Mar 06, 2016 19:35 UTC
  • karamin Sani kukumi-Mahimancin sanin Allah

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau minene mahimancin sanin Allah? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari wannan.


**********************Musuc**************************


A shirye-shiryen da suka gabata, masu saurare mun fahimci cewa babu wani ilimi da ya fi ilimin sanin Ubangiji madaukakin sarki domin shine hakikahin ilimi wanda ko wani Bawa ya kamata ya fara sani a rayuwarsa domin da shi Mutune zai yi rayuwa mai kyau,da kuma shine mutune zai bautawa Allah madaukakin sarki wanda saboda da hakan Allah subhanahu wa ta’ala ya halici bayinsa, har ila yau ta hanyar wannan ilimi ne Bawa zai kai ga cimma tsoron Allah wanda zai kare shi fadawa cikin sabo,domin haka masu saurare sai a biyo domin amsar tambayar daga nauyaya biyu wato Alkur’ani da tafarkin iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka. Hakika sakin Allah shine mabudin farko na tsarkake Aiyuka ma’ana suka kasance tsarkakaku da za su bada sakamako mai kyau.hadisai da dama sun yi ishara da hakan,kamar yadda shehin malamin nan mai tsoron Allah Bn Waram ya ruwaito a ciikin littafinsa mai suna Tanbihul khawatir: wani Mutune ya tambayi Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka kan cewa wani aiki ne ya fi:sai Ma’aikin Allah ya ce: (ilimin sanin Allah da kuma ilimin sanin hukunce-hukuncen Addininsa) haka ya kasance Manzon Allah yana maimaita wannan Magana ga wannan bawan Allah.sai matanbayin ya ce Ya ma’aikin Allah na tambayeka dangane da aiki kuma kai ga bani amsa dangane da ilimi.sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce masa hakika wannan sani (ma’ana ilimin sanin Allah da kuma ilimin sanin hukunce-hukuncen Addininsa)zai amfaneka koda da aiki kadan shi kuma Jahilci (jahilcin ilimin sanin ubagiji da sifoffinsa) ba zai amfaneka ko da za ka aikata aiyuka masu yawa).a cikin wani hadisin kuwa Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(kimshiki da kuma Asasin Addini sanin Allah madaukakin sarki,tabbaci, yakini da kuma hankali mai amfani domin shi ke hana Bawa fadawa cikin sabon Ubangiji, domin sanin Allah shi ke gadar da Yakini, bayan haka sai Nutsuwa a cikin zukata, kamar yadda Hankali ke kasancewa mai tsaro wajen kare mutune daga fadawa cikin sabon Allah wanda ke kai bawa ya zamanto daga cikin tababbu).ta haka ne masu saurare za mu fahimci cewa sanin Allah madaukakin sarki na sanya Bawa ya dandana dadin hakikanin Imani, shin sanin Allah ya kan kai ga Bawa ya cimma kololuwar Imani? Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka :(wanda ya fi ku imani, wanda ya fi sani).(wato sanin Allah madaukakin sarki kuma ya yi aiki da saninsa) Littafin Ma’arijul Yakin fi Usuluddin.


**************************Musuc***************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da littafin Amaly na Shek Tusy inda a cikinsa aka ruwaito hadisi daga Muhamad bn Sama’a ya ce:wasu daga cikin sahaban Imam Sadik (a.s) sun tambayi Imam (a.s) daga cikinsu y ace: Ya Imam bani labarin minene fiyeyyen aiki? Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa: tauhidinka da Ubangijinka,wato yarda da kuma yadda dayanta Allah da kuma yadda ya siffanta shi, sai kuma na biyu ya ce Ya Imam wani Zunubi ne ya fi ko wane girma? Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa mai baiwa Ubangiji kammani da sifoffi irin na halittu). A cikin wani hadisi na daban shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika mafi fifikon wajibci da farillai a kan mutune shine sanin Ubangijinsa da kuma samun tabbaci a kan bautarsa).masu saurare abin fahimta a cikin wadannan hadisai biyu da suka gabata, shine sanin Allah madaukakin sarki shine Asali da kuma kimshikin dukkanin Aiyuka kyawawa domin haka nema kokari wajen cimma wannan ilimi ta hanyar da suka dace wajibi ne ga ko wani Dan Adam.har ila yau masu saurare, sanin Allah madaukakin sarki yak an sanya dan Adam ya dandana dadin Imanin gaskiya kuma hakan bai takaita kawai bag a imanin Bawa da kuma aiyukansa na gari ba, bari mu saurari kyawawen kalamai na shugaban masu kataita Allah Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) a yayin da yake siffanta Mala’iku  cikin riwayar da Shek sharif Ridah ya kawo a cikin Littafin Nahjul-Balaga.