Suratul Qasas, Aya ta 26-28 (Kashi na 701)
Suratul Qasas, Aya ta 26-28 (Kashi na 701)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
----------------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 26 cikin suratu Kasas.
قَالَتْ إِحْدَاهُمَا يَا أَبَتِ اسْتَأْجِرْهُ إِنَّ خَيْرَ مَنِ اسْتَأْجَرْتَ الْقَوِيُّ الأَمِينُ
26-Sai dayarsu ta ce:"Babana, ka dauke shi aiki mana, don kuwa hakika ba wanda ya fi dacewa a dauke shi aiki sai kakkarfa amintacce.
A shirin da ya gabata, mun bayyana cewa Annabi Musa (a.s) ya taimakawa 'yan Matan Annabi Shu'aibu (a.s) inda ya janyo musu ruwa daga cikin rijiya suka kuma shayar da dabbobinsu, bayan sun tafi gida ma'aifinsu ya bukace su da su kira Annabi Musa (a.s) ya kuma saka masa kan taimakon da yayiwa 'ya'yansa, bayan ya amsar kiran Annabi Shu'aibu, ya sanar da shi dukkanin halin da yake ciki, kama daga abinda yayi a garin Masar har zuwansa birnin Madayya, Annabi Shu'aibu (a.s) ya fada masa cewa ya tisa daga hannun Azzalimai sannan kuma ya bashi zabi a kan cewa yana iya zama a tare da shi iya lokacin da yake so.
Wannan Aya na cewa Diyar Annabi Shu'aibu wacce ta kira Annabi Musa ta shawarci ma'aifinta da dauke a matsayin wadanda zai yi musu kiwo ta yadda za su 'yan Matan za su huta da zuwa kiwo ko wata rana.
Wajen gabatar da wannan shawara ta fadi wasu siffofi da shi Musa yake da su: na farko shi ne karfin jiki, na biyu kuma rikon amana, karfin Musa ya bayyana ne a yayin da shi kadai ya janyo ruwan da babbar guga wacce ta shayar da dukkanin dabbobin Annabi Shu'aibu. Tsarki, gaskiya da kuma rikon amanar sa ya bayyana ne a hanyarsa ta zuwa gidan Annabi Shu'aibu, a maimakon ita diyar ta Annabi Shu'aibu (a.s) ta shiga gaba domin ta gwadawa Annabi Musa gidansu, sai ya bukaci shi ya shiga gaba ita kuma ta tsaya a bayansa, daga bayansa ta fada masa hanyar da zai bi har su isa gidan, saboda kadda idanunsa su fada kallon wannan matashiyar mata.
A cikin wannan Aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-'ya'yanmu maza ne ko mata, su nada 'yancin gabatar da shawara kan abinda suke ga ya dace tare da bayyana dalilai na hanakali, kuma hakan babu babbanci a tsakanin maza da mata.
2-domin daukan aiki, ya kamata a dauki mutanan da suka dace da aiki, kuma a zabi na kwarai daga cikin su.
3-karfi da rikon amana, ko kuma mu ce gwaninta da kuma rikon alkawari, abu biyu da ya dace ayi la'akari da su wajen bayar da aiki, ko shugabanci.
Yanzu kuma zamu saurari karatun aya ta 27 da ta 28 cikin suratu Kasasi
قَالَ إِنِّي أُرِيدُ أَنْ أُنكِحَكَ إِحْدَى ابْنَتَيَّ هَاتَيْنِ عَلَى أَن تَأْجُرَنِي ثَمَانِيَ حِجَجٍ فَإِنْ أَتْمَمْتَ عَشْرًا فَمِنْ عِندِكَ وَمَا أُرِيدُ أَنْ أَشُقَّ عَلَيْكَ سَتَجِدُنِي إِن شَاء اللَّهُ مِنَ الصَّالِحِينَ
27-Sai ya ce da (Musa): ina so in aura maka daya daga 'ya'yayen nan nawa guda biyu, a kan ka yi min aiki na shekara takwas, sannan idan ka cika goma, to wannan dadinka ne, ban a kuwa nufin in kuntata maka, za ka same ni kuwa in Allah ya yarda daga masu cika alkawari.
