karamin Sani kukumi-Sanin Allah Ta Hanyar Ilimin Ilhami
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi, shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah da kuma Sunar Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, shirin na yau zai yi bayyani kan hanyoyin sanin Allah madaukakin sarki, domin nasossi da dama sun bayyana mana hanyoyi da dama, daga cikin a kwai hanyar dabi’ar Dan Adam wato dabi’ar da Allah madaukakin sarki ya halicce shi, ko kuma na ta hanyar ilhami ,tambayar ta yau ita ce ta yaya za mu san Allah ta hanyar ilhami? Kafin amsa wannan tambaya ba ri saurari abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.
********************Musuc**************************
Masu saurare kamar yadda shirin ya saba, za mu fara da Littafin Allah mai tsarki, a cikin suratu Rumu Aya ta 30 Allah madaukakin sarki ya ce:(sannan kuma ka tsayar da fuskarka ga Addini madaidaici(wanda shi ne )dabi’ar da Allah ya halicci mutane a kai,wannan shi ne Addini mikakke, sai dai kuma yawaicin Mutane ba su san (haka) ba.) a cikin Littafin Almahasin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yayin da yake fasarra wannan Aya ya ce ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce ko wani yaro ana aifuwarsa bisa dabi’ar sanin mahaliccinsa kuma shine fadar Allah madaukakin sarki (wallahi da za a tambaye su wanda ya halicci sammai da kassai,lallai za su ce Allah ne )Zuraratu bn A’ayun ya tambayi Imam Bakir (a.s) kan ma’anar wannan Aya sai Imam (a.s) ya ce masa an halicce su a kan sanin cewa hakika Allah shi ne ubangijinsu, in ba dan haka ba, da ba su san amsar da za su bayar ba a lokacin da aka tambayesu da ubangijinsu da kuma wanda yake arzutar da su).a cikin littafin Kafi an ruwaito wani hadisi daga Zuraratu bn A’ayun yayin da ya tambayi shugabanmu Imam Bakir (a.s) dangane da fadar Allah madaukakin sarki (kuna masu mika yuwa ga Allah, ba masu tarayya da shi ba)suratu hajji Aya ta 31sai Imam (a.s) ya ce mika yuwa shine dabi’ar da Allah ya halicci mutane a kansa babu wani canji ga halittar Allah, ya halicesu bisa saninsa) har ila yau a cikin Littafin Attauhid na shekh Saduk an ruwaito hadisi daga Imam Bakir (a.s) yayin da yake fasara wannan Aya ya ce(an haliicce su bisa Tauhidi, bisar alkawari a kan sanin cewa lalle shine Ubangijinsu, in ba dan haka ba, da ba su san amsar da za su bayar ba a lokacin da aka tambayesu da ubangijinsu da kuma wanda yake arzutar da su), masu saurare, abin fahimta a cikin wadannan nasossi masu albarka, sanin Allah madaukakin sarki a matsayin wanda ya halicci dan Adam mai arzutawa, abin bauta, abu ne da Allah madaukakin sarki ya halicci ko wani mutune da shi,hakika Allah madaukakin sarki tun asalin halitta ya sanya wa ko wani mutune saninsa da kuma cewa Allah madaukakin sarki ne kawai abin bautarsa , kuma ko wani Dan Adam ya dauki alkawarin rike Allah madaukakin sarki a matsayin abin bautar sa tun farkon halittarsa kuma wannan shine abinda Alkur’ani mai tsarki yayi ishara a cikin suratu A’arafi Aya ta 172 Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma (ka tuna) lokacin da Ubangijinka ya fiddo zuriyar ‘yan adam daga tsatsonsu, ya kuma sa su suka yi wa kansu shaida, (ya ce da su) “Yanzu ba Ni ne Ubagijinku ba? “suka ce Ba Ja kai ne Ubangijinmu mun shaida (mun yi haka ne) don kada ku ce a ranar Alkiyama, ‘hakika mu ba da masaniya a wannan), a cikin Tafsiru Ayyashi an ruwaito hadisi daga shugabanmu imam Bakir (a.s) ya ce:(Allah yana fitar da Ziriyar Annabi Adam (a.s) daga tsatsonsa har zuwa ranar Alkiyama, suna fita kamar kwayar zarra, a lokacin ne yake sanar da su kansa , ba don haka ba, da babu wani mutune da zai san ubangijinsa ba) har ila yau a wata riwayar Imam (a.s) ya bayyana cewa (hakika sani ya tabbatu tun lokacin da aka halicce su, sai suka mance lokacin kuma za su tuna shi, ba don haka kuma ba, da babu wani mutune da zai san mahilicinsa da kuma mai arzuta shi ba)
