Oct 18, 2017 15:13 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 5-8 (Kashi na 696)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

---------------------------------------------------------

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au ne tare da sauraren karatun Aya ta 5 da ta 6 a cikin Suratu Kasasi

 

وَنُرِيدُ أَن نَّمُنَّ عَلَى الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا فِي الأَرْضِ وَنَجْعَلَهُمْ أَئِمَّةً وَنَجْعَلَهُمُ الْوَارِثِينَ

 

5-Muna kuma so Mu yi baiwa ga wadanda aka wulakanta a bayan kasa Mu kuma sanya su Shugabanni,kuma Mu mayar da su magadan (milkin fir'auna)

 

وَنُمَكِّنَ لَهُمْ فِي الأَرْضِ وَنُرِي فِرْعَوْنَ وَهَامَانَ وَجُنُودَهُمَا مِنْهُم مَّا كَانُوا يَحْذَرُونَ

 

6-Mu kuma kafa su a bayan kasar, kuma Mu nuna wa fir'auna da Hamana da rundunoninsu gaba dayansu abin da suke jin tsoro game da su (mutanen).

A shirin da ya gabata mun bayyana cewa an umarci Annabi Musa (a.s) da ya ji wajen fur'auna domin hana zalinci da ake yiwa Mutanan Bani Isra'ila, saboda Fur'auna ya riki wannan Mutane cikin kaskanci da bauta, yana kashe Mazajensu ya kuma sanya matayen aikin bauta ko kuma ya rike su a matsayin Bayi.wadannan Ayoyi na cewa, a tunanin Fur'auna zai zauna a kan kujerarsa ta milki har abada,duk abinda yake so, yana iya aikatawa, to saidai abinda bai sani ba,iradar Ubangiji ta kawar da wannan tunanin na sa,domin yayi alkawarin zai gaskantar da masu girman kai, sannan su kasance a karkashin hannun wadanda suke ganin su a matsayin makaskanta, su ne za su kasance masu iko, kuma su milke su.

Fur'auna da wazirinsa Haruna saboda tsoron boren Bani Isra'ila su kuma wargaza hukumar su, dukkanin aiki mai wahala na gaskanci suke sanya matasan Bani Isra'ila kuma duk wani matashi da aka gano ya nada akidar bore ko makaman haka, sai su kashe shi,to amma abinda Fir'auna da Fir'aunawa suke tsoro, sai da ya zo da yardar Ubangiji,Bani Isra'ila bisa jagorancin Annabi Musa (a.s) suka yi galaba a kansu tare da gadar tarin dukiyar da suka tara gami da manya manyan fadodi na milkin kasar.

Ko da yake Iradar Ubangiji ba haka take tabbata, ba tare da wani dalili ba, duk Al'ummar dake son 'yantuwa daga kangi na zalincin milki, to ya zama wajibi ta tashi, ta yi wani abu, ma'ana tayi ta juyawa hukumar baya, sai Allah ya taimako su ci nasara a kan Azzalimai, wannan ita ce sunnar Ubangiji a tsahon tarihi, da kuma hakan ya kasance makomar ko wata Al'umma dake fayyace hallayen su.duk Al'ummar da ba ta bukaci sauyi da kanta ba, to babu canji da za ta gani.

Bisa hadisan da aka ruwaito cikin litattafan musulinci, a karshen Zamani, Imam Mahdi (a.t.f) daga zuriyar Annabin (s.a.w.a) zai bayyana ya kuma ci nasara a kan masu girman kai da Azzalimai, ya kuma isar da milki ga masu karamin karfi bayan ya cika Duniya da Adalci.

Daga cikin wadannan Ayoyi za mu dauki Darasi kamar haka:

1-So da kuma iradar Ubangiji ne kawar da hukuncin masu girman kai da Azzalimai sannan kuma ya gadar da milkin ga masu karamin karfi.

2-Hukuncin Danniya da milkin Mallaka, makaminta shi ne amfani da raunin Al'umma da kuma dadin baki ta yadda za su samu damar yin rinjaye cikin sauki.

3-cin nasara da kuna galaba a nan gaba na masu karamin karfi da wadanda aka zalinta ne, wannan albishir ne da Ubangiji ya bayar, domin samun karfin gwiwa na kara juriya da kokari a kan gwagwarmayar na cimma fatan da ake da shi nan gaba.

4-Azzaliman makunta masu girman kai gami da Azzalimai, bayan azabar ubangiji ta Duniya, ba za su amintu da azabar ubangiji ba tun a nan Duniya, domin sai sun kaskanta a hanun Muminai.

Yanzu kuma za mu saurarin karatun Aya ta 7 da ta 8

 

وَأَوْحَيْنَا إِلَى أُمِّ مُوسَى أَنْ أَرْضِعِيهِ فَإِذَا خِفْتِ عَلَيْهِ فَأَلْقِيهِ فِي الْيَمِّ وَلا تَخَافِي وَلا تَحْزَنِي إِنَّا رَادُّوهُ إِلَيْكِ وَجَاعِلُوهُ مِنَ الْمُرْسَلِينَ
 

7-Muka kuma kimsa wa mahaifiyar Musa cewa:"Ki shayar da shi, to yayin da kika ji tsoro game da shi,sai ki jefa shi a cikin kogi, kada kuma ki ji tsoro, kuma kada ki yi bakin ciki, Hakika mu masu dawo muku da shi ne, kuma masu sanya shi ne cikin mazaunni.