قَالَ ذَلِكَ بَيْنِي وَبَيْنَكَ أَيَّمَا الأَجَلَيْنِ قَضَيْتُ فَلا عُدْوَانَ عَلَيَّ وَاللَّهُ عَلَى مَا نَقُولُ وَكِيلٌ
28-(Musa) ya ce:"Wannan tsakanina da kai ne, duk dayan lokatan biyu da na cika babu kwaruwa a gare ni, Allah kuwa shaida ne game da abin da muke fada.
Annabi Shu'aibu (a.s) ya amince da shawarar da Diyarsa ta gabatar masa na daukan Annabi Musa (a.s) aikin kiwo, amma ba zai iya amincewa da wani Matashi maras aure ya zauna a gidansa, alhali shi kuma ya nada 'yan Mata guda biyu a cikin gidansa, domin hakan ya shawarci Annabi Musa (a.s) da ya auri daya daga cikin 'ya'yansa wanda hakan zai bashi damar zama da kuma rayuwa tare da su a cikin gida guda, ganin cewa ba ya so ya dawwama a aikin kiwo, Annabi Musa ya kula yarjejjeniya da Annabi Shu'aibu (a.s) bayan aure, zai kasance tare da su akalla shekaru takwas, yana kiwo daga bisani kuma ya dauki matarsa ya fice, saboda Annabi Shu'aibu ba ya so Annabi Musa (a.s) bayan daurin aure ya dauki matarsa ya fice ya rabu da zuriyarsa, saboda idan hakan ya kasance, bayan bai taimaka musu ba, kuma ya rage musu mutum guda da yake taimaka musu a aikin kiwo, domin matar ta annabi Musa ta kasance tana taimakawa 'yan uwarta wajen kiwo dabbobin su.
Domin haka, Annabi Shu'aibu (a.s) ya sanya sharadin auren, kiwo na shekaru takwas da hakan zai amfani bangarorin biyu.a bangare guda matsalar gida, Mace, rayuwa na Annabi Musa an magance ta, a bangare guda kuma, a maimakon 'ya'yan annabi Shu'aibu su dinga shiga cikin daji da babu tsaro cikin sa domin kiwon dabbobin su , yanzu za su zauna a cikin gidajensu, kusa da iyayensu.
Abin lura a nan shi ne, shekaru takwas na aikin kiwo ga annabi musa, ko ya kasance sadakin diyar Annabin Shu'aibu ne ko kuma ya kasance sharadin daurin auren ne,shawarar matar musa ne domin amfaninsa na komawa ne zuwa gare ta ba zuwa ga ma'aifinta ba, saboda a lokacin da diya mace ya zame mata wajibi ta tafi kiwo saboda tsufan ma'aifinta, ko wata rana sai ta shiga cikin Daji domin kiyon dabbobi, fatan ta samu matashi mai klarfi kuma mai tsarki da rikon amana ya aure ta, ya karbi kuma wannan shugabanci, domin ta huta da wannan aiki mai matukar wahala.
A yayin gabatar da wannan shawara ga Annabi Musa, annabi Shu'aibu ya tabbatar da cewa ba ma so mu tilasta maka a kan komai, idan ka nada Magana ka fadi ra'ayinka mu ji,duk da wannan sharadi da aka gindayawa annabi musa (a.s) ya amince da wannan aure, inda ya ce zan kasance shekaru takwas a tare da ku ina yi muku kiwo,kuma zai aiwatar tare da cika sharadin da na dauka, idan kuma ina so in kasance a tare da ku sama da shekaru takwas da Karin shekaru biyu wato shekaru goma, zan ci gaba da yi muku kiwo ta yadda za mu samu abincin da za mu rayu da shi, ku kuma mu ci gaba da yi muku hidima.
A cikin wadannan Ayoyi za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-idan saurayi ya kasance mai tsarki ne, mai gaskiya kuma amintacce ne, ma'aifi ko kuma dangi su gabatar masa da shawar auran diyarsu babu laifi.
2-Domin amincin al'umma, aure shi ne gaba da aiki.
3-wajen sanya sadaki ga matar da take son yin aure, ta yi la'akari da karfi wanda zai aure ta kadda aka sanya masa sadakin da ya fi karfinsa ya kuma sanya shi cikin takura.
**************************************Musuc**************************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..