May 23, 2017 05:03 UTC

shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirin da ya gabata mun yi bayyana kan abinda ya wajabta a kan mu dangane da Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na farko shi ne yi masa da'a da biyayya, tambayarmu ta Yau mine ne ya wajabta kanmu na biyu dangane da Ma'aiki (s.a.w.a)?, Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

************************Musuc*****************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, Hakika a cikin Nassosin da suka gabata mun fahimci cewa daga mahiman batutuwan da suka wajabta kanmu dangane da Masoyin Allah Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka bayan yi masa da biyayya sai kuma wajibcin komawa gare shi a dukkanin al'amuran da aka samu sabani a cikin sa, mai yiyuwa babu wata Aya da ta bayyani kan wannan Hukunci kamar wadannan Ayoyi na cikin Suratu Nuri, inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Hakika Mun saukar da Ayoyi masu bayyana komai da komai. Allah kuwa Yana shiryar da wanda ya so ne zuwa tafarki madaidaici*kuma suna cewa:"Mun ba da gaskiya da Allah da kuma Manzo kuma mun bi, sannan wata kungiyar daga cikinsu takan ba da baya bayan wancan (Imani).wadannan kuwa ba muminai ba ne*idan kuwa aka yi kiran su zuwa gag a Allah da Manzonsa dan ya yi hukunci a tsakanin su sai ka ga wata kungiya daga cikinsu tana bijerewa*Idan kuwa suna da wani hakki (da suke nema) sai su zo wurinsa suna masu kaskantar da Kai*Shin raunin imani ne a cikin zukatansu ko kuwa suna tababa ne, ko kuma suna tsoro ne kada Allah da manzonsa su zalunce su ne?A'a wadannan su ne Azzalimai*Muminai bas u da wata Magana idan aka kira su zuwa ga Allah da Manzonsa don ya yi hakunci a tsakaninsu sai fadar"Mun ji kuma mun bi"Wadannan kuwa su ne masu babban rabo*Duk kuwa wanda ya bi Allah da Manzonsa kuma yake tsoron Allah kuma yake kiyaye dokokinsa, to Wadannan su ne masu rabauta) Suratu Nuri daga Aya ta 46 zuwa Aya ta 52, Masu saurare, abin fahimta a wadannan Ayoyi masu albarka da suka gabata shi ne gaskiyar da'a da biyayya ga Allah madaukakin sarki da kuma Ma'aikinsa (s.a.w.a) tana bayyana ne ta hanyar amfani da dokokin da shi Ma'aiki ya zo da shi domin shi baya wata fama da son ransa Allah madaukakin sarki y ace:(Allah yana rantsuwa da tauraro yayin da ya fadi*Mutuminku bai bata ba kuma bai kauce hanya ba*Kuma ba ya yin Magana bisa son rai*Ba wani abu ba ne shi face wahayi da ake yuwo(masa)*Mai tsananin karfi ne ya sanar da shi*Ma'abocin karfi na boye sannan ya daidaita (a halittar da Allah ya yi masa) domin haka Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka shi ne sahibin Isma Mutlaka wato shi ne keda kariya daga wajen Allah wacce za ta kiyaye shi aikata duk wani sabo, kuma wannan isma ta kumshi dukkanin tausayi da ta kasance tsarkakkekiya daga duk wani son rai, domin haka shi Ma'aikin Allah ya fi kowa dacewa wajen daukan hukunci ga Al'ummar da kuma  warware duk wani sabani a tsakanin su.kuma wajibi ne ga wani musulmi ya koma gare shi game da duk wani sabani kuma ya yarda da hukunsa, ko da kuwa ya sabawa abinda yake tunani.domin ya kamata ga wani Mumuni ya bi hukuncin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) domin hukunci tsarkakekke ne daga ko wani irin zalinci, babu wani tsoro a cikin sa.da wannan za mu fahimci cewa bayyanan Ayoyin da suka gabata juyawa hukunci Annabi (s.a.w.a) baya zalinci ne kuma alama ce ta rashin gaskanta Imani bayan ga hakan, wannan zai zamanto musababi na fadawar Mutum cikin bata da azaba mai radadi, a bangare guda kuma komawa gareshi (s.a.w.a) a dukkanin al'amura alama ce ta gaskiyar Imani, yarda da hukuncinshi kuma tare da yi masa da'a da biyayya sanadi ne na rabauta gami da rabo mai girma.

