hasham hakika babu tsaron Allah ga wanda bai san Allah ba, kuma wanda bai san Allah ba,bai sanyawa zuciyarsa ba akidar sanin sa ba, sanin Allah shi ke sanya Bawa akikar gaskiya a zuciyarsa ya kuma shiryar da shi zuwa ga Bautar Allah madaukakin sarki).har ila yau a cikin wani hadisin Imam (a.s) ya ce:(babu tsira sai da da’a, babu da’a sai da Ilimi, kuma Ilimi sai an koya shi kuma koyo saida hankali, kuma babu wani hakikanin Ilimi sai ilimin ubangiji).


A cikin Littafin Kanzul Fawa’id, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(ku kautata Nazari ga abinda jahilcinsa ba zai kai ga kokarinku ba, ku yiwa kawunaku Nasiha, ku yi kokari wajen neman sanin abinda ba za a yi muku uziri ba a kan jahilcinsa, hakika Addinin Allah ya nada rukuna, kuma wanda ya jahilcesa ba zai amfanu da tsananin kokarinsa wajen yin ibada a zahiri, kuma babu cutarwa ga wanda ya koyesu, ku kyautata nemansu da niya mai kyau, babu wata hanya ga kowa saida taimakon Allah madaukakin sarki).


Masu saurare a takaice amsar wannan tambaya ita ce sanin Allah madaukakin sarki da abinda ya shafi Asalin Akida shine jigon tabbatuwar mumuni wajen bautawa Allah madaukakin sarki kyakkyawar Ibada,tare da bin hanya madaidaiciya, daga bisani kuma Mutune ya kai ga Kamala tare da samun rayuwa mai kyau a duniya da Lahira, da fatan Allah madaukakin sarki ya arzita mu da wannan.


****************************Musuc*********************************


Masu saurare, anan za mu dakata, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman ma Injeniyanmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama aleku wa rahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.