Hakin Da Ya Wajaba Kan Mu Ga Ma'aiki (s.a.w.a) 05
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan wasu hakokin Ma'aiki (s.a.w.a) da ya wajaba kan mu, Tambayar mu ta Yau Mine ne hakkin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na biyar da ya wajaba a kanmu ? amma kafin mu shiga cikin Shirin sai a dakace mu da wannan.
************************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kamar yadda Shirin ya saba zai fara da hasken shiriya na farko wato Alkur'ani mai tsarki, inda Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya kadda ku sha gaban Allah da Manzonsa (wajen hukunci). Kuma ku ji tsoron Allah, Hakika Allah Mai ji ne Masani.* Ya Ku wadanda kuka bada gaskiya kada ku daga muryoyinku sama da muryar Annabi kada kuma ku rika daga masa Magana kamar yadda sashinku yake daga wa Shashi don kada ayyukanku su lalace alhali kuwa ku ba (ku sani ba) ba kwa jin haka.*Hakika Wadanda suke yin kasa-kasa da muryoyinsu a wurin Manzon Allah wadancan su ne wadanda Allah ya jarraba zukatansu da tsoron Allah, suna da gafara da lada mai girma. *Hakika Wadanda suke kiranka ta bayan dakuna,mafiya yawansu ba sa hankalta.*Idan da kuma cewa dai su, sun yi hakuri har sai da ka futo wurinsu da ya kasance mafi alheri a gare su,Allah kuma Mai gafara ne Mai rahama) Suratu Hujurat daga Ayar farko zuwa Aya ta 5, kafin mu bayyana irin mu'amalar da ya kamata mu yi da ma'aikin Allah (s.a.w.a) kamar yadda wannan Aya ta yi bayani, za mu fara ishara da gaskiyar da Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya shiryar da Mu, inda a cikin ta yake bayyana mana yin iltizami da kuma riko da wannan hanya ta mu'amala tare da Masoyinmu Mustapha tsira da aminicin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma yin hakan hanya ce ta samun rabauta zuwa ga ziyararsa da kusanci da Shi a Lahira. Na'am Hakika Shekh Saduk cikin Littafinsa Sawabul-A'amal ya ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Duk wanda ya karanta Suratu Hujrat a ko wani Dare ko kuma ko wata Rana ya kasance daga cikin maziyartan Muhamadu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka). Masu Saurare, abin fahimta a wannan hadisi da kuma yin nazari game da ayoyin da suka gabata, sun bayyana mana tushen mu'alar da ya wajaba mu yi da ma'aiki (s.a.w.a) shi ne girmama shi da kuma karrama shi a yayin ko wata irin mu'amala tare da Shi (s.a.w.a) tare kuma da hani a kan aiyuka da kuma mu'amalar da ta sabawa hakan, a cikin Tafsiru Aliyu bn Ibrahim Qummy yardar Allah ta tabbata a gare shi, an ruwaito musababin saukar wadannan Ayoyi inda aka ce wani gungu daga cikin kabilar Bani Tamim sun kasance idan suka je wajen Ma'aikin Allah (s.a.w.a) sai su tsaye a bakin dakin sa suna kira Ya Muhamad Ka fito gare Mu, kuma sun kasance idan suna tafiya suna shiga gabansa, idan kuma suna Magana da shi, suna daga muryoyin su a kan ta ma'aikin Allah (s.a.w.a) suna cewa:Ya Muhamad Mi za kace dangane da kaza da kaza kamar yadda suke Magana ga sashinsu, Sai Allah madaukakin sarki ya saukar wadannan Ayoyi masu albarka.kuma kamar yadda zahiri a Ayar farko shiga gaban Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya sabawa tsoron Allah kamar yadda ya zo a karshen Ayar (Kuma ku ji tsoron Allah, Hakika Allah Mai ji ne Masani) kuma hakika Maliman tafsiri sun bayyana cewa Shiga gaban Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya shafi dukkanin abinda ya gabata a zance ne ko kuma a aiki ne, kamar yadda wannan adabi yake gudana a lokacin rayuwarsa ne da kuma bayan fakuwarsa (s.a.w.a), domin haka ne ma hadisai da dama suka yi hani na bawa Hubbarinsa baya, kuma suka yi hukunci da bacewar sallar da aka yita yayin da aka bawa Hubbarin Ma'aiki (s.a.w.a) baya, ko da ma ba dukkaninsa ba ne aka bashi baya ko kuma a zarta shi kadan.