***************************Musuc******************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kada a sha'afa shirin na zo muku kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, Hakika masu saurare bayyanin da muka yi a baya , gaskiya ce da Ayoyin Alkur'ani mai tsarki suke bayyani kansa, kamar yadda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Bai kamata ga wani mumini ko wata mumina ba, idan Allah da Manzonsa suka yi hukunci a kan wani al'amari  su zama suna da wani zabi game da al'amarinsu.wanda kuwa ya saba wa Allah da Manzonsa, to hakika ya bata, bayyanannen bata) suratu Ahazabi Aya ta 36, Hakika Hukunci Ma'aikin Allah (s.a.w.a) Hukuncin Allah madaukakin sarki ne, saboda haka ya wajaba aiki da shi cikin ko wani irin sabani a matsayi tabbaci na aiki da Umarnin Allah, Allah madaukakin sarki ya ce:(Yak u wadanda kuka ba da gaskiya, ku bi Allah ku kuma bi Manzo,da kuma majibinta alamuranku(wato shugabanin Addini).Sannan idan kuka yi sabani game da wani abu,to sai ku mai da shi zuwa ga Allah (watau Alkurani) da Manzonsa (lokacin da yake raye ko kuma sunarsa bayan fakuwarsa),idan kun kasance kun ba da gaskiya da Allah da ranar Lahira.(Yin) wancan (shi ya fi) alheri ya kuma fi kyakkyawar makoma) Suratu Nisa'I Aya ta 59.hakika masu saurare wannan Aya mai albarka na tabbatar da cewa a wajen Ma'aikin Allah (s.a.w.a) za a samu kyakkyawan tawuli da kuma fassarar maganar Allah tabaraka wa ta'ala, alamar gaskiyar imani kuma shi ne komawa gare shi domin fahimtar hakikanin fadar Allah, kamar yadda wannan Aya take ishara, Allah tabaraka wa ta'ala y ace:(Na rantse da girman Ubangijinka ba za su bada gaskiya ba har sai (lokacin da) suka sanya ka mai hukunci game da abin da ya faru a tsakaninsu, sannan kuma ba za su samu wata tababa ba a zukatansu game da abin da ka hukunta, su kuma mika wuya gaba daya) suratu Nisa'I Aya ta 65.a nan kuma tambayar da za ta bijiro ta yaya wannan wajibci zai tabbata (sanya ma'aikin Allah mai hukunci a tsakanin mu ) bayan fakuwarsa? Amsar kuma shi ne da farko Ayar da ta gabata ta wajabta mana yin da'a ga majinta Al'amuran Musulmai wato Shugabaninsu na addini kamar yadda Aya ta 59 cikin Suratu Nisa'I ta bayyana, wannan Aya ta sanya yin da'a da biyayya ga majibinta alamura a matsayin Da'a ga Ma'aikin Allah kuma dangane da hakan akwai Ishara na Ismarsu wato karkuwa daga sabon Allah kamar na Ma'aikin domin Allah yayi umarni da a yi musu da'a kamar yadda ya yi umarni a yiwa Ma'aikin Allah(s.a.w.a) da wannan hujja, hukuncinsu kamar hukuncin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) kuma su ma Shugabanin Addini 12 na iyalan gidan Anabta sun nisantu daga duk wata fada ta son rai, domin haka Aya ta 59 cikin Suratu Nisa'I ta yi ishara ga komawa a gare su domin hukuncin su hukuncin Ma'aikin Allah ne kuma Hukuncin Ma'aikin Allah hukuncin Allah ne,har ila yau cikin Suratu Nisa'I Allah madaukakin sarki ya ce:(Idan kuma wani labari ya zo musu na aminci (cin nasara) ko na tsoro (rashin nasara), sai su watsa shi,(don su raunana zukatan Muminai) da dai za su komar da shi(watsa labaran) zuwa ga masu hankali daga cikin su, lallai da wadanda suka tace shi(labarin) daga cikinsu sun gane shi (labaran da ya kamata su watsa) Da ba don falalar Allah ba a gareku da kuma rahamarsa, da ba shakka kun bi shaidan (kana bin da yake kawata muku na miyagun abubuwa) in ban da 'yan kadan daga cikinku) Suratu Nisa'I Aya ta 83.Hakika Masu saurare falalar Allah da Rahamarsa ya sanya komawa wajen Ma'aikin Allah a Hukunci na sabani ,kuma wannan Al'amari ne mai yiyuwa har zuwa ranar Alkiyama ta hanyar komawa zuwa ga majibinta Al'amura wato shugabanin Addini na iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka kamar yadda ya tabbata a cikin Alkur'ani mai tsarki da kuma Hadisai masu inganci.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.