Suratul Qasas, Aya ta 22-25 (Kashi na 700)
Suratul Qasas, Aya ta 22-25 (Kashi na 700)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
-----------------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 22 da kuma ta 23 cikin suratu Kasas
وَلَمَّا تَوَجَّهَ تِلْقَاء مَدْيَنَ قَالَ عَسَى رَبِّي أَن يَهْدِيَنِي سَوَاء السَّبِيلِ
22-Yayin da kuma ya fuskanta wajen (birnin) Madayana, sai ya ce:"ina fatan Ubangijina Ya shiryar da ni, hanyar da ta fi dacewa".
وَلَمَّا وَرَدَ مَاء مَدْيَنَ وَجَدَ عَلَيْهِ أُمَّةً مِّنَ النَّاسِ يَسْقُونَ وَوَجَدَ مِن دُونِهِمُ امْرَأتَيْنِ تَذُودَانِ قَالَ مَا خَطْبُكُمَا قَالَتَا لا نَسْقِي حَتَّى يُصْدِرَ الرِّعَاء وَأَبُونَا شَيْخٌ كَبِيرٌ
23-Lokacin da kuma ya gangara wajen ruwan (rijiyar)Madayana sai ya samu wasu mutane masu yawa suna shayar (da dabbobinsu), sai ya ce (da su) Me ya same ku ne? sai suka ce: Mu ai ba ma shayarwa har sai duk makiyayen sun juya,kuma ma'aifinmu tsoho ne tukub.
A shirin da ya gabata, daya daga cikin mazauna fadar Fur'auna ya sanar da Annabi Musa (a.s) dangane da kudirin da fada ta dauka na aiwatar da kisa a gare shi, inda ya bukaci ya gaggauta fita daga cikin garin Masar, wadannan Ayoyi masu albarka sun bayyana cewa Annabi Musa (a.s) ya kudirin ficewa daga garin Masar da ya kasance karkashin milkin Fir'auna, inda ya nufin birnin Madayyana dake kudancin Sham wanda yake bay a karkashin milkin Fir'auna.
Amma wannan bulaguro yana tattare da hatsari, a bangare guda, akwai yiyuwar bada daga kan hanyar, a bangare guda kuma ga yadda aka baza jami'an tsaron Fir'auna domin neman Annabi Musa (a.s), domin haka ne ma Musa ya bukaci taimakon Allah madaukakin sarki da ya shiryar da shi zuwa hanyar ta kwarai.
Ci gaban Ayar na cewa, kafin shiga garin madayyana, Annabi Musa (a.s) ya hadu da wasu makiyaya a kusa da wata rijiya suna ban ruwa,sanannan abu ne Annabi Musa (a.s) ya kasance cikin gajiya domin ya sha wahalar hanya, ya nufi rijiya domin ya samu ruwan da zai sha, sannan kuma ya karkade kurar dake jikinsa domin shiga cikin gari, to saidai a kusa da rijiyar ya hadu da wani abin ban al'ajabi, wanda hakan ya ja hankalinsa, ya ga wasu 'yan Mata guda guda biyu suma kamar sauran makiyayan, sun so da dabbobin su domin shayar da su ruwa, to amma sun tsaya a gefe guda, suna tsare da dabbobinsu domin kadda su hade da dabbobin Mutane, Annabi Musa (a.s) yayi mamaki da ganin hakan, domin ya kasa gane dalilin da ya sanya suka rabe a kusa da rijiyar da kuma yadda suka rabe da makiyaya mazan, sai tambaye su kan dalilin sun a yin hakan, su kuma sai suka amsa masa da cewa Ma'aifinmu tsofo ne wanda hakan ya tilasta mana yin kiyo mu kuma shayar da dabbobin mu ruwa, amma saboda ba ma so mu tsudu da Maza,muka rabe har su gama shayar da dabbobin su, su fice, idan sun fice mu kuma sai mu isa bakin rijiyar , ruwan da yayi saura mu shayar da dabbobinmu.
A cikin wadannan Ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:
1-Shirin Hijra daga gari da mazauna mutum, na daga cikin shirye-shiryen mutanan kirki masu kawo gyara a cikin al'umma, domin fuskantar wahalhalu da matsalolin ababen dake cikin sa da kuma mai zuwa a gaba.
2-Addu'a, bayan da mutum ya fara wani aiki, abu ne mai ma'ana, ba kawai ba, Mutum ya zauna ba tare da ya kaddamar da wani abu, y ace zai yi Addu'a, wannan abu ne da bas hi da wata ma'ana.
3-kiyaye tsuduwa tsakanin Maza da Mata a wurin aiki, ko kuma a wani wuri, abu ne mai mahimanci, (kamar yadda 'ya'yan Annabi Shu'aibu (a.s) suka nisantar da dabbobin su daga bakin rijiya da kuma shayar da su ruwa domin kiyaye tsuduwa da Maza).