***********************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashin Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban Shirin zai ci gaba da bayyani kan Ayoyin Suratu Hujrat da ta gabata, dangane da fadar Allah madaukakin sarki na cewa (kada kuma ku rika daga masa Magana kamar yadda sashinku yake daga wa Shashi) ishara ne na girmamawa da kuma karamci a gare shi a yaran khuduba, kamar yadda Aya ta 63 cikin suratu Nur ta yi ishara da hakan inda Allah madaukakin sarki ke cewa: (Kada ku mayar da kiran Manzo a tsakaninku kamar kiran junanku ga juna) Suratu Nuri Aya ta 63, a cikin Tafsiril-Aliyu bn Ibrahim AlQummy an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) yayin da yake bayyani kan ma'anar wannan Aya sai ya ce:(Allah madaukakin sarki na cewa kada ku ce Ya Muhamad, ko kuma Ya Aba Kasim, saidai ku ce Ya Annabin Allah, ko kuma Ya Ma'aikin Allah) abinda kuma ake nufi da kada a Ambato sunansa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka kai tsaye shi ne fadar hakan ya kori siffar Annabci da risalarsa, ba wai ana nufin kada a ambaci sunansa mai girma ba ko kuma kuniyarsa sai dai an so a kira shi da sunan Annabin Allah ko kuma Ma'aikin Allah.a cikin Hadisan iyalan gidan Anabta tsarkaka an yi hani da daga murya a wajen Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka a rayuwarsa da kuma bayan kaurarsa da kuma wajen Khubbarinsa mai tsarki, Hakika Shugabanmu Imam Husain (a.s) ya kafa hujja da fadar Allah madaukakin sarki na cewa:( Ya Ku wadanda kuka bada gaskiya kada ku daga muryoyinku sama da muryar Annabi) da kuma fadarsa:( Hakika Wadanda suke yin kasa-kasa da muryoyinsu a wurin Manzon Allah wadancan su ne wadanda Allah ya jarraba zukatansu da tsoron Allah, suna da gafara da lada mai girma.)Hakika Imam (a.s) ya kafa hujja da wadannan Ayoyi masu girma a yayin da yake jayayya da wadanda suka hana ya jadadda alkawari tare da janazar Dan Uwansa Imam Hasan (a.s) a Hubbarin Kakansa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma Hakika Imam (a.s) dangane dangane da wanan jayayyar da aka ruwaito cikin Littafin Kafi na Sikatul-Islam Kulaini ya yi bayyani dangane da yadda wannan mu'amala ke ci gaba da gudanar bayan fakewar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) inda ya ce:(Hakika Allah madaukakin ya harmta ga Muminan da suka rasu kamar yadda yayi karamci gare su a yayin da suke raye) ma'anar wannan hadisi shi ne duk abinda aka haramta a yiwa Muminai suna raya ya rahamta a yi musu bayan sun rasu.Masu Saurare Takaicecciyar amsar da za mu fahimta cikin wannan Shiri da ya yi bayyani a bisa hakki na biyar daga cikin hakkokin da suka rataya kanmu dangane da Masoyinmu Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare su tare da iyalan gidansa tsarkaka shi ne Karamci da kuma girmamawa ta hanyar kin shiga gabansa a kan komai, da kuma rashin daga murya a gabansa da kuma kiran sa da Lakabin Annabta da makamancin da ya kasance misdaki ne na karamci da girmamawa, kuma wannan mu'amalar da ya wajaba mu yi da shi (s.a.w.a) na gudana ne bayan fakuwarsa da kuma lokacin ziyarar Hubbarinsa mai tsarki kamar yadda yake gudama a lokacin rayuwa.
**********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.