Oct 18, 2017 15:54 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 14-17 (Kashi na 698)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

----------------------------------------------/

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 14 cikin Suratu Kasas

 

وَلَمَّا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَاسْتَوَى آتَيْنَاهُ حُكْمًا وَعِلْمًا وَكَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ

 

14-Lokacin kuma ya kai karfinsa ya kuma kamala, sai Muka bas hi hukunci da ilimi, kamar haka kuwa Muke sake wa masu kyautatawa.

Wannan Aya,na ishara ne ga wani bangare na tarihin rayuwar Annabi Musa(a.s) tana mai cewa a yayin da Musa ya kai Matashi, Allah madaukakin sarki ya karfafa shi da karfin tunani,hankali da kuma ilhami na Ubangiji, ya bashi ilimi da Basira da zai iya gano gaskiya kuma zai iya rarrabewa tsakanin karya da gaskiya, ya kuma yi kyakkyawan alkalanci,abin fada a nan shi ne yayin da Annabi Musa (a.s) ya zama saurayi Allah ya arzuta shi da karfi da kuma jarumtaka sama da ko wani irin mutum dake rayuwa a lokacinsa, Tausayin Ubangiji ga Annabi Musa, saboda tsarkinsa, caccantar sa, ya sanya Allah tabaraka wa ta'ala ya arzuta shi da wannan, bisa dalili na wannan Aya, duk wanda ya kasance mai kyautatawa ne zai hadu da tausayin Ubangiji, amma ban Wahayi da kuma Anabta wanda daga bisani aka bawa Annabi Musa (a.s) da kuma daga karshe ya samu mikamin Ma'aiki.

Daga cikin wannan Aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Zamanin sarmutaka, zamani ne da ya fi kowane na rayuwar Mutum, saboda a wannan lokacin ne, karfin jiki da kuma cikar hanhali ke kasance ga mutum,har ya kasance kamilin mutum.

2-Kyautatawa ga Mutane da kuma aikata kyawawen ayyuka,  wasila ne na samun Litifin Ubangiji na musaman.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun Aya ta 15 cikin Suratu Kasas

 

وَدَخَلَ الْمَدِينَةَ عَلَى حِينِ غَفْلَةٍ مِّنْ أَهْلِهَا فَوَجَدَ فِيهَا رَجُلَيْنِ يَقْتَتِلانِ هَذَا مِن شِيعَتِهِ وَهَذَا مِنْ عَدُوِّهِ فَاسْتَغَاثَهُ الَّذِي مِن شِيعَتِهِ عَلَى الَّذِي مِنْ عَدُوِّهِ فَوَكَزَهُ مُوسَى فَقَضَى عَلَيْهِ قَالَ هَذَا مِنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ إِنَّهُ عَدُوٌّ مُّضِلٌّ مُّبِينٌ
 

15-Sai ya shiga cikin birnin a lokacin gafalar mutanensa, sai ya sami mutum biyu a cikinsa suna fada, wannan dan kabilarsa ne, wannan kuma abokin gabarsa ne, sai dan kabilar tasa ya nemi taimakonsa a kan abokin gabarsa, to saidai Musa ya dan zungure shi, sai kuwa ya kashe shi, (da ya ga haka sai) y ace:"wannan yana daga aikin shaidan, hakika shi kuwa makiyi ne bayyananne, mai batarwa.

Har zuwa lokacin sarmantakarsa, Annabi Musa (a.s) na rayuwa ne a fadar Fur'auna, ganin cewa shi ma daya ne daga cikin Mutanan fadar Fur'auna, an koyar da su dibarun yaki.wata rana ya fito daga cikin fada yana kewaya kafarsa a cikin titunan birnin Masar, sai ya hadu da wasu Mutane gida biyu suna fada har suna kokarin kashe kawunan su, daya daga cikin su daga cikin mutanan Bani Isra'ila ne, kuma kuma daga cikin kabilan Kibdawa ne 'yan asalin kasar Masar, Dan kabilar bani-isra'ilan, na daga cikin 'yan uwan Annabi Musa na jinni, ya gane Annabi Musa(a.s) sai ya nemi taimakonsa, ganin cewa Annabi Musa ya fahimci zalinci ne aka yiwa Dan uwan nasa, sai ya gaggauta zuwa taimakonsa, sai ya naushi abokin fadan nasa, shi kuma ya fadi kasa kuma ya mutu, Annabi Musa (a.s) bai yi tunanin cewa ba naushi daya sai yi sanadiyar mutuwar Mutum, saboda ba shi da niyar kashe mutum, yayi hakan ne domin kare mutuman da ake kokarin yiwa zalinci, duk da haka dai, Bakibden bai iya jurewa naushin Annabi Musa (a.s) ya fadi yam utu, a nan Musa ya fahimci musababin wannan tashin hankali da rikici, duk wanio rikici da rashin jituwa Shaidan ne yake sanyawa a tsakanin Mutane, a hakikanin gaskiya shi Shaidan makiyin Mutum ne, ta hanyar sanya rikici da tashin hankali a tsakanin Mutane ya kan kai ga kisa.

