Suratul Qasas, Aya ta 9-13 (Kashi na 697)
Suratul Qasas, Aya ta 9-13 (Kashi na 697)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.
--------------------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 9.
وَقَالَتِ امْرَأَتُ فِرْعَوْنَ قُرَّتُ عَيْنٍ لِّي وَلَكَ لا تَقْتُلُوهُ عَسَى أَن يَنفَعَنَا أَوْ نَتَّخِذَهُ وَلَدًا وَهُمْ لا يَشْعُرُونَ
9-Muatar Fur'auna kuma ta ce:(Shi) kwanciyar rai ne a gare ni har da kai, kada ku kashe shi, muna fatan ya amfane mu, ko kumz mu dauke shi a matsayin da, alhali kuwa su ba su san (abin da zai faru ba).
A shirin da ya gabata,mun bayyana cewa Fir'auna da Uwan gidansa Asiya na zaune ne a gefen fadar masarauta dake mashigar Kogin Nilu, sai kawai suka ga wani Akwati yana yawo cikin ruwa, Fir'auna ya bayar da umarnin dauko sandukin nan daga cikin ruwa da aka bude shi, sai suka hada ido da wani kyakkyawan jariri, bisa umarnin da fir'auna ya bayar ya zama wajibi a kashe wannan jariri saboda jariri ne da ya fito daga zuriyar Bani-Israila, kuma jami'an tsaron fir'auna na kokarin zartar da wannan umarni sai Asiya matar Fir'auna dake zaune a kusa a Mijinta ta dakatar da su, tana mai cewa da wani dalili kuke son kashe shi, wannan Jariri ne kuma yana iya kasancewa sanadiyar kawo albarka da sanya farin ciki da walwala a fadar mu, kuma idanuwa sun kara haske da ganin wannan jariri, Mu da bamu da yaro, muna iya rike shi a matsayin Dan mu, mu girmar da shi a matsayin Dan mu, saboda nan gaba sai ya kasance wanda zai gaje ka a kan karagar milki.
Wannan bayyani da Asiya yayi tasiri a zuciyar Fir'auna, da hakan ya sanya shi canza ra'ayinsa na kashe wannan jariri, sannan ya bayar da umarni a shiga da wannan jariri cikin fada a kuma bashi kulawa ta musaman, a hakikanin gaskiya wannan ita ce Kaddarar Ubangiji, da ya kaddara Fur'auna shi da kansa ne zai bayar da kariya ga Annabi Musa (a.s) dake a matsayin makiyinsa da kuma ceto Bani-isra'ila daga kisan da ake yiwa 'ya'yansu duk kuwa da irin cece kucen da ake yi na wannan Kisa.
A cikin wannan Aya muna iya daukar Darasi kamar haka:
1-Mace na iya canza makomar Al'umma, Asiya Matar Fir'auna, hanin da ta yin a kashe Annabi Musa (a.s), ta ceto Bani-Isra'ila daga kangin Fir'auna, kuma ta canza tahirin wannan Al'umma.
2-Zukata na hanun Ubangiji ne, idan ya so yana iya canza Zukata masu tsanani zuwa masu tausayi da Rahama kamar yadda ya canza zuciyar fir'auna kekeshasshiya da har ma ta bayar da umarnin kisa da farko (kamar yadda ake kashe duk wani jaririn da aka Haifa daga cikin zuriyar Bani-isra'ila) ta koma sanyayyar Zuciya har ma ta amince da daukan yaunin wannan Jariri.
Yanzu kuma za mu saurari karatun Ayoyi na 10 da na 11 cikin Suratu Kasasi.
وَأَصْبَحَ فُؤَادُ أُمِّ مُوسَى فَارِغًا إِن كَادَتْ لَتُبْدِي بِهِ لَوْلا أَن رَّبَطْنَا عَلَى قَلْبِهَا لِتَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
10-Zuciyar ma'aifiyar Musa kuma ta wayi gari ba komai a cikinta (sai tunaninsa), ba shakka sauran kiris ta bayyana shi, ba don Mun sa dauriya zuciyarta ba don ta zama cikin muminai.
وَقَالَتْ لِأُخْتِهِ قُصِّيهِ فَبَصُرَتْ بِهِ عَن جُنُبٍ وَهُمْ لا يَشْعُرُونَ
11-Ta kuma ce da 'yar'uwarsa:"ki bi sawunsa",sai ta hango shi daga nesa, su kuwa bas u gane ita ('yar'uwarsa ba ce).
Bayan ma'aifiyar Annabi Musa (a.s) tas jefa Dan ta cikin Kogin Nilu, tsoro da fargaba ya mamaye zuciyarta, tayi ta dukan uku-uku, ta kasance kamar ta shiga cikin ruwan ta dauko Akwatin da ta sanya Dan ta a ciki,ta tseratar da jaririnta, to amma Ubangijin da yayi mata ilhami na ta sanya Dan ta cikin Akwati ta jefa sa cikin Ruwa, shi ne kuma ya sanya karfin gwiwa a zuciyar ta, domin cika alkawarinsa na dawo mata da Danta, domin ta samu Nutsuwa da konciyar hankali.domin haka, a maimakon ita ta je ta yi wani abu da zai sanya a gano ta, sai aka umarci 'yar uwar Annabi Musa (a.s) da ta bi Akwatin daga nesa har ta gano inda za ya isa,kuma mai zai faru da shi? Shin wani zai dauke shi daga cikin ruwa? Ko kuma zai ci gaba da hanyar da dauka?
