Jun 07, 2017 12:26 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a Shirye-shiryen a uku na baya da suka gabata mun yi bayyani kan hakin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) a kan mu, da suka hada da hakin da'a ko biyayya, da kuma hakin komawa zuwa gare shi cikin sabani domin warware shi, sai kuma hakin soyayya na Shi da na iyalan gidansa tsarkaka gami da yin tawaye ga makiyansu, Shirin na Yau kuwa zai yi bayyani kan hakki na hudu, wato tambayarmu ta Yau ita ce mine ne hakki na hudu ga  Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da ya wajaba a kanmu? Kafin amsa wannan tambaya sai a dakace mu da wannan.

*************************Musuc********************************

Masu Saurare, barkanmu da sake saduwa, idan muka yi nazari cikin Nassosi da dama za mu ga cewa daga cikin Hakin Ma'aikin Allah (S.a.w.a) da ya wajaba kanmu shi ne yi masa Salati a yayi da aka ambaci sunansa, kuma hakika Allah madaukakin sarki ya kebe Sa da wannan karama daga cikin Annabawansa (a.s) inda ya yi umarni da yi masa salati, Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika Allah da Malaikunsa suna yin salati ga Annabi. Ya Ku wadanda kuka bada gaskiya, ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama sallama mai yawa) Suratu Ahzabi Aya ta 56, Allah ka yi salati ga Annabi Muhamadu da kuma iyalan gidansa tsarkaka, Masu Saurare Hakika wannan Aya mai albarka ta kira mu da mu yi koyi da Allah madaukakin sarki da kuma malaikunsa wajen yi wa Annabi salati, Hadissai da dama  sun yi sharhi ga wannan Aya mai girma kamar yadda ya zo cikin Tafsirul Aliyu bn Ibrahim AlQummy, an ce ma'anar yiwa Annabi Salati ga Allah tabaraka wa ta'ala shi ne ya tsarkake shi (s.a.w.a) daga duk wata dauta, amma salatin Malaiku (a.s) a gare shi shi ne Yabo da kuma godiya a gare shi, shi kuma Salatin Mutane a gare shi (s.a.w.a) shi ne yi masa Addu'a da gaskanta shi gami da yin tabbaci game da falalarsa.misali cikin Littafin Ma'anil- Akhbar  na Shekh Saduk kamar yadda aka ruwaito cikin Tafsirul-Burhan da sauransu daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da yake amsa tambayar daya daga cikin sahabansa dangane da ma'anar Ayar da ta gabata sai ya ce:(Salati daga Allah madaukakin sarki rahama ce, daga kuma Mala'iku tsarkaka ce, daga Mutane kuma Addu'a ce, amma fadar Allah madaukakin Sarki:( kuma ku yi sallama sallama mai yawa) shi ne meka wuya a kan abinda aka ruwaito daga gare shi, a wata riwayar kuwa meka wuya gareshi a kan komai, a wata riwaya ta uku kuma meka wuya gare shi ta hanyar wulaya da kuma abinda ya zo da shi.Masu Saurare, Hakika Hadisai da dama sun yi ta'akidi da kuma tabbaci kan mahimanci da kuma albarkar dake tattare da aiki da umarnin Alkur'ani da ya gabata tare kuma da cika wannan wajibi daga wajiban da suka rataya kanmu dangane da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin Littafin Kafi an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Babu wasu Mutane da za su hadu a wani Majalisi kuma ba su ambaci sunan Alllah madaukakin sarki, kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba face wannan mazalisi na su ya kasance Hasara da bala'I a gare su) wannan hadisi a bangaren Litattafan Shi'a Kenan, a bangaren Litattafan Sunna kuma, Hadisin da aka ruwaito cikin littafin Sunanul Kubra daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(babu wasu Mutane da za zauna a wani Majalisu su  kuma waste ba tare da su yi salati a gare Ni, Majalisun zai kasance yana doyi

kamar doyin Gawa). A cikin Littafin Sunanu Ibn Majah, an ruwaito Hadisi daga Ma'aiki (s.a.w.a) ya ce:(duk wanda ya manta yi mani salati , ya bata daga hanyar shiga Aljanna), a cikin Littafin Jami'ul-Sagir, an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Wanda ya fi kowa rowa daga cikin Mutane shi ne wanda za a ambaci Suna Na a wajen sa amma bai yi salati a gare ni ba) har ila yau an ruwaito daga gare shi (s.a.w.a) ya ce:(daga cikin bijerewa, a ambaci suna Na a gaban Mutum ba tare da ya yi mani salati ba) Allah ya kiyaye Mu Masu saurare da bijerewa Ma'aikin Allah (s.a.w.a).

