Hakin da Ya Wajaba Kan Mu Ga Ma'aiki(s.a.w.a) (3)
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirye-shiryen da suka gabata mun yi bayani kan abinda ya wajaba a kanmu dangane da Ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarka, inda a shirin farko muka bayyana cewa a kwai hakin da'a da biyayya a gare shi, a kuma shiri na biyu muka bayyana cewa hakin ruji'I da komawa a gare shi a wuraren sabani domin sanin hukuncin Allah wanda ya nisanta da na son rai, tambayarmu ta Yau mine ne hakki na uku a gare mu dangane da Ma'aikin Allah(s.a.w.a) a gare mu? Kafin amsa wannan tambaya sai a dakace mu da wannan.
*************************Musuc**************************
Masu saurare, Hakika cikin Nassosi da dama kama daga Ayoyin Alkur'ani mai girma gami da ingantantun Hadisai za mu samu cewa daya daga cikin hakkokin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka a kan bil-adama har zuwa ranar Alkiyama shi ne hakin Mawadda ko soyayya a gare shi da kuma kiyayya ga makiyansa gami da kaurace musu. Hakan kuma shi ne hakikanin Imani, domin Soyayyar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ita ce mafi fifikon soyayya a wajen Allah da hakan ya kasance sharadi na Imani kamar yadda aka ruwaito cikin tafsirin Safi daga Ma'aiki (s.a.w.a) ya ce:(dayanku ba zai samu dandanon Imani ba har sai ya so don Allah kuma ya ki saboda Allah), baya ga wannan, Ayoyin Alkur'ani sun shiryar da mu zuwa ga wannan Hakki daga cikin Hakkokin Ma'aikin Allah a kanmu, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce(da su):"Idan iyayenku da 'ya'yanku da 'yan uwanku da matayenku da danginku da dukiyoyin da kuke tara da kasuwancin da kuke tsoron gurguncewarsa da kuma gidajen da suke kayatar da ku, idan har su suka fi soyuwa a gare ku fiye da Allah da Manzonsa, da kuma jihadi saboda Shi, to sai ku saurara har sai Allah ya zo da al'amarinsa. Allah kuwa ba ya shiryar da Mutane fasikai) suratu Tauba Aya ta 24.Hakika Masu Saurare wannan Aya mai albarka tana bayyani ne a kan cewa Soyayyar Allah da Ma'aikinsa ya wajaba ta kasance sama da ko wata sayayya, ta ma'aifa ce ko 'ya'ya, ko zuriya matukar dai suka gyara aiyukansu ba su ki Allah da Ma'aiki ba, amma idan sun ki Allah Allah da Ma'aiki, to ya haramta ma a yi mu'amala da su cikin tausayi da soyayya kamar yadda wannan Aya ke cewa:(Ba zaka sami mutanen da suka bada gaskiya da Allah da Ranar lahira ba suna kaunar wadanda suke gaba da Allah (suke kangarewa) da manzonsa,ko da kuwa sun kasance iyayensu ne ko 'ya'yansu ko 'yan uwansu ko kuma danginsu.Wadancan Ya rubuta imani (tabbatarwar imani) a cikin Zukatansu Ya kuma karfafa su da haske daga gare Shi,zai kuma shigar da su aljannoni (wadanda) koramu suke gudana ta karkashinsu madawwama a cikinsu,Allah ya yarda da su,su ma sun yarda da shi,Wadancan ne rundunar Allah, Na'am Hakika rundunar Allah su ne marabauta)suratu Mujadalati Aya ta 22.a bangaren Hadisai da suke bayyani dangane da wannan maudi'I su nada yawan gaske, daga cikin su wanda Shekh Saduk ya ruwaito a cikin Littafin sa na Ilalu Shara'I'I , Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Imanin Bawa ba zai cika ba har sai na kasance mafi so a gare shi da shi kansa, kuma iyalan gida Na suka kasance mafi so a gare shi da iyalan sa) Masu saurare irin wannan hadisi ya zo cikin bangaren Ahlul-sunna, haka zalika an ruwaito wani hadisi na daban a cikin Littafin Ilalu Shara'I' daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na cewa:(ku so Allah kan abinda yake ciyar da ku daga Ni'imarsa kuma ku so ni saboda Allah madaukakin sarki, ku so kuma iyalan gida Na saboda Ni).
