Jul 06, 2017 06:56 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ,Shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurbata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau, Mine ne Hakki na takwas daga cikin hakkokin da suka wajabta kanmu dangane da Ma'aikin Allah (s.a.w.a)? Hakika a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan wasu hakkoki guda bakwai da suka wajaba kanmu dangane da Ma'aiki(s.a.w.a) kamar haka, hakkin da'a da biyayya, hakin komawa gare shi domin yin hukunci garesu a yayin wani bullar sabani, hakin soyyaya, hakin yi masa salati, hakin girmamawa kamar yadda Allah madaukakin sarki ya girmama shi, hakin mubaya'a da kuma meka wuya gare shi ga dukkanin umarninsa da kuma hakkin ziyartar shi daga nesa ko daga kusa,Hakin bayar da Khumusi bayan hakan Mine ne Hakki na tara daga cikin hakkokin da suka wajabta kanmu dangane da Ma'aikin Allah (s.a.w.a)? kafin amsa wannan tambaya, sai a dakace mu da wannan.

*********************Musuc**************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa,Hakika cikin Nassosi masu albarka za mu fahimci cewa Hakki na tare daga cikin hakkokin da suka wajaba kanmu dangane da Ma'aiki (s.a.w.a) shi ne Hakki Ubba ga Al'umma wacce ta zama  jiki ga mafi martabar matsayi cikin rahama da tausayi a kan Ma'aikin Allah (s.a.w.a) bisa maslahar Bayi kamar yadda muka Ambato cikin hadisai da dama cikin shirye shiryen da suka gabata, A cikin Suratu Tauba Allah tabaraka wa ta'ala ya ce: (Hakika Manzo daga cikinku ya zo muku,abin da zai cuce ku yana damunsa, mai kwadayin shiriyarku,mai tausayawa kuma mai jin kayi ga muminai) Suratu Tauba Aya ta 128. Hakika masu saurare cikin Hadisai masu inganci na bangarori daban daban na musulinci an bayyana cewa Annabi mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka nada matsayi uba ga Bayi, Kuma hakika Ayatullahi Sayyida Mar'ashi Annajafi yardar Allah ta tabbata a gare shi ya tattaro hadisi da dama da suka bayyani a kan wannan maudi'I cikin litattafan Ahlu-Sunna a Littafinsa mai suna Muhakatu-Ihkakul-Haq,daga cikin wadannan hadisai, wanda aka ruwaito cikin Littafin Lukka mai Suna Mufradat na Abi Kasim Ragib Esfahani, daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Ya Ali Ni da Kai iyayen wannan Al'umma ce, kuma hakkinmu a kansu ya fi hakin iyayen da suka aife su, domin mu tseratar da su, idan muka yi biyayya gare mu daga wuta zuwa tabaceccen gida, kuma mu hadar da su zuwa bauta ta zababbun bayi), a cikin Sharhin Ikhtiyari Ma'arifatil-Rijal na Shekh Tusy, an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Ya Ali Ni da Kai iyayen wannan Al'umma ce, kuma Allah ya la'anci wanda ya sabawa Iyayensa).kuma a cikin tafsirin Burhan na Allama Bahrani an ruwaito haidisi daga babban jikan Annabin Rahama (s.a.w.a) wato Imam Hasan Mujtaba (a.s) ya ce:(Muhamadu da Ali sune iyayen wannan Al'umma, albarka ta tabbata ga wanda ya san wannan hakki, da kuma hakkin su cikin ko wani hali kuma mai biyayya gami da da'a a gare su, Allah zai sanya shi daga cikin mazauna Aljannarsa ya kuma rabautar da shi da karama gami da yardarsa), bisa wadannan haskake da muka bayyana za mu fahimci cewa daga cikin wajibcin da ya wajaba a kanmu game da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka cika hakkokin Uba kan 'ya'yansa ta hanyar mafi girma da martaba saboda mikamin iyaye na ma'anawiya da Allah madaukakin sarki ya sanya a kan sa (s.a.w.a). Hakika Nassosi masu albarka sun bayyana cewa hakkokin iyaye a kan 'ya'ya su ne hakkin biyayya da kuma neman yardar su da kuma gode musu, yi musu sadaka, bayar da kauta na kyawawen aiyuka gare su, kyautata musu, jin kaisu da sauransu da kuma dukkanin abinda ya kamata a yi game da Annabin Rahama ta fuskar da ya dace saboda matsayinsa mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalanm gidansa tsarkaka.a cikin Tafsirin Daka'ik an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) y ace:(hakika Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka da kuma Imam Ali (a.s) sun fi jin kai ga bayi ga iyayensu da suka aife su, kuma a gare mu soyayya a cikin littafin Allah, kuma Ma'aikin Allah (s.a.w.a) da Imam Ali(a.s) su ne iyayen da Allah ya umarci zuriyar su su gode musu).