4-idan ya kama, 'ya'yan Annabawa Mata suna iya yin kiwo, amma har abada ba za su meka hannayansu domin neman sadaka ba.
Yanzu kuma za su saurari karantu aya ta 24 da kuma ta 25 cikin suratu Kasas
فَسَقَى لَهُمَا ثُمَّ تَوَلَّى إِلَى الظِّلِّ فَقَالَ رَبِّ إِنِّي لِمَا أَنزَلْتَ إِلَيَّ مِنْ خَيْرٍ فَقِيرٌ
24-To sai ya shayar musu (da dabobbobin nasu) sannan ya koma wurin wata inuwa ya ce:"Ya Ubangijina, Hakika ni mabukacin wani alherin da za ka saukar mini ne"
فَجَاءَتْهُ إِحْدَاهُمَا تَمْشِي عَلَى اسْتِحْيَاء قَالَتْ إِنَّ أَبِي يَدْعُوكَ لِيَجْزِيَكَ أَجْرَ مَا سَقَيْتَ لَنَا فَلَمَّا جَاءَهُ وَقَصَّ عَلَيْهِ الْقَصَصَ قَالَ لا تَخَفْ نَجَوْتَ مِنَ الْقَوْمِ الظَّالِمِينَ
25-To sai dayansu ta zo masa tana tahiya cikin jin kunya ta ce:Babana yana kiran ka don ya saka maka ladan shayarwar da ka yi mana."To lokacin da ya zo wurinsa ya kuma bashi labarin (abubuwan da suka faru), sai ya ce da shi:"kada ka ji tsoro, ka tsira daga azzaliman mutane.
Annabi Musa (a.s) da ya kasance ya bar garin Masar saboda tsoron fur'auna , ya isa garin Madayyana cikin gajiya, a halin da ake ciki, ya manta da matsalolinsa, sai ya shagaltu da janyo ruwa daga rijiya domin taimakawa wadannan 'yan Mata guda biyu su shayar da dabbobin su ruwa, bayan ya kamala aiki, ba tare da ya bukacin ladan aikinsa ba, sai ya nufi karkashin itaciya, domin ya huta, to saidai yunwa ta tilasta masa zuwa neman abinci, ganin cewa Annabi Musa (a.s) bako a cikin wannan gari kuma bai san kowa ba, ba rantana ma ya sauka a gidan sa kuma ya ci abinci, sai ya bukaci Ubangiji da ya taimaka masa kan abinda yake ganin ya dace da shi domin ya kawar da matsalarsa ta yunwa da masauki.
A bangare guda kuma ga 'ya'yan Annabi Shu'aibu sun isa gidan su cikin sauri fiye da sauran kwanaki, sai Ma'aifinsu ya tambaye su, shin ba ku shayar da dabbobin ba kuka dawo gida da wuri haka? Sai 'ya'yan Annabi Shu'aibu suka sanar da shi abinda ya faru da su a wurin shayar da dabbi ruwa, da kuma irin taimakon da Annabi Musa (a.s) ya yi musu, daga jin haka, sai Annabi Shu'aibu (a.s) ya bukaci 'ya'yan nasa da su koma su kira Musa domin ya saka masa kan taimakon da yayiwa 'ya'yansa ya kuma gode masa.
Daya daga 'yan Mata cikin kunya sai ta je wajen Annabi Musa tace masa ma'aifinmu yana kiran ka domin ya saka maka aikin da kayi mana, yanayin da wannan Mata ke Magana, sai Annabi Musa (a.s) ya fahimci cewa ta fito ne daga gidan tarbiya da karamci kuma ma'aifinsu babban mutum ne da bai kamata ya ki amsa kiransa ba, domin haka ya amince ya kuma amsa kiran, sannan ya bi wannan 'yan Mata zuwa gidansu, a yayin da isa gidan Annabi Shu'aibu (a.s) sai ya sanar da shi halin da yake ciki, daga ina ya fito kuma mine ne abinda ya fitar da shi daga garin Masar har zuwa garin Madayyana.sai Annabi Shu'aibu (a.s) ya fada masa cewa ka tsira daga Azzalimai, kuma kana iya zama a nan iya lokacin da kake so.
A cikin wadannan Ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:
1-A yayin da kake cikin matsala, kadda ka manta da matsalar mutane, kuma iya naka kokari domin magance matsalar waninka.
2-Mu nemi taimakon Ubangiji wajen magance matsalolinmu da bukatunmu, domin ya shiryar da mu zuwa hanyar da take maslaha a gare mu.
3-A makarantar Annabawa, babu laifi mace ta kasance a cikin Al'umma, da sharadin cewa ta kiyaye mutuncinta, da kuma tsuduwa da Maza.
4-Mu mutunta Hidimar da wasunmu suka yi masa,kuma mu saka musu ta hanyar da ya dace.
*************************************Musuc***********************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..