karamin Sani kukumi-A wajen Wa Ya kamata Mu Dauki Ilimi
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake saduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayani kan mahimancin ilimin Sanin Allah madaukakin sarki, tambayarmu ta yau kuwa, itace daga wajen su wa ya kamata mu samu wannan ilimi, kuma ta yaya za mu tabbatar da ilimin da muka samu gaskiya ne? kafin amsa tambaya ga wannan
************************Musuc*******************************
Masu saurare a shirin da ya gabata, mun yi bayyani cewa Dan Adam na iya sanin Allah madaukakin ta hanyar girmansa, Ayoyi da kuma siffofinsa wadanda suka nisanta da siffantashi da halittu kuma takaita girman milkinsa madaukakin sarki, hadisai da dama sun bayyana cewa sanin Allah mataki-mataki ne ya danganta da imanin Bawa, duk lokacin da Imani,tsoron Allah da kuma takawar Bawa suka karu sai ya rabauta da martaba mai girma na sanin Allah madaukakin sarki, wannan shine abinda muka bayyana a shirye-shiryenmu da suka gabata na batun ilhami ko kuma ilmun Ladunni, kuma hadisai da dama sun tabbatar da cewa babbar martaba na sanin Allah hakikanin sani, Allah madaukakin sarki ya kataitashi ga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma iyalan gidansa tsarkaka, ya zo a cikin wani sahihin Hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) yace wa Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s): (Ya Ali Babu wanda ya san Allah hakikin sani baya na da kuma bayanka), har ila yau a cikin wani sahihin hadisin na daban da aka ruwaito cikin Littafin Masharikul Anwar, Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce: (Ya Ali babu wanda ya sanka face Allah madaukin sarki da ni ba, kuma babu wanda ya san Ni face Allah madaukakin sarki da Kai ba, kuma babu wanda ya san Allah face Ni da Kai ba)
Masu saurare da wannan hadisi za mu fahimce cewa cimma ilimin sanin Allah ko kuma inda ya kamata mu san Allah madaukakin sarki hakikanin sani shine ta hanyar iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka, hadisan su, bayyanansu, da kuma yadda suka fassara Alkur’ani mai tsarki, ta hakan ne kawai za su fahimci Allah da kuma hakikanin girma da kuma matsayinsa madaukakin sarki, yazo a cikin Ziyaratu Jami’a (amincin Allah bisa masana Allah,Alkukin hasken Allah,kidajen Albarkar Allah,ma’ajiyar hikmar Allah, taskar ilimin Allah, wadanda suka kiyaye sirrin Allah, kuma wadanda suke dauke da Littafin Allah da kuma wasiyan Annabin Allah, Zuriyar Ma’aikin Allah amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, rahamar Allah da kuma Albarkarsa) har ila yau wasu hadisai na daban sun bayyana cewa,gaskiya da kuma tabbatar da wilayar Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma na iyalan gidansa tsarkaka shine tabbacin rabauta da sanin Allah madaukakin sarki hakikanin Sani, a cikin Littafin Alfutuh,ibn A’asam Alkufi ya ruwaito wani hadisi daga shugaban muwahidai Aliyu bn Abi Talib (a.s) y ace:(hakika Allah madaukakin sarki ya nada taskoki da ba na zinari ko kuma azurfa ba ne, sai dai mutane mumunai wadanda suka san Allah hakikanin sani kuma sune mataimakan Mahadi a karshen zamani)
************************Musuc*********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, a cikin Littafin Tuhuful Ukul an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s)ya ce:(hakika masoyanmu na boye da na bayyane sunada Alamomi da ake ganesu da shi, da farko sun son ilimin kadaita Allah hakikanin Sani, kuma sun karanci hukunce-hukuncen sa, kuma sun yi imani da abinda suka sani na tauhidi, da kuma sifoffinsa kyawawa, sannan sun san iyakar Imani, gaskiyarsa da kuma sharudansa), a cikin littafin Tuhuful Ukul an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika masoyanmu na boye da na bayyane sunada alamomi da ake ganesu da shi, na farko ana sun fahimci tauhidi ko kuma ilimin kadaita Allah hakikanin Sani, kuma suna aiki da ilimin tauhidin kuma sun yi imani da abinda suka sani ta tauhidi da sifoffin Allah madaukakin sarki, sannan kuma sun san iyakar imani, gaskiyarsa da kuma sharudansa) har ila yau a cikin wani dogon hadisi daga ruwaito cikin Littafin Kifayatul Asar, an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika Malumai sun gaji ilimi ta hanyar nema, su kuma masu gaskiya sun gaji gaskiya ta hanyar kaskantar da kai,da yawan ibada, duk wanda ya dauki wannan hanya wato ta yawan ibada ko ya fadi warwas ko kuma ya daukaka, mafi yawan wadanda suke faduwa ba sa kuma daukaka idan ba su kiyaye hakkin Allah ta’ala ba, kuma ba su yi aiki da umarninsa ba, wannan shine siffar ita ce wanda bai san Allah hakikanin sani ba to ta yaya zai soshi, domin haka, kada sallar su, azuminsu,iliminsu da kuma bayyansu su yaudareku).sannan Imam Sadik (a.s) ya ci gaba da cewa Rawin Ya Yunus idan kana bukatar sahihin Ilimi to a wajenmu Ahlulbait, hakika mune muka kaje ji kuma an bamu hikima da kyawawen bayanai…Allah ya zabemu kuma ya tsarkakemu sannan ya bamu abinda bai baiwa wani daga cikin talikai ba)
Masu saurare, amsar tambayar da muka fahimta a wadannan nasossi masu albarka, ita ce , cimma sanin Allah hakikanin sani yana tabbatuwa ne ta hanyar iyalan gidan Annabta, Ahlulbait (amincin Allah su tabbata a garesu) da fatan masu saurare, Allah bamu ikon aiki da abinda muka saurara.
***********************Musuc**********************************
Masu saurare a nan za mu dasa Aya saboda lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala , ni da na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.