Daga cikin wannan Aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-Duk da cewa Musa ya girma a fadar Fir'auna, amma shi mai taimakon wadanda aka zalinta ne, ba azzalimai ba, kamar yadda Asiya Matar Fur'auna tana rayuwa a fadar Fur'auna, amma tayi Imani da Annabi Musa (a.s) kuma ta sadaukar da rayuwar ta a wannan hanya.

2-Annabawa Mutane masu jarimta, kuma masu tausayin wadanda aka zalinta, masu yaki da zalinci, saboda kariya ga wadanda aka zalinta, suna kalubalantar duk wani azzalimi.

3-Sanya fada da rikici a tsakanin mutane, aikin Shaidan ne, domin haka ya kamata mu zamanto masu hadiye fishi, kadda mu bari shaidan ya rinjaye mu.

Yanzu kuma za mu saurari Aya ta 16 da kuma ta 17.

 

قَالَ رَبِّ إِنِّي ظَلَمْتُ نَفْسِي فَاغْفِرْ لِي فَغَفَرَ لَهُ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ

 

16-Ya ce: "Ya Ubangijina, hakika ni na zalinci kaina, sai ka yi gafara, sai ko ya yi masa gafara, hakika Shi kuwa mai gafara ne mai jin kai.

 

قَالَ رَبِّ بِمَا أَنْعَمْتَ عَلَيَّ فَلَنْ أَكُونَ ظَهِيرًا لِّلْمُجْرِمِينَ

 

17-Ya (kuma) ce:"Ya Ubangijina, saboda ni'imar da ka yi min b azan zamo masu taimakon laifi ba."

Bayan mutuwar Bakibde,sananan abu ne  'yan uwansa Kibdawa za su bi sahun wanda ya kashe musu dan uwa domin su kama shi,su kuma hukunta shi,nushin da Musa ya yiwa Bakibden ya zalince sa, saboda hakan yayi sanadiyar mutuwarsa, su kuma 'yan uwansa Kibdawa na farauta Musa domin su hukunta shi, saboda haka ake ganin Musa a matsayin mai laifi.amma wannan abu ya sanya aikinsa nag aba ya kasance mai matsananciyar wahala, domin haka ne ma ya nemi gafarar Ubangiji idan ya aikata laifi ko kuma yayi kuskure a wajen nauyin da ya rataya kansa, zai Allah madaukakin sarki ya tseratar da shi daga sharrin Fir'auniyawa domin cikin hikimar sa yayi abin ya sanya Annabi Musa bai fada hanun Kibdawa ba.

Annabi Musa ya dauki alkawarin cewa idan Allah madaukakin sarki ya tseratar da shi daga fadewa hanun makiya, zai godewa lutufi da tausayin sa ta hanyar kin goyon bayan Mujrimai da kin kasancewa abokin Azzalimai har karshen rayuwarsa domin haka ne ma ya ki komawa fadar milkin Fur'auna ya yanke duk wata alaka dake tsakanin su.

Daga cikin wannan Aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-A yayin tseto muminai daga hannun Azzalimai, ya kamata ayi taka tsantsan, kuma a kiyaye fadawa cikin wani hadari.da zai sanya a hadu da mumunan sakamako da ba a yi zato ba.

2-Kurkure ko sabaninsa, ko da kuwa ba da gaggam aka yi ba, yana da tasiri a dabi'ance

3-Godiyarsa  ga Allah gwani, shi ne  taimakon wadanda aka zalinta, da kuma nisanta da aiki tare da azzalimai, da mujrimai.

*******************************Musuc**************************************

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..