*************************Musuc***************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran, bisa tafsirin Aya ta 14 cikin suratu Lukman inda Allah tabaraka wa ta'ala ke cewa:(Saboda haka ka gode min da kuma iyayenka) cikin littafin Usulul-Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugaban Muminai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Iyayen da Allah madaukakin sarki ya wajabta godiya a gare su su ne wadanda suka aifar da ilimi,kuma suka gaji hikima kuma ya umarci Mutane da yi musu da'a da biyayya), a cikin Littafin Raudatul-Wa'izin, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) yayin da yake bayyani game da misdakin Aya ta 23 cikin suratu Isra'I, inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Ubangijinka kuwa ya hukunta cewa kada ku bauta wa (wani ) sai Shi,da kuma kyautatawa ga iyaye…)sai ya ce Iyaye su ne Muhamadu da Ali. Wato hakika Allah ya yi umarni da kyautata musu amincin Allah ya tabbata a gare su, saidai kuma ta yaya za mu kyautata ga Annabin Rahama mai girma(s.a.w.a) alhali shi ne babban makoma wajen kautatawar Allah madaukakin sarki a kan hallitunsa? Masu saurare, Shugabanmu Imam Hasan Mujtaba (a.s) ya amsa mana tambaya yayin da yake ishara kan kyautatawa ga iyayen wannan Al'umma wato Mustatapha (s.a.w.a) da kuma wasiyinsa Murtada (a.s) ya kasance ta hanyar kautatawa zuwa zuriyarsu da kuma makusantansu, kuma ya bayyana mana mahimancin cika wannan wajibi cikin hadisin da aka ruwaito a Littafin Biharu-Anwar daga Imam Hasan Askari (a.s) ya ce Imam Hasan Mujtaba (a.s) ya fada cewa:(Na hore ka da kyautatawa zuwa ga makusantan iyayen Addininka Muhamadu da Ali, ko da kuwa ka yi rashin makusantanka iyayenka na jini, to kadda kayi rashin makusantan iyayenka na Addininc wajen biyar makusantan iyayenka na jini, idan wadannan suka yi godiya ga iyayenka na Addininka Annabi Muhamadu da Imam Ali amincin Allah ya tabbata a gare su, za su samar maka da godiyar iyayenka na Jini, Hakika makusantan iyayenka na Addini idan suka gode maka a wajen su, komin kadan za a dube su da idan rahama kuma a shafe zunubanka da na su ko da kuwa yawansu ya kai yawan tsakanin Asara zuwa Al'ashi, idan kuma makusantan iyayenka na jini suka gode masa alhali ka barar da makusantan iyayenka na Addini, hakan ba zai wadatar da kai da komai ba).

Masu saurare,Hakika an ruwaito Hadisai da dama da suke bayyani kan kiran Mutane na su girmama Zuriyar Anabta  a matsayi giramama Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, da kuma cika hakin sun a iyaye ga Al'umma kai ga ma Dan Adam baki daya har zuwa ranar Alkiyama.

*********************Musuc*************************************

Masu saurare ganin lokaci da aka debawa shirin ya zo karshe, a nan za mu dakata, sai kuma a maku nag aba da yardarm allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimamakawa shirin har ya kamala musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da jagoranci shirin nike muku fatan alheri, wassalama alekum.