********************************Musuc**************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,daga mahiman batutuwan da suke sanya bayyanar wannan sani da aka halicci ko wani Dan Adam da shi,mantuwa da dabi’ar dan adam idan ya samu wani abu sai ya shagaltu ya manta da manufar da ta sanya aka haliccesa, a cikin littafin Biharul Anwar an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Hasan Askari (a.s) ya ce:(Allah shine wanda ko wani mahluki yake komawa gareshi a yayin bukata da tsanani da kuma lokacin da duk fata ya yanke daga waninsa ,da kuma lokaci wasu dadilai suka kare daga wajen waninsa) ma’ana shine a yayin da bawa ya shiga cikin wani tsanani yana bukatar taimako, da farko zai fara nema ne daga halittu, amma lokacin da ya nema bai samu ba ya bi hanyoyi da dama, ya bi ta kan wane-wane bai samu ba duk fata da yake da shi a wajen halittun Allah ya kare, sai ya koma ga Allah, a wannan lokacin ne zai tuna da Allah madaukakin sarki, amma da farko, da ya dogara da Allah ya meka bukatarsa wajen mahilicinsa da bai zubar da mutuncin shi ba a gaban mutane.a cikin litafin Rabi’ul Abrar da tafsirul burhan, an ruwaito hadisi daga Imam sadik (a.s) yayin da yake ishara kan sanin Allah madaukakin sarki, wani mutune ya je wajensa ya ce Ya Dan Ma’aikin Allah ka shiryar da ni sanin Allah, mafi yawa daga cikin masu jayayya sun kasa gamsar da ni , fada mini wanene Allah, amma kada ka fara ambato mini duniya ko nuni da abu abu kace ta haka ne za ka sanar da ni Allah, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa Ya kai Bawan Allah shin ka taba hawan jirgin ruwa ?sai Mutuman ya ce Na’am, imam ya ce masa shin wata iska mai tsanani ta taba samun ka kana cikin jirgin ruwan kuma jirgin ruwan ya kare-raye, yayin da babu damar jirgin ruwan nan ya ceceka kuma iyo bai zai wadatar da kai ba daga nutsewa? Sai wannan mutune ya ce Na’am, sai imam (a.s) ya ce a wannan lokaci za kaji wani fata a cikin zuciyarka da kake tunanin ya nada iko ko kuma zai iya kubutar da kai daga hallaka ? sai wannan mutune ya ce eh ya Dan Ma’aikin Allah sai Imam (a.s) ya ce wannan fata da kak da shin a cewa a kwai wani wani da zai iya cetonka kuma ya nada ikon yin hakan shine Allah madaukakin sarki domin Allah shi ne mai ikon kubutarwa a lokacin da babu mai kubutarwa, mai taimako a lokacin da bawa ya rasa mai taimakonsa sannan sai Imam (a.s) ya karanto wannan Aya mai albarka (idan kuma tsoro ya same ku a cikin kogi sai duk wadanda kuke kira su bace (muku) sais hi kawai,)suratu Isra’I Aya ta 67 har ila yau Imam ya karanto wannan Aya mai albarka(sannan kuma idan cuta ta same ku to wurinsa kuke kai kuka) suratu Nahali Aya ta 53.masu saurare, abin fahimta a takaice cikin shirin na yau, shine sanin Allah madaukakin sarki ta hanyar fitra ko kuma kamar yadda aka halicemu yana tabbatuwa yayin da duk wani dalili ko wani fata ya gushe , a wannan lokacin ne bawa zai koma ga zuciyarsa ta tabbatar masa da cewa babu wani abu da zai iya arzutawa ko kuma hanawa, kubutarwa ko kuma tseratarwa face mahalici, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu iko da amfana da abinda muka saurara.
***********************Musuc**********************************
Masu saurare a nan za mu dasa Aya saboda lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shiri idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala , ni da na gabatar nike muku fatan Alheri, wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.