Ranar Duniya Ta Koda
A yau shirin zai maida hankali kan ranar duniya ta Koda, ranar da MDD ta ware domin fadakar da al’umma akan mahimmacin koda ga jikin dan Adam dama kare kai daga kamuwa da cututukan dakan shafi Kodar kan ta.
Jama’a masu saurare assalamu alaikum barkan ku da yau da kuma sake saduwa damu a cikin wannan shiri na lafiya sai da kula.
Shirin da a cikin sa muke tattauna dukkan batuwan da suka shafi kiwan lafiya bil adama musamen a hahiyar mu ta Afirka.
A yau shirin zai maida hankali kan ranar duniya ta Koda, ranar da MDD ta ware domin fadakar da al’umma akan mahimmacin koda ga jikin dan Adam dama kare kai daga cututukan dakan shafi Kodar da kan ta.
Ranar 10 ga watan Maris ta kowace shekara ita ce ranar da MDD ta ware domin fadakar da al’umma akan mahimmacin koda da ma yadda za’a kare kai daga kamuwa da cututukan dakan shafi kodar da kan ta.
A bana dai anyiwa ranar taken “” kula da koda, lafiyar gobe "
Wani bincike dai da masana sha’anin kiwan lafiya suka gudanar ya gano cewa dubban al’umma ne ke fama da matsalar koda ba tare da ma sun yi la’akari da hakan ba, sai lokaci ya kure.
To domin tattauna wannan batun a yau mun gayyato Dr Agali Anaba kwararan likita a babbar asibitin jihar Maradi dake jamahuriya Nijar, sannan kuma a hannu guda muna tare da Dr Buzu Buyidi jami'in kiwan lafiya a babbar asibitin jihar Zinder dake Nijar a cikin shirin dani Hassan Barka na shirya kuma na gabatar.