Jul 02, 2017 06:43 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata mun yi bayyani a kan hakki na biyar daga cikin hakkokin da suka rataya kanmu dangane da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, shi ne hakin Girmamawa da kuma rashin shiga gabansa a dukkanin al'amuranmu tare da kuma rashin daga murka a gabansa, Tambayar ta Yau mine ne hakki na shidda daga cikin hakkokin da suka rataya kanku dangane da Ma'aiki (s.a.w.a)? kafin amsa wannan tambaya sai a dakace mu da wannan.

******************Musuc***************************

Masu Saurare Barkanmu da sake saduwa, Hakki na Shida daga cikin hakkokin Annabin Rahama Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi tare da iyalan gidansa tsarkaka a kan Mu shi ne Hakkin Mubaya'a wato tabbatar da goyon baya, Hakika cikin wurare uku na Alkur'ani mai girma an Ambato hakin Mubaya'a ga Annabi a kan ko wani musulmi, da farko za mu fara da suratu Fatahi, Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika wadanda suke mubaya'a (tabbatar da goyon baya) da kai, ba shakka suna mubaya'a ne da Allah,hannun Allah yana saman hannayansu, sannan duk wanda ya warware ta (wato mubaya'ar ) Hakika kansa ya warwarewa, wanda kuma ya cika abin da ya yi wa Allah alkawari a kansa, to da sannu zai bashi lada mai girma) Suratu Fatahi Aya ta 10. Hakika masu saurare tabbatar da wannan gaskiya ta Anabta da kuma cika wannan alkawari gare shi sanadi ne na rabauta da lada mai yawa, da kuma rabauta da yardar Allah tabaraka wa ta'ala kamar yadda Aya ta 18 cikin Suratu fatahi tayi bayyani Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika Allah Ya yarda da muminai da suke yin mubaya'a da Kai a karkashin bishiya,sai Allah Ya san abin da yake cikin zukatansu sannan ya saukar musu nutsuwa ya kuma sama musu mabayyanin budi na kurkusa (wato cin nasara))Suratu Fatahi Aya ta 88.Hakika Alku'ani mai girma ya bayyana cewa wannan hakki ya rataya ga muminai Mata, domin shi wajibi ne ga kowa, bai takaita a kan nasarar yaki ba, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya Kai Wannan Annabi! Idan muminai mata suka zo maka suna mubaya'a da kai, a kan ba za su tara wani da Allah ba, ba za su yi sa taba, ba za su yi zina ba, ba za su kashe 'ya'yansu ba, ba za su zo da wata karya ba wadda za su kage ta da tsaskanin hannayensu ko da kafafuwansu ba, kuma ba za su saba maka cikin abin sani a shari'a ba sai kayi mubaya'a da su ka kuma nema musu gafarar Allah, hakika Allah mai yawan gafara ne mai jin kai ne) Suratu mumtahinati Aya ta 12, bayan karanto wadannan Ayoyi, tambayar da za ta biyo baya ita ce mi ake nufi da mubaya'a, kuma ta yaya za mu cika wannan wajibci ga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka a zamanin da muke ciki? Masu saurare, abin fahimta daga Aya ta 10 ta Suratu Fatahi kanta, wato mubaya'a nau'I ne na riko ga wanda yayi mubaya'ar kamar yadda Ayar ta yabi wanda yayi riko da wannan mubaya'a yana mai cewa :( wanda kuma ya cika abin da ya yi wa Allah alkawari a kansa, to da sannu zai bashi lada mai girma), cikin tafsirin Al-Mizan Allama tabataba'I ya bayyana cewa Mubaya'a wani nau'in alkawari ne ta hanyar kokari na da'a da biyayya, wato hakikanin ma'anarsa shi ne meka hanu ga mai milki domin ya yi aiki da shi ta hanyar da yaga dama. Da wannan ma'ana za mu fahimci cewa yiwa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka mubaya'a da kuma da'a , yiwa Allah madaukakin sarki mubaya'a da da'a ne kasancewarsa ma'asumi  domin shi duk abinda ya fada wahayi ne ba ya firici da son ran sa.

