Oct 18, 2017 16:14 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 18-21 (Kashi na 699)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

-------------------------------------------------

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 18 da kuma ta 19 cikin suratu Kasas

 

فَأَصْبَحَ فِي الْمَدِينَةِ خَائِفًا يَتَرَقَّبُ فَإِذَا الَّذِي اسْتَنصَرَهُ بِالأَمْسِ يَسْتَصْرِخُهُ قَالَ لَهُ مُوسَى إِنَّكَ لَغَوِيٌّ مُّبِينٌ

 

18-Sai ya wayi gari a cikin birnin a tsorace yana dar-dar,sai ga wanda ya nemi taimakon nan nasa a jiya yana sake neman taimakonsa, (sai) Musa ya ce da shi:"hakika kai dai batacce ne sosai.

 

فَلَمَّا أَنْ أَرَادَ أَن يَبْطِشَ بِالَّذِي هُوَ عَدُوٌّ لَّهُمَا قَالَ يَا مُوسَى أَتُرِيدُ أَن تَقْتُلَنِي كَمَا قَتَلْتَ نَفْسًا بِالأَمْسِ إِن تُرِيدُ إِلاَّ أَن تَكُونَ جَبَّارًا فِي الأَرْضِ وَمَا تُرِيدُ أَن تَكُونَ مِنَ الْمُصْلِحِينَ

19-To lokacin da ya nufi wawurar abokin gabar tasu (sai mai neman taimakon ) y ace:"Ya Musa shin yanzu nufi kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe wani rai a jiya? Ba a binda kake nufi sai ka zama mai tsaurin rai a bayan kasa,b aka kuma nufin ka zama cikin masu kyautatawa.

A shirin da ya gabata mun bayyana cewa a zamanin da ya kai matashi Annabi Musa (a.s) ya fito daga cikin fadar Fur'auna zuwa tsakanin Al'ummar Gari, a wannan lokaci Bani Isra'ila sun kasance cikin kangin zlinci na Fur'auniyawa da Kibdawa.a yayin da yake rawaya kafa a cikin gari, sai ya hadu da wani Bakibde yana kokarin kashe wani mutum daga cikin Bani Isra'ila, sai Mutuman ya bukaci taimakon Annabi Musa (a.s), inda Shi kuma Musa ya gaggauta kai masu taimako ya naushi Bakibden, ba a da son bas hi kuma ya mutu.

Wannan Aya na nuni da cewa, bayan aukuwar wannan lamari, Annabi Musa(a.s) bai koma ba fadar Fur'auna, kuma ya boye a cikin garin, domin tsoron shiga hanun jami'an tsaron Fur'auna, a rana ta biyu sai ya sake ganin wannan mutum daga Bani-isr'ila yana fada da wani Bakibde, sai ya bukaci taimakon Musa (a.s), sai Annabi Musa (a.s) ya ce masa me ya sanya kake fada da kibdawa kana jefa rayukarka cikin hadari, abinda kake yi, ba wai kawai ba shi da amfani ba, z aka janyowa Bani isra'ila matsala. Amma duk da hakan shi mazlumi ne wato an zalince sa kuma ya fada cikin kangin zalinci, domin haka Annabi Musa (a.s) ya gaggauta zuwa taimakonsa, amma a wannan karo, a maimakon bugo, ya shiga gaban Bakibden domin hana shi bugun Ba'isra'ilan.

Daga cikin wannan Aya za mu ilmantu da ababe uku kamar haka:

1-A yayin Yaki da makiyi, bai kamata a shiga filin dag aba tare da shiri ba,a maimakon a samu sakamako, sai ka janyo kanka da wusunka matsala.

2-idan 'yan uwa da abokanni sun yi laifi ko kuskure, to ya kamata a yi musu fada kuma a kwantata musu abinda suke yi ba daidai ba ne, to amma duk da hakan bai dace abar su su kadai a hanun Azzalimai ba.

3-A gaban Makiya, kamata Mutum ya tsaya da karfinsa, ya kuma kalubance su da dukkanin iyawarsa.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari Aya ta 20 da ta 21 cikin suratu Kasas.

