Mar 06, 2016 19:41 UTC
  • karamin Sani kukumi-Mahimancin sanin Addini (3)

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayani kan mahimancin Sanin Allah madaukakin sarki a rayuwar Mutune da kuma samun sa’adarsa gami da tsira, ganin mahimancin maudu’in a yau ma za mu ci gaba da shi, amma kafin mu shiga shirin ga wannan.


************************Musuc********************************


Masu saurare, hakika daga cikin tasirin ilimin sanin Allah madaukakin sarki shine samarwa Dan Adam Izza kuma ya fitar da shi daga cikin kankin gumcin zuciya da kuma kaskanci meka bukatu ga wasu,shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(duk wanda ya zaunar da ilimin Allah a Zuciyarsa,za a sanya masa wadatuwa daga halitun Allah) hakika masu saurare sanin Allah madaukakin sarki ya kan sanya haske a cikin zukatan bayi ta yadda za su fahimci cewa dukkanin Alheri daga Allah madaukakin sarki ne, kuma duk wani alheri da Bawa zai samu daga wajen wani Mutune to daga Allah ne, kuma duk wani alheri da bawa zai samu daga waninsa na a matsayin wasila ko dalili na isar ga Alherinsa zuwa ga bayinsa, kuma mumuni ba ya nemen wani Alheri sai daga wajen Allah Tabaraka wa Ta’ala, kamar yadda sanin Allah madaukakin sarki ya kan ‘yantar da mutune daga son duniya, domin shin sanin Allah ya kan buda zuciyar mutune wajen neman Alheri dawamamme da kuma babbar yarda,shugaban mumunai kuma shugaban masu dayanta ubangiji amincin Allah ya tabbata a gareshi ya ce:(ribar Sani, shine kwadayi ga gidan da   ba shi da karshe ) ma’ana ribar Sani, shine mutune ya aikata aikin da zai sanya yana shaukin haduwada ubangijinsa, masu saurare, wannan shine tasirin sanin Allah, ma’ana gudun duniya da kuma ‘yantuwa daga kanginta,a cikin wani Jami’in hadisi da sikatul Islam kulaini ya ruwaito a cikin Littafinsa mai suna Raudatul Kafi, shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya bayyana cewa:(da Mutane sun san irin falalar dake tattare a cikin Sanin Allah,da ba su zura idanunsu ba a kan dadin da Allah madaukakin sarki ya horewa makiya daga rayuwar Duniya da kuma ni’imar dake cikinta, da kuma ya kasance abinda suke takawa da kafafuwansu ya fiye musu ga rudun rayuwar Duniya , da kuma sun ni’imtu da sanin Allah madaukakin sarki tare kuma da dandana dadin da ba ya karewa na koramun Aljanna tare da waliyan Allah, Hakika sanin Allah madaukakin sarki,aboki ne a yayin da bawa ke cikin kadaita na babu wani a gurinsa  kuma sahibi ne daga duk wata kadaitaka,haske kuma daga duk wani duhu, karfi ne kuma daga duk wani rauni, waraka ne kuma daga duk wata rashin lafiya) har ila yau Imam (a.s) ya ci gaba da bayyana tasirin sanin Allah wajen dagewa da juriya a kan Addinin gaskiya daga duk wasu wahalhalu:(hakika kuma ya kasance a gabaninsu mutanan da aka dinka kashe su  da kuma konasu , duk da haka sun ci gaba da bayyana Umarnin Allah, da kuma yadda duniya ta yi musu gumshi, sun kasance ba za mayar da martani a kan abinda ake yi musu, ba don komai ba sai don yardar Allah mabuwayi abin yiwa godiya, ku nemi makamancin  matsayinsu daga wajen Allah Ubangijinku, ku yi hakuri a kan wahalhalun duniyarku, sai ku cimma irin ladan kokarin da suka yi), har ila yau masu saurare daga cikin Albarkatun dake tattare da sanin Allah garkuwa daga girman kai, domin girman kai wata cuta ce daga cikin zukata da take kai mai shi zuwa hallaka, shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce :(bai kamata ba ga wanda ya san girmar Allah, ya dauki girman kais u dorawa kansu , hakika matsayin wadanda Allah ya girmama su kaskantar da kansu a gareshi)


********************Musuc*****************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, daga cikin albarkar sanin Allah ,karuwar girman soyayar Allah madaukakin sarki a cikin zukatar Arifai,ta yadda za su ci gaba da gudanar da ibadarsu cikin shauki da soyayya wanda ke kara tabbatar da nutsuwa cikin zukuta.a cikin Littafin Alkhisal, Shekh Saduk ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Iman Sadik (a.s) ya ce:(hakika bautar da Mutane suke yiwa  Allah madaukakin sarki nau’i uku ne, wasu Mutane na bautawa Allah saboda kwadayin Ladansa, irin wannan bauta itace ibadar masu kwadayi, wasu Mutanan kwa na bautawa Allah saboda tsoron wuta, irin wannan ibada itace ibadar bayi, ni kuma ina bautawa Allah saboda soyayyata a gareshi, kuma irin wannan ibada itace ibadar amintattu, domin Allah madaukakin sarki a cikin littafin sa mai tsarki ya fada cewa(duk wadanda suka zo da kyakkyawan (aiki),to suna (da lada) fiye da shi, kuma sun amintattu ne daga firgitar wannan rana)suratu Namli Aya ta 89, a cikin suratu Ali-Imrana Aya ta 31 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce (da su) “ idan kun kasance kuna son Allah to ku bi ni,Allah ya so ku, ya kuma gafarta muku zunubanku.Allah kuwa Mai gafara ne Mai jin Kai) duk wanda yake son Allah,Allah zai so shi, kuma duk wanda Allah ya so shi zai kasance daga cikin amintattu).har ila yau masu saurare daga cikin girmar Albarkar dake tattare da sanin Ubangiji, tabbatuwar irfani na fitira , karfafa alakar Bawa da mahalicinsa tare da rusa duk wani hijabin samar da hasken imani ga Dan Adam,wannan shine abinda shugaban masu kadaita Allah Ali bn Abi talib (a.s) ya bayyana a cikin munajatinsa mai albarka na watan Sha’aban( Ya Ubangina ka bani cikekkiyar kamalar isa gareka, ka kuma haskaka basirar zukatanmu da hasken da zai sanya ta kai gareku, har sai duk wani hijabi da zai yi Katanga zuwa gareku ya rushe da kuma yadda zukatanmu za su kai ga taskar girmanku, ruhinmu kuma  ya zamanto ya hadu da buwayar tsarkinku..zuwa karshen Addu’ar) masu saurare, hakika sanin Allah shine hanyar wadatuwa da ‘yantuwa daga kankin wanin Allah da kuma kankin son duniya kamar yadda ya kasance babbar hanya ta kaiwa ga babban matsayin na bautar Allah wacce itace ibadar masoyya, har ila yau sirri ne na juriya da samun sabati a kan Addini da kuma samun damar ci gaba da dawwama da kuma irtibati da Allah madaukakin sarki.


***************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.