karamin Sani kukumi-Hakikanin sanin Allah
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayani kan mahimancin Sanin Allah madaukakin sarki a rayuwar Mutune da kuma samun sa’adarsa gami da tsira,tambayarmu ta Yau minene hakikanin sanin Allah ? shin tana yuyuwa Dan Adam ya san Ubangijinsa hakikanin Sani? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.
****************************Musuc*****************************
Masu saurare kamar yadda shirin ya saba yak an yi nazari da kuma bincike cikin nauyaya guda biyu Alkur’ani mai tsarki da kuma hadisan iyalan gidanan Ma’aikin Allah tsarkaka domin amsar tambayar, a cikin suratu An’ami Aya ta 91 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ba Su Kuma girmama Allah kamar yadda ya kamata ba, lokacin da suka ce (da Annabi game da sha’anin Alkur’ani) Allah bai saukar da wani Abu ba……) hakika maluman Tafsiri sun fasarra wannan Aya da cewa bas u sanshi ba hakikakin Sani cikin Rahama da kuma dabobbi bisa Bayi. Ya zo a cikin littafin Fikhu Ridha Imam (a.s) ya ce:( hakika farkon abinda Allah madaukakin sarki ya wajabtawa bayinsa shine saninsa da kuma kadaitashi wajen bauta, Allah madaukakin sarki ya ce:( Ba Su Kuma girmama Allah kamar yadda ya kamata ba,) ma’ana ba su san Allah hakikanin Sani ba) sannan Imam (a.s) ya ce daga ma’aifana su kuma daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce: sani shine bada gaskiya, meka yuwa, ikhlasi cikin sirri da kuma a bayyane, kuma hakikanin sanin Allah shine ka yi biyayya kada kuma ka yi sabo, kayi godiya kada kuma ka kafirce).a cikin Littafin Usulul Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanin shiriya Imam Muhamad Bakir da kuma Ja’afaru Sadik (amincin Allah ya tabbata a garesu) yayin da suke fasarar wannan Aya (Ba Su Kuma girmama Allah kamar yadda ya kamata ba,) sun bayyana cewa hakika ba a siffanta Allah madaukakin sarki da wani abu, ta yaya za a siffanta shi alhali a cikin Littafinsa mai tsarki ya ce (Ba Su Kuma girmama Allah kamar yadda ya kamata ba) ba a siffantashi da kaddara saidai ya kasance mafi girma da hakan). A cikin Littafin Attauhid, shek Saduk ya ruwaito wani hadisi mai tsaho inda a cikinsa Imam Ridha (a.s) yake amsa tambayar Ma’amun Abbasi, kuma ya zo a bangaren kissar Musa (a.s) mutanansa sun ce hakika idan ka roki Ubangijinka da ya baka damar ganinsa da ya amsa naka, kuma da ka kasance kana bamu labarin yadda yake kuma mu san shi hakikakanin Sani, sai Annabi Musa (a.s) ya ku Mutane Hakika ba a ganin Allah da idanu kuma a kotamtashi da ni, ana sanin Allah ne ta hanyar Ayoyinsa da kuma wakilansa, ma’ana(Annabawa da kuma shugabanin shiriya daga cikin iyalan gidansa tsarkaka)
Masu saurare abin fahimta a cikin wadannan hadisai masu albarka da suka gabata daya daga cikin ma’anar sanin Allah hakikanin Sani, shine saninsa ta hanyar abinda a waki’I kamar girma, kudura , rayuwa,Ililmi da saurensu kamar sifoffinsa masu albarka.kuma hakan ba zai iya tabbatuwa ga ko wani Dan Adam daga cikin halittu ba, kuma wannan matsayi babu wani mahluki da zai iya cimma wannan matsayi domin Allah madaukakin sarki ba shi da haddi, kuma Dan Adam ya nada Haddi, ba zai yi yuwa ga wanda yakeda haddi ya san wanda ba shi da haddi hakikanin sani.
*********************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,duk yadda mahluki zai yi tutuni kan girmar Ubangiji, to girmansa ya fice haka, kuma wannan , ma’anar Kalamar Allahu Akbar wacce it ace shi’arin Tauhidin musulinci kuma a kan hakan ne yak an kasancewar ma’anar hakikanin Sanin Allah, hadisai da dama sun bayyana cewa babu wani mahluki da zai san Allah hakikanin Sani, a cikin Littafin Awalil-Ali na ibn Abi Jamhurul-Ihsani an ruwaito hadisi daga Annabi mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Da kun San Allah hakikanin Sani Da Duwatsu masu girma sun gushe saboda Addu’arku, babu wani da zai iya cimma hakikanin saninsa, sai aka ce da shi har kai ya Ma’aikin Allah, sai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce har da ni Allah madaukakin sarki ya fi karfin an son karshen sa ko kuma karshen saninsa) Ibn Abi Jamhur ya yi Ta’aliki a kan wannan hadisi,ya ce domin haka ne ma’aikin Allah (s.a.w) cikin Addu’arsa yake cewa (Ya wanda bai san waye shi idan ba shi ba) kuma ya ce:(tsarki ya tabbata a gareka ba mu sanka ba hakikanin saninka ba), masu saurare idan muka yi nazari dangane da ma’anar hadisin da ya gabata za mu fahimci cewa waliyan Allah sune suka san Allah a matakin farko ba wancan sanin ba da Ma’aikin Allah madaukakin sarki ya bayyana cewa ko shi kansa bai san Allah karshen sani ba domin abinda dake da hadi ba zai taba sanin abinda bas hi da haddi hakikanin Sani ba,kuma wannan shine ma’anar fadar ma’aikin Allah (s.a.w): (da kun san Allah hakikanin saninsa da kun yi tafiya a bisa rusa kuma da duwatsu sun gushe saboda Addu’arku) ba shakka wannan sani shine irin sanin da Annabawa, Ma’aika, da waliyan Allah madaukakin sarki suka sani, ba kuma wancan karshen sanin ba. Hakika kuma an ruwaito hadisai da dama wadanda suke ta’akidin cewa mumunai za su cimma ilimin sanin Allah na gaskiya wanda babu tashbihi da kuma daidaita Allah ga hallitu a cikinsa, kuma wannan shine za mu kawo muku a shirinmu na gaba da yardar Allah, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon amfani da abinda muka saurara.
***************************Musuc*****************************
Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.