 

وَجَاءَ رَجُلٌ مِّنْ أَقْصَى الْمَدِينَةِ يَسْعَى قَالَ يَا مُوسَى إِنَّ الْمَلَأَ يَأْتَمِرُونَ بِكَ لِيَقْتُلُوكَ فَاخْرُجْ إِنِّي لَكَ مِنَ النَّاصِحِينَ
 

 

20-Sai wani mutum (mumini daga mutanen fur'auna) ya zo daga kuryar birnin yana gaggawa, ya ce:"Ya Musa, hakika manyan gari(suna can) suna shawara game da kai don su kashe ka, to ka fita (daga birnin) Hakika ni ina cikin masu yi maka nasiha

 

فَخَرَجَ مِنْهَا خَائِفًا يَتَرَقَّبُ قَالَ رَبِّ نَجِّنِي مِنَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ

 

21-Sai ya fita daga cikin sa (watau birnin) a tsorace yana ta dar-dar, ya ce:" Ya Ubangijina, ka tseratar da ni daga Azzaliman mutanan nan".

Abinda ya faru a cikin gari, labarinsa ya isa zuwa ga kunan Fir'auna:fada tsakanin wani mutum daga cikin Bani Isra'ila da ya kasance Bawa ne, da Mutane biyu Kibdawa, cikin kwanaki biyu a jere, kuma a yayin fadar Musa ya taimakawa Bawan daga cikin Bani isra'ila, har ta kai yayi nasara a kan Bakibden.

Wannan labarin bai yiwa Fadawan Fir'auna dadi ba, har ma sun kasa nuna juriya a kan hakan,domin hakan suka kada kuri'ar amincewa da Kashe Annabi Musa (a.s) domin ya zamanto izina ga Bani'isla'ila, ko da gobe wani daga cikin zai iya daga kai a gaban Bakibde.

Kafin jami'an tsaro su fara aikinsu, wani daga cikin makusantar Fur'auna ya samu wannan labari, ba tare da bata lokaci bay a shiga cikin gari, ya bawa Annabi Musa (a.s) labarin matakin da aka dauka a kansa, sannan ya ce masa  ya zama wajibi ka fice daga cikin garin nan domin ka tsira da rayuwarka. Kamar yadda aka ruwaito cikin hadisai an bayyana cewa sunan wannan Mutum (Hazkilu), bayan da Musa ya zamanto Annabi yayi Imani da shi, kuma ya shahara da wannan Suna Muminin Ali-Fir'aun,duk da cewa yana rayuwa a cikin fadar Fir'auna shi ma kamar Mata Fir'auna, ba su amince da tsarin Fur'aunanci ba, sun kasance masu jiran wandanda za su yi bore a kan wannan hukunci na zalinci, a yayin da ya fahimci mu'amalar Musa zai ya fahimci cewa wannan mutum ya nada shiri da kuma karfin da ya dace na yiwa Fir'auna bore, domin kare ran Musa ya shigo gari domin ya tsirarar da shi daga hadari.

Duk da hakan dai Musa bai dauki labarin wannan Mutum da wasa ba, a nan take ya kudiri fita daga cikin garin, kuma a yayin da yake ficewa daga cikin garin yana kula da kansa kuma yana takatsantsan, domin a ko wani lokacin yana jiran wani abu ya faru da shi, domin haka ya bukaci taimakon Ubangiji nay a fita daga cikin Gari cikin lafiya, ya kuma tsira daga kangin Azzalimai.

Daga cikin wannan Aya za mu ilmantu da ababe hudu kamar haka:

1-An haramta taimakon Azzalimai, amma shiga cikin Azzalimai da kuma samun wuri a cikin su da nufin taimakawa raunana, marasa kalihu, da wadanda aka zalinta, tare kuma da shiga gaban zalinci, abu ne mai kyau.

2-Idan muka yi aiki don Allah, a yayin hadari, Allah zai taimake mu ya kuma kare mu.

3-bayar da labara da sauki a kuma lokacin da ya dace na iya sauya makomar Al'umma, misali, idan wannan Mutum da ya kasance mabiyin Musa ne bai isar da labarin da wuri ba, kuma Annabi Musa bai fice daga cikin garin ba da ya fada hanun  jami'an tsaron Fir'auna kuma sun kashe shi.

4-A tsakanin wadanda suke rayuwa a gidan milki, akwai yiyuwar a samu Mutane masu neman gaskiya, kuma daga cikin mazauna unguwar matalauta, akwai yiyuwar samun mutane masu goyon bayan karya da yaudara, amma duk da haka, ma'aunin shi ne gaskiya da karya, ba wai wurin zama ba, ko wurin rayuwa.

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..