karamin Sani kukumi-Mahimancin Taklidi (2)
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,shirin na yau zai bayyani ne dangne halarcin Taklidi, abin tambaya a nan wasu sun ce Alkur’ani mai tsarki ya aibata yin taklidi bayan maluman fikhu ke bayyana cewa wajibi ne ga wand aba mujtahidi ba yayi taklidi ga malami mujtahidi to ta yaya za mu hada wannan hukunci da wancan? Ma’ana shin a kwai Wani taklidi ne aka amince da shi da kuma wanda aka aibata? Idan amsar ta kasance Na’am to ta yaya za mu iya babbance su ? Sai abiyo domin jin amsar wadannan tambayoyi.
******************Musuc***************************
Masu saurare kamar yadda shirin ya saba za mu fara da Littafin Allah mai tsarki wato Alkur’ani mai girma, inda a cikinsa za mu samu ayoyi da dama wadanda suke aibata yi taklidi da iyaye, za mu takaitu da wadannan Ayoyi biyu masu albarka wadanda suke bayyani dangane da sirrin hana yin taklili da kuma ma’anar Taklidin da aka aibata, a cikin Suratu Zuhurufi daga Aya ta 20 zuwa ta 25 Allah madaukakin sarki ya ce:( Suka Kuma ce:”Da Allah Arrahamanu Ya So, da Mu bauta musu ba (watau Mala’ikun)” Ba Su da wani takamaiman sani na wannan. Su dai ba abin da suke yi sai kagen karya kawai*ko kuwa Mun ba su wani littafi ne gabaninsa(Alkur’ani), saboda haka suke rike da shi kam-kam.*A’a, cewa dai suka yi mun sami iyayenmu a kan wani Addini ne, mu kuma lallai sawunsu muke bi* kuma haka abin yake, ba mu taba aiko wani mai gargadi ba,a wata alkarya a gabaninka sai mawadatanta sun ce hakika mu mun sami iyayanmu a kan wani addini, kuma hakika mu hanyarsu muke kwaikwayo* Y ace da su: “(yanzu za ku yi koyi da su) ko da na zo da abin da yake shi ya fi shiryarwa a kan abinda kuka sami iyayanku a kansa?” Suka ce Hakika mu masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne”. *Sai Muka saka musu. To duba ka ga yadda karshen masu karyatawa ya kasance). Masu saurare, idan muka nazari a kan wadannan Ayoyi masu albarka za mu fahimci cewa taklidin da aka yi ki a cikin Nassin Alkur’ani shine ya kasance bisa ta’asubi da kabilanci na madanda suke yi ido rufe daga magabata da kuma iyaye,domin shi irin wannan Taklidi na zuwa ne daga jahilci da kuma rashin ilimi kamar yadda Alkur’ani mai tsarki ya ce(Ba Su da wani takamaiman sani na wannan) kuma hakan na zuwa da bin Al’adu, son dadi da kuma kin yin kokari wajen neman hanyar tsira kamar yadda Al’kur’ani ya ce:( sai mawadatanta sun ce hakika mu mun sami iyayanmu a kan wani addini, kuma hakika mu hanyarsu muke kwaikwayo) domin haka ne mai yin taklidin ido rufe zai fada cikin mumunar makoma.amma idan mai taklidi ya rabu da ta’asubanci , jahilci da kuma bin Al’adu, kuma taklidinsa ya kasance bisa ilimi, yayin da yake taklidin malamin da ya san cewa mai bincike ne a kan iliminsa, hakan ba zai zamanto baa bin ki,saidai ma ya zamanto abinda ya kamata bisa hukunci hankali,kuma irin wannan taklidi shine taklidin wanda ba Mujtahidi ba ga Mujtahidi a cikin hukunce-hukuncen Addini.kuma yanayin mai irin wannan taklidi kamar yanayin wanda zai je wajen likita ne a lokacin da yake rashin lafiya ya karbi magani bayan da ya fahimci kwarewarsa a kan wannan fanni,kazalika kamar yadda shima Likitan na iya zuwa wajen marar lafiyar kansa a bangaren da yak ware, misali idan ya kasance babban malami wanda ya kai matsayin ijtihadi sai yayi taklidinsa a bangaren hukunce-hukuncen Addini.
