Mar 06, 2016 19:37 UTC
  • karamin Sani kukumi-Mahimancin sanin Addini (2)

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, shirin na yau zai dora a shirin da ya gabata,inda muka yi bayyani kan mahimancin sanin Allah a rayuwar Mutune? Amma Kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.


**********************Musuc**************************


Masu saurare da shirin da ya gabata mun amsa tambayar wannan tambaya a jumulci bayan bincike a cikin Littafin Allah mai tsarki da kuma sunar Ma’aikinsa Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare kuma ta iyalan gidansa tsakaka, a shirin na yau za mu ci gaba da amsa tambayar ne fila-fila, hakika nasossi da dama sun tabbata da cewa sanin Allah madaukakin sarki shine Asasin ilimi mai amfani, ma’ana da sanin Allah ne ilimi ke amfana, idan kuma bah aka ba ilimin zai zamanto kamar jikin da aka sare kansa kaka babu rayuwa a tare da shi.a cikin Littafin Tauhidi na shek Saduk an ruwaito hadisi daga Ibn Abas yardar Allah ta tabbata a gareshi y ace:wata rana wani Balaraban kauye ya zo wajen Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce Ya Ma’aikin Allah ka sanar da ni wani ilimi daga cikin lilimi mai zurfi, sai Ma’aikin Allah ya ce masa mi kayi da ilimin farko da ya kamata ko wani musulmi ya sani? Sai y ace wani ilimi ne na farko da ko wani Bawa ya kamata a ce ya sani? Sai Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce:sanin Allah hakikanin saninsa, sai mutuman ya ce ya ye ne sanin Allah hakikanin sani? Sai Ma’aikin Allah ya ce Kasan Allah ba tare da misali ba, da kuma siffantashi da halitunsa ba da kuma yi masa kishiya wajen bauta,domin shi Allah shine na farko wanda bashi da na biyu  shine zahiri da badini sannan kuma na farko da na karshe babu daya da ya kasance tamkarsa bas hi da abokin tarayya, sanin haka, shine hakikanin Sanin Allah madaukakin sarki), a cikin Littafin Guraru Hikam,an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) inda a cikin hadisi ya bayyana ma’anar Tauhudi a jumulce (Tauhidi shine rayuwar Rai).


Masu saurare, hakika Sanin Allah shine mabodin bauta masa na gaskiya kuma saboda manufar hakan ne aka halici Aljan da Mutune kamar yadda Alkur’ani mai tsarki ya sarraha, a cikin Zariyati Aya ta 56, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ban Kuwa halicci Aljan da Mutum ba sai don su bauta min),hakika shek Saduk (yardar Allah ta tabbata a gareshi) ya ruwaito wani hadisi a cikin littafinsa mai suna Kitabu Tauhid , inda a cikinsa aka ce wata Bani Hashim suka cewa shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) Ya Abal Hasan ka hau minbari ka shiryar da mu  a kan ilimin da za mu bautawa Allah madaukakin sarki da shi, ma ana ya bayyana musu nagarcecciyar hanyar da za su bautawa Allah madaukaki sarki, Sai Imam Ali (a.s) ya Hau Minbari ya yi shuru saboda mahimancin Maudu’in har wani lokaci har sai da ta kai wasu daga cikin mahalartan sun fara Magana, sai Imam (a.s) yayi godiya ga Allah madaukakin sarki sannan ya yi Annabi da iyalan salati, sannan ya ce:(farkon Ibadar Allah saninsa kuma Asalin Saninsa shine Tauhidi) , hakika masu saurare, sanin Allah madaukakin sarki shine mabudin bautarsa kuma daga bisani Bawa ya wadatu da bautar waninsa.a cikin Littafin Ilalu shara’I’I shek Saduk ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce wata Rana Imam Husain bn Ali (amincin Allah ya tabbata a garesu) ya fita wajen sahabansa y ace musu :Yak u Mutane hakika Allah madaukakin sarki ya ambata cewa bai halicci bayi ba sai don su san shi, idan kuma sun san shi sai su bauta masa, idan kuma sun bauta masa sun wadatu daga bautar waninsa).


**********************Musuc*****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa,masu saurare sanin Allah madaukakin sarki shine wasilar tabbatar da hakikanin Ibada kamar yadda wannan hadisi mai albarka da aka ruwaito cikin littafin Attauhid ya bayyana , Maulana Imam Kazim (a.s) ya ce:(wasu Mutane sun cewa Imam Sadik (a.s) lalle mun kasance muna rokon Allah ba tare da samun amsa ba, ma’ana sun jima suna rokon Allah amma har wannan lokaci , a cewarsu Allah bai amsa rokon da suka yi masa ba, Sai Imam Sadik (a.s) ya ce: dalilin haka shine kun kasance kuna bautawa wand aba ku sani ba ne).kamar yadda zurfafa a kan sanin Allah ya kan sanya Bawa ya zurfafa da kara kaimi wajen bautarsa, daga bisani wajen samun amsar Addu’a,domin Addu’arsa za ta kasance cikin kyakkyawan saninsa, domin hikimarsa,fadin ramarsa, kusancinsa da bayinsa da kuma Kudurarsa tana bisa komai. Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(daga cikin Mutane wanda ya fi ko kowa sanin Allah shi ne ya fi meka bukatarsa a gareshi), har ila yau a cikin Addu’arsa da yayin cikin cikin Masallacin Ju’ufi:(Ya Ubangijina ta ya ya zan kira ka alhali na tabbatar da ina saba mka, kuma ta ya ya zan ki kiranka alhali na sanka).


Masu saurare, sanin Allah madaukakin sarki shine wasilar samun takwa da tsoron Allah wadanda su ne ke kiyaye Mutune  daga fadawa cikin sabo da kuma abinda zai kai shi ga tabewa, shugabanmu Amiru mumunin (a.s)ya ce:(duk wanda ya san Allah madaukakin sarki ba zai tabe ba har abada) har ila yau a cikin wani Hadisin Imam (a.s) ya ce:(ina mamaki ga wanda ya san Allah ta ya ya ba zai tsanata tsoronsa ba) a wani hadin kuma Imam (a.s) ya ce:(wanda ya fi sanin Allah daga ciki Mutane shine wanda ya fi tsoron Allah).a karshen shugaban muwahidai Aliyu bn Abi talib (a.s) a cikin daya daga cikin khudubobinsa yayin da yake wassafa fajirai da fasikai yana mai cewa:(da sun yi tunani ga girman Kudura da kuma Ni’imarsa da sun komo kan hanya,kuma da sun ji tsoron Azaba mai radadi, saidai kuma zukatansu sun kasance marassa lafiya idanuwansu sun shiga cikin juna! Ba sa gani ganganiyar halitar da Allah madaukakin sarki ya halitta,ta yay a zai yi hukuncin halittarsa da kuma yadda ya tabbatar da tsarinsa, , ya kuma halarta masa ji da gani ya daidaita kashishuwansa, Azaba ta tabbata ga wanda ya yi inkarin mai wannan kudura kuma yayi jayayya ga wannan tsari…)


Masu saurare, a takaice sanin Allah madaukakin shine asasin abinda ke sanyawa a samu ilimi mai amfani,kuma ta sanin Allah ne Mutune zai yi hakikanin rayuwa mai nagarta, kuma ya gudanar da ibada ta gaskiya, har ila yau ta sanin Allah hakiknin tsoron Allah, tsira daga tabewa da kuma karbar Addu’a.


***************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.