Oct 18, 2017 15:00 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 1-4 (Kashi na 695)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

--------------------------------

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta farko zuwa Aya ta 3 cikin suratu Kasas.

 

طسم

 

1-DA SIN MIN, Allah ne Ya san abin da yake nufi da wannan.

 

تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ الْمُبِينِ

2-Wadannan su ne ayoyin Littafin mabayyani.

 

نَتْلُوا عَلَيْكَ مِن نَّبَإِ مُوسَى وَفِرْعَوْنَ بِالْحَقِّ لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

3-Mune Karanta maka labarin Musa da Fir'auna na gaskiya don mutanen da suke ba da gaskiya

Bayan kawo karshen suratu Namili, a cikin wannan shiri za mu fara tafsirin Suratu Kasas wacce take da Aya 88 kuma an saukar da ita ne a garin Makka bayan hijrar Ma'aiki (s.a.w.a) daga Makka zuwa Madina. Kimanin Ayoyi 40 ne na cikin wannan surat da suke a matsayin rabin surar, na bayyani ne dangane da rayuwar Annabi Musa (a.s) kamar daga haifuwarsa, yarintarsa, har zuwa auransa sannan kuma zuwa ga samun sako ma'ana lokacin da aka tayar da shi a matsayin Ma'aiki.

Wannan surat kamar  surori 28 na Alkur'ani mai girma na farawa ne da harufan Mukada'a, kuma kai tsaye surat sai ta yi ishara zuwa ga Ayoyin Littafin da aka saukar daga sama, ko da yake dai kafin hakan dai, mun bayyana cewa, mai yiyuwa hakan na ishara ga wannan gaskiya na cewa Allah madaukakin sarki ya saukar da wadannan Ayoyi ne domin bayyana mu'ijizar Al'kur'ani mai girma, daga wadannan Harrufa da ya saukar da su ga Mutane, kuma kai ma idan kana iya kawo kamar wadannan harufa daga wani Littafi mai kama da wannan, da Ayoyinsa suka kasance a bayyane, mai rarrabe gaskiya daga karya, da kuma yake shiryarwa zuwa ga hanya madaidaiciya to sai ka kawo.

Ci gaban ayoyin suna bayyani kana bin ya faru tsakanin Annabi Musa (a.s) da fur'ana, Allah madaukakin sarki na cewa: Mu hakika a cikin wannan Alkur'ani, bisa tushen abinda ya faru da gaskiya, kuma nesa da duk wani abu na rashin gaskiya, ko kuma abinda bai faru ba, muke baku labarin Annabawa da kuma Mutanan da suka gabata, domin Muminai su san irin wahalhalu da matsalolin da Mutanan kirki masu Imani suka fuskanta a baya, kuma su sun nuna jimiri da juriya game da wadannan wahalhalu da matsaloli da suka fuskanta a zamaninsu.

Daga wadannan Ayoyi muna iya daukar darusa kamar haka:

1-Sanin sunnonin Ubangiji game da rayuwar mutanan da suka gabata, na iya zama darasi da kuma izna a gare mu da masu zuwa nan gaba.

2-Fada da Dagutu da Azzalimai, hanyar Annabawan Ubangiji ne kuma ya zama wajibi ga Muminai su ci gaba da bin wannan hanya.

3-Labarin Alkur'ani mai girma ya ginu ne a kan gaskiya, kuma Hasashe, tatsuniya, ko kuma wani lamari da bai wakana ba, ba shi da wuri a cikin Alkur'ani mai tsarki.

Yanzu za mu saurari Aya ta 4 cikin Suratu Kasas.

 

إِنَّ فِرْعَوْنَ عَلا فِي الأَرْضِ وَجَعَلَ أَهْلَهَا شِيَعًا يَسْتَضْعِفُ طَائِفَةً مِّنْهُمْ يُذَبِّحُ أَبْنَاءَهُمْ وَيَسْتَحْيِي نِسَاءهُمْ إِنَّهُ كَانَ مِنَ الْمُفْسِدِينَ

4-Hakika Fir'auna ya yi dagawa a bayan Kasa ya kuma sanya mutanenta kungiyoyi daban-dabn, yana bautar da wata kungiya daga cikinsu,yana yanke 'ya'yansu maza, yana kuma raya mata. Hakika shi ya kasance shi ya kasance cikin masu barna.

Wannan Aya na ishara ne game da son milki na Fur'ana tana mai cewa: domin kaskanta Bani Isra'ila da kuma ci gaba da milkarsu fir'auna na amfanin da hanyoyi daban-daban. Ya sanya sabani a tsakanin Al'umma kuma ya hana su, su hada kansu, duk kuma wanda  ya yunkura domin hada han Al'umma zai tunkare shi da Azzalimin milkinsa, a yau ma siyasar (sanya sabani, kuma ka yi milki) siyasa da manyan kasashen Duniya ke amfani da ita wajen mamaya da samun rinjaye a kan kasashe da Al'umma daban daban.

Abinda fur'ana yayi shi ne , 'yan asalin kasar Masar wato Kibdawa ya samar musu da ababen more rayuwa, kuma ya basu mikami daban daban na hukumarsa, a bangare guda Bani Isra'ila da Hijira ce suka yi zuwa kasar Masar sun kasance suna yiwa Kibdawa aiki a matsayin Bayi, duk wani aiki mai bakar wahala ya rataya ne a kansu, bas u da wani aiki face bauta ga Misrawa wato Kibdawa, ko baya ga haka basu amfana da ababen more rayuwa.

Fur'auna ya ji cewa Bani Isra'ila hatsari ne a gare shi ko kuma ga milkinsa, domin haka ne ya bayar da umarnin cewa duk Yaron da aka Haifa daga cikin Bani Isra'ila to a kashe shi, idan kuma Mace ce, to a gyaleta kuma idan ta girma ta kasance Baiwa mai hidima a gidan hukuma. Ta wannan hanya ce Fur'auna yake so ya shiga gaban karuwar matasan Bani Isra'ila ta yadda ba za su iya tashi a kan hukumarsa ba ko kuma su yi masa bori ba.a irin wannan yanayi ne aka haifi Annabi Musa (a.s), Ma'aifiyarsa, kare rayuwar sa ya tilasta masa sanya cikin akwati sannan kuma ta jefa shi cikin ruwa.

Daga wadannan Ayoyi muna iya daukar darusa kamar haka:

1-har zuwa lokacin da Al'umma suke kiyaye hadin kan su, to babu wata Hukuma ko Gwamnatin zalinci ta za ta iya samun rinyaye a gare su, domin haka,Azaliman mahukunta ke kokarin samar da rarrabuwa kai gami da sabani a tsakanin Al'umma.

2-kawar da ruhin mazaje tare da daukaka Mata a kan Maza a matsayin kare kyakkyawan hakkin Mata, Siyasa ce da a rayuwarmu ta yau ke gudana da salo mababbanta.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..