****************************Musuc******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani dangane da taklidin da maluman fikhu suka wajanta wanda kuma ke cikin furu’uddin ma’ana rashan Addini wanda yake bukatar kwarewa ta ilimi kafin Mujtahidi ya fitar da su, amma kamar su Akida, da kuma Usuluddin kamar su wajibcin sallah,bada Zakka, zuwa Hajji, yin Azumin cikin watan Ramadan da kuma wulaya babu taklidi a cikinsu.idan muka koma cikin Hadisai kwa da farko sun yi galgadi kan yin taklidi ido rufe wanda ke tattare da ta’asubanci da kuma jahilci kamar yadda Ayar da ta gabata ta Ambato(Suka Kuma ce:”Da Allah Arrahamanu Ya So, da Mu bauta musu ba) kamar yadda Imam Sadik (a.s) ya ce:(na haneku da yin Taklidi, domin duk wanda ya yi taklidi a cikin Addininsa ya hallaka saboda Allah madaukakin sarki(sun dauki malimansu da fada-fadansu iyayen giji maimakon Allah)suratu Taubat Aya ta 31ku saurara wallahi ba su yi sallah da Azumi dan su ba, saidai sun halarta musu ababen da suke haramun ne kuma suka harmta musu abinda yake hala ne sai suka yi musu taklidi a kan hakan suka kasance suna yi musu bauta alhali ba su fahimci hakan zai faru ba) masu saurare wannan hadisi ya shafi ko wani irin taklidi har da ma wanda ake yiwa malumai ya kasance bisa sika da kuma samun tabbaci da yarda na tsoron Allah su da kuma kwarewarsu a kan ilimin da ake yi musu taklidi, a tabbatar da cewa ba sa yin wata fatawa a kan karan kansu ransu ,duk abinda suke fada sun samo shi daga cikin Alkur’ani da hadisan Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.
Masu saurare da wannan za mu fahimci cewa yin taklidi ga Malumai masu tsoron Allah kamar yin taklidi ne ga Alkur’ani mai tsarki da kuma sunna.kuma yin hakan shike tabbatar da tsayawar Mutune a bisa Addinin gaskiya,wanda kuma ya yi taklidi ga maluman da bas u tsoron Allah, wadanda suke fitar da fatawa bisa son ransu da kuma wani matsi da sarakuna kamar ya bata Addininsa ne kuma yin hakan zai fitar da shi daga Addininsa ya kasance yana bautawa wanin Allah madaukakin sarki.Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya dauki addininsa daga bakunan Mutane to wata rana mutanan za su fitar da shi daga cikin Addini,kuma duk wanda ya dauki Addininsa daga Littafin Allah da sunna,zai kasance mai riko da Addininsa ko da dukkanin duwatsu sun kushe shi ba zai kauce daga barin Addininsa ba)
Masu saurare a takaice amsar tambarmu ita ce a kwai nau’I biyu na taklidi,wanda shari’a ta amince da shi da kuma wanda ta aibata wanda kuma shine yin taklidi bisa ta’asubanci da jahilci ido rufe kamar mutune zai yi taklidi da wanda bai cancanta a yi taklidin da shi ba ko saboda karamcin ilminsa ko kuma tsoron Allansa, taklidin da aka shri’a ta amince da shi shine komawar wand aba kwararre bag a kwararre a bangaren da yak ware a kansa wanda kuma ya kasance malami mai tsoron Allah wand aba ya wata fatawa bisa son rai.
*******************Musuc**********************************
Masu saurare, a nan za mu dasa Aya saboda lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman ma Injiniyanmu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni madugun shirin nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.