***********************************Musuc************************

Masu Saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa Shirin na Karamin sani Kukumi na zuwa muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, hakika yi wa ma'aki mubaya na a matsayin yiwa Allah madauaki sarki, kuma da hakan ne Mumini zai sadaukar da kansa gami da Dukiyarsa ga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi domin ya yi abinda yake so da kuma abinda ya ga dama da shi da kuma dukiyarsa domin ba ya son wani abu face abinda Allah madaukakin sarki yake so na gyarar Bayi da kuma rabautar su a Duniya da Lahira daga bisani kuma ya basu Lada mai girma, a hakikanin gaskiya abinda ake nufi da mubaya'a, gabatar da aiki a aikace bisa fahimtar meka wuya Bawa ga umarnin Allah madaukakin sarki, da kuma cika alkawari bisa wannan al'amari, Hakika wannan matsayi ya kebanta ga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) saboda kariyar da yake da ita na Isma Mutlaka, kuma cikekkiyar biyayyarsa ga Allah madaukakin sarki kamar yadda Shugabanmu Imam Aliyu bn Musa Arridha ya yi ishara a hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Uyunul-Akhbar yana mai cewa:(Hakika Allah madaukakin sarki ya fifita Annabinsa Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka a kan dukkanin halittu daga Annabawa da Mala'iku, ya sanya kuma Da'a da biyayyarsa a matsayin da'a da biyayya a gare shi, mubaya a gare shi na a matsayin mubaya'a ga Allah madaukakin sarki, haka zalika ziyarsa a Duniya da Lahira a matsayin ziyartar Allah tabaraka wa ta'ala, Allah madaukakin sarki ya ce:( Wanda ya bi Manzo, to hakika ya bi Allah), kuma Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce: Duk wanda ya ziyarce Ni a rayuwa ta da kuma bayan mutuwa ta, hakika kamar ya ziyarci Allah ne, kuma matsayin sa (s.a.w.a) a Aljanna mafi girman matsayi ne, duk wanda ya ziyarce shi da matsayinsa a Aljanna kamar ya ziyarci Allah tabaraka wa ta'ala ne).

Masu Saurare, dangane da tambayarmu ta biyu wato ta yaya za mu cika hakkin mubaya'a ga Ma'aikin Allah bayan wafatinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi tare da iyalan gidansa tsarkaka a zamanin da muke ciki? wannan shi ne abinda Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya amsa mana da kansa, cikin wani bangare na Khudubar ranar Qadir,(Duk wanda ya yi mubaya'a a gare Ni hakika ya yi mubaya'a ga Allah, hannun Allah yana saman hannayansu, Ya Ku Muatne ku ji tsoron Allah, kuma ku yi mubaya'a ga Ali Shugaban Muminai da Hasan da Husain da kuma Shugabanin Hikima tsarkakekkiya madawwamiya, Allah zai hallaka wanda ya kauracewa wannan mubaya'a ya kuma jikan wanda ya cika ta), har ila yau Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana cewa:(Ya Ku Mutane Hakika Ni na bayyana muku kuma na fahimar da ku, kuma wannan Ali ne zai fahimtar da ku baya Na,Ku saurara bayan kamala khuduba ta ina kiranku zuwa ba Ni Hannu bisa mubaya'a ta da kuma tabbatar da ita, sannan kuma ku baiwa Imam Ali hannu ku yi masa mubaya'a baya Na, Ku Saurara!Hakika Ni Na yi mubaya'a ga Allah, Shi Kuma Ali Hakika ya yi mubaya'a a gare Ni, kuma Ni na karbi mubaya'arsa daga wajen Allah madaukakin sarki, sannan duk wanda ya warware ta (wato mubaya'ar ) Hakika kansa ya warwarewa) domin haka Masu saurare, cika hakkin mu na mubaya'a ga Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka a wannan zamani, da farko na tabbatuwa ne ta hanyar yi masa alkwari na yi masa da'a da biyayya a gare shi a kan dukkanin Umarni da hani da suka tabbata daga gare shi ne, na biyu kuma mubaya'a ga Shugaba Ma'asumi daga iyalan gidansa tsarkaka da ya kasance biyayya da kuma meka wuya gare shi, yin da'a da kuma meka wuya ne ga Umarnin Allah madaukakin sarki, domin Shi Shugaba ma'asumi ne da isimar Annabi Muhamad (s.a.w.a) kuma wannan shi ne ya jawaba kanm8 mu tabbatar ga Shugaban zamaninmu Imam Mahdi (a.t.f), da fatan Allah ya bamu ikon cika wannan alkawari don albarkar Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.