Jul 02, 2017 06:45 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau, Mine ne Hakki na bakwai daga cikin hakkokin da suka wajabta kanmu dangane da Ma'aikin Allah (s.a.w.a)? Hakika a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan wasu hakkoki guda shida da suka wajaba kanmu dangane da Ma'aiki(s.a.w.a) kamar haka, hakkin da'a da biyayya, hakin komawa gare shi domin yin hukunci garemu a yayin wani bullar wani sabani, hakin soyyaya, hakin yi masa salati, hakin girmamawa kamar yadda Allah madaukakin sarki ya girmama shi,da kuma hakin mubaya'a da kuma meka yuwa gare shi ga dukkanin umarninsa, bayan hakan Mine ne Hakki na bakwai daga cikin hakkokin da suka wajabta kanmu dangane da Ma'aikin Allah (s.a.w.a)? kafin amsa wannan tambaya, sai a dakace mu da wannan.

*********************Musuc**************************

Masu saurare, Haki na Bakwai daga cikin hakkokin Rahamar Allah mai girma Manzo tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka da ya wajaba kanmu shi ne hakin ziyartar sa (s.a.w.a), wannan Shi ne abinda za mu amfana daga Nassosi da dama na Alkur'ani da Sunna, kamar yadda Ayoyi dake kiran muminai zuwa Hijra ga Allah da Ma'aikinsa suka yi ishara da hakan, domin haka ziyartarsa (s.a.w.a) na daga cikin misdakin hijra zuwa gare shi a zamanin rayuwarsa da kuma bayan fakuwarsa, Hakika cikin Suratu Nisa'I Allah tabaraka wa ta'ala ya yi ishara kan girman ladan Hijra zuwa ga Allah da Ma'aikinsa, Allah madaukakin sarki ya ce:(Duk wanda ya yi hijra saboda Allah to zai sami wurare masu yawa a bayan kasa na turmuza hancin abokan gaba da kuma yalwa.Duk wanda ya fita daga gidan sa yana mai kaura zuwa ga Allah da Manzonsa, sannan mutuwa ta riske Shi(a hanya), to ba shakka ladansa cikakka ya tabbata a wurin Allah. Allah kuwa ya kasance Mai yawan gafara ne Mai yawan Rahama) Suratu Nisa'I Aya ta 100, Hakika Annabin Rahama Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana mana cewa ziyartarsa na daga cikin misdakin yin hijra zuwa ga Allah madaukakin sarki, a cikin Littafin Kafi na Sikkatul-Islam Kulaini, an ruwaito hadisi Shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya ce:(Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce: Duk wanda ya isa Makka a matsayin Alhaji wato Bako kuma bai ziyarce Ni ba, zan kaurace sa.ranar Alkiyama, kuma wanda ya ziyarce Ni ceto Na ya wajaba a gare shi, wanda kuma ceto Na ya wajaba a gare Shi, Aljanna ta wajaba a gare shi, duk kuma wanda ya rasu a tsakanin  harami biyu wato Makka da Madina ba za a yi masa Hisabi ba, duk kuma wanda ya rasu yana mai hijra zuwa ga Allah ta'ala, Allah zai tayar da shi tare da Mutanan Bader) Masu saurare, wannan hadisi mai albarka ya bayyana mana cewa rashin Ziyartar Ma'aiki Allah ga Alhaji wani nau'I ne na bijerewa Ma'aiki (s.a.w.a) da hakan zai yi sanadiyar kauracewa Ma'aikin Allah a gare shi ranar Alkiyama, kuma wannan umarni shi ne abinda za mu iya fahimta da wata Aya ta Suratu Hajji, domin ita wannan Aya ta yi amfani da wasu kalamomi kamar za su zo maka, ma'ana za su zo wa Ma'aiki domin ziyartar Dakin Allah mai girma, zuwan kuma ko ya kasance ga Annabi Ibrahimu Khalilullah (a.s) ko kuma ga Ma'aikin Allah (s.a.w.a). Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma ka yi shela cikin Mutane saboda yin hajji, za su zo maka matafiya a kasa da kuma kan kowanne rakumi, za su zo maka daga kowanne lungu mai nisa) suratu Hajji Aya ta 27.domin haka ne ma Nassosi da dama suka bayyana cewa kamala kuma da cikar aiki Hajji na tabbatuwa ne bayan ziyarar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da kuma Shugabanin Shiriya na iyalan gidan Anabta tsarksaka, kamar yadda aka ruwaito cikin Littafin Kafi daga Shugabanmu Imam Muhamadu Bakir (a.s) a yayin da ya ga Mutane ba su son abinda za suyi ba sai ya ce:(Na rantsa da Allah ba a umarce su ba da wannan, ba abinda aka umarce face su gusar da kazantar su (kamar yin aski da yanke farce) kuma su cika alkawarinsu na yin hadaya da layya, kuma su biyo ta kanmu domin su bamu labarin wulayarsu sannan kuma su bayyana Nasarar su a gare mu).