'Yar uwar Annabi Musa (a.s) tayi aiki da umarnin da aka bada da kyau, domin ta sanya wa wannan Akwatin idanu daga nesa, yayin da jami'an tsaron Fadar Fir'auna suka dauki wannan Akwati ba su ganta ba, idan ba haka ba suna iya gano alakar dake tsakanin su da wannan Jariri, da ya sanya take bin wannan Akwati daga nesa.
A cikin wadannan Ayoyi, muna iya daukan Darasi kamar haka:
1-Rike sirri daya daga cikin halayen masu Imani ne, watsa sirri ko bayyana shi alama ce ta raunin Imani, musaman ma ga makiyan Addini, wadanda suke bibiyar sirrin Mayaka da Mujahidai da hakan zai basu damar cin galaba a gare su.
2-Nutsuwar zukata da samun konciyar hankali game da wata jarrabawa, na daga cikin tasirin Imani ga Allah da kuma alkawarinsa.
3-Dogaro ga Allah, ba ya nufin rungumar hannu ga zauna ba tare da ka aikata wani abu ba, Ma'aifiyar Annabi Musa, duk da cewa ta dogara ga Allah, amma ta tayar da Diyarta ta bi Akwatin da Danta ke ciki, domin ta gano inda zai tafi, ko kuma a hanun waye zai fada, a kwai wani Karin Magana na yaran Farisanci dake tabbatar da wannan Magana, shi ne Da dogaro da Allah ka daure kafar Rakumin ka.
Yanzu kuma za mu saurari karatun Ayoyi na 12 da na 13 cikin suratu Kasasi,
وَحَرَّمْنَا عَلَيْهِ الْمَرَاضِعَ مِن قَبْلُ فَقَالَتْ هَلْ أَدُلُّكُمْ عَلَى أَهْلِ بَيْتٍ يَكْفُلُونَهُ لَكُمْ وَهُمْ لَهُ نَاصِحُونَ
12-Da ma kuma can Mun haramta masa (nonon) masu shayarwa sai ('yar'uwar tasa) ta ce: 'Yanzu ba na nuna muku mutanen wani gida da za su shayar muku da shi ba, su kuma za su kyautata masa?
فَرَدَدْنَاهُ إِلَى أُمِّهِ كَيْ تَقَرَّ عَيْنُهَا وَلا تَحْزَنَ وَلِتَعْلَمَ أَنَّ وَعْدَ اللَّهِ حَقٌّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لا يَعْلَمُونَ
13-Sai muka dawo da shi wurin mahaifiyarsa don hankalinta ya kwanta kuma don kada ta yi bakin ciki don kuma ta son cewa alkawarin Allah gaskiya ne, sai dai kuma yawaicinsu bas a fahimtar (haka).
A dabi'ance, Jaririn da aka raba da ma'aifiyarsa na tsahon Sa'o'I, zai kasance cikin ishirwa da yunwa, wanda hakan zai sanya yayi ta kuka, Fur'auna ya bayar da umarni a samowa wannan jariri 'yar reno, amma da kudirin Ubangiji, Jaririn dake tsananin jin yinwa yana kuma kuka, ya ki amincewa da Maman ko wata 'yar reno, ya ki shan Nono,sai kuka yake, Ma'aikatan fir'auna sun kai makura, sun rasa yaya za su yi da wannan jariri.
A irin wannan yanayi, 'yar uwar Annabi Musa,ba tare da ta fadi wani abu da zai sanya jami'an Fir'auna su yi shakka da ita, sai ta fada musu cewa akwai wata Mata mai tausayi kuma tana iya renon wannan Jariri a gidanta, wato ta gabatar musu da ma'aifiyar Annabi Musa (a.s), ba tare da wata wata ba suka amince da wannan shawara, kai tsaye suka fice zuwa gidan Ma'aifiyar Annabi Musa (a.s) daga lokaci da ji hanun ma'aifiyarsa sai yayi shuru, su kuma, sai suka ji dadi, saboda sun cika umarnin da aka basu da kyau.
Daga cikin wadannan Ayoyi muna iya daukan Darusa kamar haka:
1-a gaban Makiyi ya kamata Mutun ya zamanto mai wayo, ba tare da an gano ta ba ta cika aikin da aka sanya ta kuma ta zartar da shirinta cikin sauki('Yar uwar Annabi Musa (a.s), ba tare da ta kira sunan ma'aifiyar ta ba, ta hanyar kwatamce ta gabatar da ita)
2-Mu yi amince kuma mu yi Imani da alkawarin Ubangiji madaukakin sarki na Duniya da Lahira, ayyukan Ubangiji kadda mu auna su da ma'aunin Duniya mai iyaka.
3-Da shi ne konciyar hankali da nutsuwa na Ma'aifiya, Ma'aifan da suka yi nisa da 'ya'yansu kuma suna tsamanin kamar ba su da 'ya'ya, hankalin su na tashi, a hakikanin gaskiya sun rasa dadin sabo da kuma zama da Yaransu.
******************************Musuc****************************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..