 

فَالْتَقَطَهُ آلُ فِرْعَوْنَ لِيَكُونَ لَهُمْ عَدُوًّا وَحَزَنًا إِنَّ فِرْعَوْنَ وَهَامَانَ وَجُنُودَهُمَا كَانُوا خَاطِئِينَ
 

8-Sai mutanen fir'auna suka tsince shi don (daga baya) ya zama abokin gaba da kuma bakin ciki a gare su.Hakika Fir'auna da Hamana da rundunoninsu sun kasance a kan kuskure.

Wadaannan Ayoyi suna bayyani a kan aifuwar Annabi Musa (a.s)da kuma ababen da suka faru a lokacin, daya daga cikin misalan sunar Ubangiji na bawa masu karamin karfi nasara a kan masu girman kai, mun yi bayyani a Aoyoyin da su gabata, Bokaye da 'yan duba sun bawa Fir'auna labarin cewa za a haifi wani yaro a cikin zuriyar Bani Isra'ila  a wannan shekara, wanda a gaba zai rusa sarautarka, jin haka ya sanya fur'auna daukan mataki , inda ya bayar da umarnin cewa duk yaron da aka Haifa a cikin zuriyar Bani Isra'ila a kashe shi, kuma kadda a tausaya ko wata Mata ko iyali daga cikin su, a yayin da aka haifi Annabi Musa (a.s), sai Allah madaukakin sarki yayi wahayi na ilhami ga Ma'aifiyar Annabi Musa (a.s) na cewa ta shayar da shi Nono sannan kuma ta sanya shi cikin akwati ta jefa shi cikin gogin Nilu, Allah madaukakin sarki zai kare shi,Ma'aifiyar ta yi aiki da umarnin da aka yi mata ilhami, bayan ta shayar da shi Nono sai ta sanya shi cikin akwati ta jefa sa cikin Kogin Nilu, amma duk da hakan ta damu da makomar jaririnta.

A bangare guda, Fir'auna da Uwar gidansa na zaune a gabar mashigar gogin na Nilu kusa da Fadar Masarauta, sai suka wani Akwati na yawo a cikin ruwan gogin, sai Fir'auna ya bayar da umarni na a dauko masa Akwatin dake yawo cikin ruwa, yana buda Akwatin sai suka hada ido da wani Dan karamin jariri sabon haifuwa maid an kyawan gaske, bai san yadda zai yi ba, saboda a bangare guda ya bayar da umarnin a kashe duk wani jariri da aka Haifa, kuma a bayyane yake wannan jariri daga cikin zuriyar Bani Isra'ila ne, saboda a tsiratar da shi daga hallaka aka sanya shi cikin ruwa, a gefe guda kuma fir'auna bas hi da Da, Uwar gidansa Asiya na son wannan Jariri ta rike shi a matsayin Da.

Amma kuma, sama da wadannan ababe da muka bayyana shi ne Iradar Allah da ya gamsar da mahaifiyar Musa (a.s) na ta amince ta jefa Danta cikin Ruwa, kuma Uwar gidan Fir'auna ita ma aka sanya mata tsananin soyayyar Annabi Musa (a.s), da hakan ya kasance masa garkuwa na hallaka, domin haka Tarbiyar Annabi Musa (a.s) ta kasance a gidan makiyinsa Fir'auna, a amintaccen wuri da bas hi da wani hatsari, ta yadda a gaba  zai kawo da karshen hukumar zalinci ta Fur'auna.

A wadannan Ayoyi masu alabarka za mu iya daukan Darasi kamar haka:

1-A yayin da aka kai makura,Allah madaukakin sarki shi ne mai taimako, mai kuma shiryar da Muminai, Shi ne mai shiryar da Muminai hanyar mafuta daga matsala.

2-Saukar da taimakon Gaibi, ba ya karo da abinda abin za a kowa, kuma ya zama wajibi mu mayar da hankali da abinda aka bamu ko kuma abinda ke hanunmu, sannan mu yi aiki da abinda ya rataya kanmu, mu kuma yi tawakkali gami da dogaro ga Allah madaukakin sarki(kamar yadda Ma'aifiyar Annabi Musa (a.s) ta shayar da Dan ta, kuma ta saka shi a cikin Akwati ta jefa shi cikin ruwa, kuma ta dogara ga Allah madaukakin sarki)

3-Duk da cewa ba mu da masaniya a game ababe mai yawa na sanadiyar umarnin ubangiji, to amma a zartar da wannan umarni kadda muyi wasa, domin tabbas a cikin hukuncin Ubangiji a kwai wani sirri, domin babu wani hukunci Ubangiji da babu hikima cikin sa ba, (kamar umarnin Allah madaukakin sarki ga Ma'aifiyar Annabi Musa (a.s) na ta sanya Danta cikin Sanduki ta kuma jefa shi cikin ruwa) a kun ga ba da jimawa ba sirri da kuhincin dake cikin say a bayyana.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardar Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..