*****************************Musuc******************************

Masu Saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar jumkhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin tahran,Hakika masu saurare idan muka koma cikin suratu Nisa'a za mu cewa Allah tabaraka wa ta'ala ya sanya ziyartar Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka cikin mafi girma na hanyoyin tawassali zuwa gare shi domin gafarar zunubai, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ba Mu aiko wani Manzo ba sai don a bi Shi da izinin Allah.Da dai a ce lokacin da suka zalunci kansu sun zo maka sannan suka nemi gafarar Allah, Manzo kuma ya nema musu gafara, to lallai da sun sami Allah mai yawan yafewa ne Mai yawan rahama)Suratu Nisa'I Aya ta 64.baya ga wannan , Aya ta 5 da kuma ta 6 cikin Suratu Munafikun sun bayyana cewa rashin cika wannan hakki daga cikin hakkokin Annabin Rahama, da kuma bijerewa ziyarar Annabi domin neman gafarar Ubangiji na daga cikin alamomin Nifaki da munafikai gami da fasikai kuma hakan na kasancewa musabbabi na haramta musu rahamar Ubangiji. Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Idan Kuma aka ce da su ku zo Manzon Allah ya nema muku gafara sai su juyar da kansu, ka kuma gan su suna fijirewa kuma suna masu girman kai* Duk daya ne a wurinsu ko ka nema musu gafara ko ba ka nema musu gafarar ba, Allah ba zai gafarta musu har abada ba.Hakika Allah ba ya shiryar mutane fasikai) Suratu Munafikuna Aya ta 5 da ta 6, Hakika masu saurare daga cikin fadadar Rahamar Ubangishi, Shi ne yadda Allah tabaraka wa ta'ala ya sanya cika wannan hakki na hakkokin Ma'aiki (s.a.w.a) a kanmu tabbatuwar  ziyararsa daga kusa ko daga Nesa ga wanda bai samu damar ziyartar shi ba ko kuma ba shi da ikon ziyartar shi zuwa garin Madina.wato daga gidan sa ko garinsu yana iya ziyartar Ma'aikin Allah(s.a.w.a). a cikin littafin Tahzibul-Ahkam, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce :(Duk wanda ya ziyarce Ni bayan rasuwa na , ya kasance kamar wanda ya yi hijira gare Ni a rayuwa ta, idan kuma ba ku samu damar hakan ba to ku aike da sallama gare Ni domin tabbas sallamarku ta na isa zuwa Ni), Aminci gare Ka Ya Masoyin Allah! Ya zababben Allah da rahamarsa gami da Albarkarsa.

Masu Saurare, takaicecciyar amsar da muka fahimta daga Nassosin da suka gabata, Shi ne daga cikin abinda ya wajaba gare mu dangane da hakkokin Ma'aikin (s.a.w.a) Shi ne cika hakkin ziyartarsa (s.a.w.a) wanda kuma hakan ne ke sanya cika da kamalar aikin hajji, da kuma rabauta da yardar Allah gami da gafarar sa. Kuma ziyartar Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na daga cikin misdakin Hijra zuwa gare Shi a rayuwarsa da kuma bayan fakuwarsa, kuma wannan yana  tabbatuwa ne daga kusa ko daga Nesa. Da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon cika wannan hakki na ziyarar Annabin Rahama (s.a.w.a).

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.