************************Musuc******************************

Masu Saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa Shirin na Karamin Sani Kunkumi na zo muku ne kai tsaye daga Sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, Ci gaban Shirin zai fara da Hadisin Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) wanda aka ruwaito cikin Littafin Kafi na Sikatu-Islam Kulaini, Imam ya cewa sahabansa :( ku yi salati ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka duk lokacin da na  ambaci Sunansa  ko kuma Lokacin da mai Ambato ya kira sunansa a kiran Salla ne ko kuma a wani wuri ne na daban) a cikin Littafin Sawabul-A'amal, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya ce:(Duk wanda ya fada a karshen Sallar Assuba da kuma Sallar Magarib kafin ya Ambato sunan wani ko kuma ya yiwa wani mutum magana:(Hakika Allah da Malaikunsa suna yin salati ga Annabi. Ya Ku wadanda kuka bada gaskiya, ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama sallama mai yawa) sannan kuma ya ce Ya Ubangiji ka yi salati ga Annabi Muhamadu da kuma iyalan gidansa da Zuriyarsa, Allah zai biya masa bukatunsa dari, saba'in a nan Duniya, talatin kuma a Lahira). A cikin Addu'ar neman biyan bukatu da aka ruwaito cikin Littafin Sahifa ta Shugaban Masu Sujada, Imam (a.s) ya ce:(Ya Ubangiji kuma kayi salati ga Annabi Muhamadu da Iyalansa, Salati dawwamamme maras yankewa har abada wanda kuma ba shi da karshe ga tsayiwarsa ka kuma sanya shi taimako a gare Ni kuma sanadi na samun rabautar bukatuna, Hakika kai mabuwayi mai karamci ne).Hakika Masu Saurare Hadisan da aka ruwaito daga bangaren Ahlul-Bait (a.s) a kan falalar yi wa Annabi (s.a.w.a) salati su nada yawan gaske, kuma suna umartar mu da yawaita yiwa Annabin Salati, kuma suna bayyana falalarsa wajen biyan bukatu da kuma amsar Addu'a gami da samun gafarar zunubai da kuma tsarkaka daga gare su, mafi girma daga cikin albartun yiwa annabin salati, Shi ne Duk wanda ya yi masa salati (s.a.w.a) so guda domin soyayya gareshi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi zai yi masa salati goma, sanannan abu ne salatin Annabi ga Mutane yana saukar da nutsuwa a gare su.kamar yadda ta 103 cikin Suratu Tauba ta sarraha hakan. amma dangane da Sigar yiwa Annabi (s.a.w.a) a shar'ance da bai halitta a wuce iyaka kansa ba, shi ne salatin da aka yi masa tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma wannan shi ne abinda Nassi na Ma'aiki ya yi ishara da shi,cikin shaharen hadisin da aka ruwaito a bangarorin Shi'a da Sunna, Hakika Buhari,Muslim, Ahmad bn Hanbali, Turmizi, Abu Dawuda, ibn Majah tare da Nisani dukkanin su sun ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Ku ce Ya Ubangiji Kayi Salati ga Muhamadu da iyalan Muhamadu kamar yadda ka yi salati ga Ibrahimu da iyalan Ibrahimu Hakika Shi Allah abin godewa ne Mai girma, ka kuma yi albarka ga Muhamadu da iyalan Muhamadu kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahimu da iyalan ibrahimu Hakika Shi Allah abin godewa ne Mai girma) kamar yadda kuma manyan Maliman Sunna suka ruwaito hadisi na hanin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) a kan yin Salatin Batra'a wato yi  masa salati ba tare da sanya iyalan gidansa tsarkaka ba.

Masu Saurare takaicecciyar amsar da mu iya fahimta a wadannan Nassosi da suka gabata shi ne na daga cikin hakin Masoyinmu Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka da ya wajaba kanmu, yi masa Salati kamar yadda aka Ambato a aika ce bisa Umarnin Alkur'ani mai girma kuma ya kasance bisa kaifiya da kuma sigar da aka Ambato na sanya iyalan gidansa tsarkaka amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.