**************************MUsuc******************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai fara da Hadisin Anas bn Malik ya ce:(Wani Mutum daga cikin Mutanen kauye ya zo wajen Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce masa yaushe ne tashin Alkiyama? Anas ya ce kafin ma'aikin Allah ya amsa masa sai lokacin Salla ya yi, sai ma'aikin Allah (s.a.w.a) yayi sallar Sa, bayan an kamala sallar sai ya ce Ina Mai tambaya a kan tashin Alkiyama, Sai Mutuman ya ce Ni ne Ya Ma'aikin Allah, sai Manzo ya ce masa da mi ka shirya mata? Sai Mutuman ya ce Wallahi ban shirya mata da aiki mai yawa kamar Salla da Azumi ba, Saidai Ni ina Son Allah da Ma'aikin sa, sai Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce: Mutum yana tare da abinda yake So.Anas ya ce: ban taba ga wata rana da Musulmi suka yi farin ciki bayan bayyanar musulinci a kan wani abu kamar yadda suka yi a wannan Lokaci ba) a wani hadisi na daban kuma da Shekh Tusy ya nakalto cikin Littafinsa Amaly daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Wani Mutum daga cikin Ansar ya zo wajen Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce: Ya Ma'aikin Allah ba na iya rabuka da kai, duk lokacin na shiga gidana, idan na tunaka, sai in bar gidan in tunkari inda kake har inganka,saboda soyayyar da nake yi maka, sai na tuna cewa idan ranar Alkiyama ta kasance ka shiga Aljanna, cikin matsayi na A'alal Iliyina yaya zan kasance Ya Annabin Allah?Imam Ali (a.s) ya ce: sai wannan Aya ta sauka, Allah madaukakin sarki ya ce:(Duk wadanda kuwa suka bi Allah da Manzo to wadancan suna tare da wadanda Allah Ya yi ni'ima a gare su, irin su annabawa da siddikai da shahidai da salihai.Madalla kuwa da wadancan kyawawen abokai) suratu Nisa'I Aya ta 69, sai Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya kira wannan Mutum sannan ya karanta masa wannan Aya tare kuma da yi masa albishir).Masu saurare, Hadisan da suka gabata sun bayyana mana cewa Hakika Soyayyar da Mutum ya kamata ya yiwa Annabin Rahama (s.a.w.a) ba za ta fi fifiko da wacce zai yiwa iyalan gidansa tsarkaka ba, Hakika Allah madaukakin sarki ya umarci Annabinsa da ya bukaci soyayyar iyalan gidansa a matsayin Ladansa kan abinda ya fuskanta na wahalhalu wajen isar da sakon Allah da kuma shiryar da Al'umma wanda wani annabi bai fuskanta ba a gabaninsa, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(……Wadanda kuwa suka bada gaskiya suka kuma yi aiki nagari, to suna shiga dausayan Aljannoni, suna samun duk abin da suke so a wurin Ubangijinsu.wannan ita ce falala mai girma*Wannan fa shi ne abin da Allah yake yin albishir da shi ga bayinsa wadanda suka ba da gaskiya suka kuma yi ayyuka na gari.Ka ce:Ba na tambayar ku wani lada a kan sa (isar da sakon) sai dai kawai Soyayya ta iyalan gida Na. Duk wanda ya aikata wani aiki kyakkyawa za Mu kara masa kyakkyawan sakamako a kansa.Hakika Allah mai gafara ne Mai godiya) suratu Shura Aya ta 22 da kuma ta 23.a bayyane yake wannan Nassi na Alkur'ani mai girma ya tabbatar mana da cewa Soyayyar iyalan gidan Anabta tsarkaka ita ce kyakkyawa da Allah madaukakin sarki ya ke yin kari na albarka domin isar da Mutum zuwa mafi martaba na Aljanna. Kamar yadda Soyayyar Ma'aiki (s.a.w.a) wasila ce ta ijtihadi da kokari wajen Da'a da kuma biyayyar Ubangiji, da kuma rabauta da matsayi irin na wadanda Allah Madaukakin sarki ya ni'imce su daga Annabawa, siddika, shahidai da kuma salihai kamar yadda muka karanta a riwayar wani Mutum daga cikin Ansar da ta gabata.
Masu Saurare takaicecciyar amsar da za mu fahimta a Shirin na Yau, shi ne Hakika Soyayyar Annabin Rahama(s.a.w.a) da kuma gabatar da ita kan ko wata irin soyayya hakki ni na Ma'aiki a kan dukkanin Mumunai har zuwa ranar Alkiyama, kuma ita wasila ce ta kokari wajen kara da'a da biyayyar Allah, dabi'antuwa da soyayyarsa da kuma cimma martaba madaukakiya tana tabbatuwa ne da soyayyar iyalan gidansa tsarkaka da kuma yin Bara'a da nuna kiyayya da masu kin Allah da Ma'aikinsa gami da iyalan gidansa tsarkaka.
**********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.