Mar 06, 2016 19:44 UTC
  • karamin Sani kukumi-Wadanda Za Su Cimma Sanin Allah

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani dangane da sanin Allah madaukakin sarki hakikanin Sani,shirin na yau kuma zai yi bayyani kan wasu hadisai da suka yi bayyanin cewa mumunai suna iya cimma wannan sani na gaskiya daidai imaninsu kamar yadda muka muku alkawari a shirin da ya gabata, amma kafin mu shiga shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.


****************************Musuc*********************************


Masu saurare kamar yadda muka bayyana a shirin da ya gabata hadisai da dama sun yi bayyani dangane da sanin Allah madaukakin sarki daidai gwalgwadon imanin mumuni, a cikin Littafin Kifayatul Asari fil A’imatul Isna Ashara, shek Hafiz Khazaz AlQummi ya ruwaito hadaisi daga Hisham bn Salim ya ce:na kasance wajen Imam Sadik Ja’afar bn Muhamad (a.s) sai Mu’awiya bn Wahab da Abdulmalik bn A’ayun suka shigo, Mu’awiya bn Wahab yace wa Imam (a.s) Ya Dan Ma’aikin Allah mi za kace dangane da labarin da aka ruwaito na cewa Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ga Ubangijinsa, bisa wata kama ya ganshi, kuma mi za kace dangane da hadisin dake cewa mumunai za su ga Ubangijinsu a cikin Aljanna, a wata kama za su ganshi? Sai Imam Sadik(a.s) yay i mulmushi sannan ya ce Ya Mu’ayuwa! Babu babban abinda ya fi muni ga mutuman da zai rayu shekaru 70 ko kuma 80 a kalkashin milkin Allah yana ci daga ni’imarsa sannan kuma bai san Allah hakikanin sani ba, Ya Mu’awiya! Hakika Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka bai ga Ubangiji Tabaraka wa ta’ala da idanuwansa ba, domin Gani kashi biyu ne, a kwai ganin zuci da kuma gani da idanu, duk wanda ya ce Ma’aikin Allah ya ga Ubangiji da ganin Zuci to yayi gaskiya, amma duk wanda ya gansa da idanuwansa hakika ya kafircewa Allah da Ayoyinsa domin Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce: (duk wanda ya kwatamta Allah da halittunsa hakika ya kafirce), masu saurare sai Imam Sadik (a.s) ya ci gaba da bayyani a kan sanin Allah madaukakin sarki kamar yadda mai tambaya ya tambaya ta dangane da yuyuwar ganin Allah da idanu , Imam(a.s) ya bayyana cewa hakika Allah mai girma ne daga idanuwa su ganshi, a karshen Hadisin Imam kuma ya ce hakika babana ya fada mani shima daga babansa Husain bn Ali (amincin Allah ya tabbata a garesu) ya ce an tambayi shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya Dan uwan Ma’aikin Allah shin ka ga Ubangijinka?sai Imam Ali(a.s) ya ce: ta yaya zan bautawa Ubangijin da ban gani ba,hakika idanuwa  ba su ganshi ba, amma kuma zukata sun ganshi da tabbacin Imani, sannan sai Imam Sadik (a.s) ya ce: duk wanda ake ganinsa da idanuwa makhluki ne  kuma ko wani mahkluki yanada mahalarci, duk wanda ya ce ana ganin Allah da idanu hakika ya  siffanta shi  da bayinsa, kuma duk wanda ya kwatamtashi da wani makhluki hakika ya riki kishiya ga Allah, kaicensu ba su ji fadar Allah madaukakin sarki ba (Gani ba ya risker Sa, shi kuma yana riskar maganai,kuma shine mai tausasawa Masani) suratu An’am Aya ta 103da kuma kaulinsa(Ba za ka gan Ni ba, amma duba zuwa (wannan) dutsen saboda haka idan ya tabbata a gurinsa to da sannu z aka gan Ni” to, lokacin da Ubangijnsa ya yi tajalli ga dutsen (sai) ya mayar da shi rugu-rugu,Musa kuma ya fadi a sume, sannan lokacin da ya farko (sai) ya ce Tsarki ya tabbatar Maka, na tubar Maka, kuma ni ne farkon mumuni) suratu A’arafi Aya ta 143.  


*****************************Musuc***************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, har ila yau za mu ci gaba da wannan hadisi mai Albarka na Imam  Sadik (a.s) a bayyannin da yake na hakikanin sanin Allah a cikin mahangar Alkur’ani mai tsarki da yake bayyani kan hikayar Annabi Musa Kalimullah (a.s) sai ya ce: kuma hakika hasken Allah madaukakin sarki ya bayyana a kan dutsi kamar hasken da ya fito daga cikin kofar Allura sai kasa ta gilgiza sannan dutsin ya rugurguje, Annabi Musa (a.s) kuma ya fadi sume, bayan Allah ya dawo masa da ruhunsa sai ya ce tsarki ya tabbata a gareshi na tuba gareka,daga fadar duk wani da ake tunanin ana ganinka, na dawo ga sani Na da kai,  hakika idanuwa ba za su iya riskarka ba, kuma ni ne farkon mumuni kuma farkon wanda ya tabbatar da cewa kai kana gani kuma kai ba a ganin ka, kuma hakika matsayinka nada girma


A karshen Imam Sadik (a.s) ya rufe hadisin da cewa: Hakika fiyeyyen farilai da kuwa wadanda suka fi zama wajibi a kan Mutune, sanin Allah da kuma tabbatuwa a kan bautarsa, kadaituwar sanin sa da cewa babu wani abin bbauta bayansa,ba aka kwatamta shi da komai,kuma an san cewa shi ne ya samar da samuwa  tun asalin wujudi,wanda kuma ba’a sifanta shi ko kuma kwatamta shi da wani Abu, shi mai ji ne kuma mai gani.


Masu saurare , abin fahimta a cikin wannan hadisi mai albarka shine sanin Allah  wanda ya dace da girmanse da kuma kudurarsa ba tare da kwatamta shi a halittu ba wajibi ne a shari’ar musulinci kuma wannan sani shine ingantattan Sani da Addini ya amince da shi kuma ya bukaci ko wani musulmi ko mumuni da ya neme shi, bayan haka, ta yaya ne mumuni zai iya cimma wannan sani?amsar wannan tambaya zai a biyo mu bashi zuwa Maku mai zuwa da yardar Allah.


***************************Musuc*****************************


Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman mai Injiniyamu Aminu Ibrahin Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamallahi ta’ala wa barkatuhu.