Oct 18, 2017 19:08 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 29-32 (Kashi na 702)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

-----------------------------------------

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 29 cikin suratu Kasas.

 

فَلَمَّا قَضَى مُوسَى الأَجَلَ وَسَارَ بِأَهْلِهِ آنَسَ مِن جَانِبِ الطُّورِ نَارًا قَالَ لِأَهْلِهِ امْكُثُوا إِنِّي آنَسْتُ نَارًا لَّعَلِّي آتِيكُم مِّنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ جَذْوَةٍ مِنَ النَّارِ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ
 

29-To yayin da Musa ya cika lokacinsa ya kuma tafi da iyalansa, sai ya hango wuta daga gefen (dutsen) Duri, ya ce da iyalansa: ku zauna(a nan), hakika na hango wuta,(zan je don) in zo muku da labari daga wurinta ko kuma wani garwashi na wutar don jin dimi.

A shirin da ya gabata mun bayyanacewa Annabi Musa ya auri diyar Annabi shu'aibu, kuma ya amince da sharadin da aka gindaya masa na cewa akalla zai yi kiwo na shekara takwas, kuma idan yana so ya ci gaba da hidima na shekaru biyu to wannan zabi ya rage a gare shi, wannan Aya na bayyana cewa, alkawarin da musa ya dauka ya cika shi, bayan kwashe shekaru goma yana kiwo, annabi musa ya kama hanun matarsa da 'ya'yansa domin komawa zuwa ga ma'aifarsa wato garin masar,amma hanyar na da nisa da hatsari, a yayin da suka isa kasar Sham, dare ya shiga suka kuma bace daga hanyarsu, inda suka dauki wata doguwar hanyar har ta kaisu da sai sun tambaya, suna cikin tafiya sai Annabi Musa (a.s) ya tsinakayo hasken wuta na tashi a kusa da wani babban Dutse, da ganin hakan, sai Annabi Musa ya ce wanda ya hura waccan wuta hakika ya sanya hanyoyin wadannan gariruwan, kuma yana isa sanya mu a hanya.

Ko baya ga hakan muna iya samo garwashi daga wajen sa domin a rura wuta muji dumi saboda yanayi na sanhi da aka yi a cikin wannan daji.

A cikin wannan Aya muna iya ilmantuwa da ababe guda uku kamar haka:

1-Namiji shi ne yaunin bukatun matarsa da iyalinsa suka rataya a kansa, kuma ya kamata iyalai su kasance tare da namiji wajen magance matsalar rayuwarsu.

2- Soyayyar gari ko ma'aifar mutum, dabi'ar mutum ne, ku kowa ya nada hakkin komawa ma'aifarsa ko bayan shekaru da dama

3-Musa da ya kasance shekara da shekaru yana rayuwa a cikin fadar fir'auna, yayi shekaru goma yana yawo cikin daji domin kiwo,domin haka duk wani dadi da kake ji to ka shiryawa matsala da wahala a gaba.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari Aya ta 30 cikin suratu Kasasi.

 

فَلَمَّا أَتَاهَا نُودِي مِن شَاطِئِ الْوَادِي الأَيْمَنِ فِي الْبُقْعَةِ الْمُبَارَكَةِ مِنَ الشَّجَرَةِ أَن يَا مُوسَى إِنِّي أَنَا اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ
 

 

30-To lokacin da ya zo wurinta (wutar) sai aka yi kira daga gefen kwari na damarsa a wani wuri mai albarka na bishiya, cewa:"Ya Musa, Hakika Ni ne Allah Ubangijin Taliakai!.

Hadisai sun bayyana cewa a yayin da Musa ya kusanci wutar, sai ya fahimci cewa wannan wuta da wutar da ya saba gani sun sha babbam, wuta na tashi a tsakanin itaciyar tsanwa shar, ba bushashiyar itaciya ba, wuta na tashi abin da ban mamaki, saboda haske kawai ke tashi babu hayaki, babu zafi.

Musa sai ya fada ciki tunani, yana tunani, ba tsammani kawi sai ya ji kira an ce Ya kai Musa! Wanda ya zo da kai nan, ni ne, nine mahalicci da kuma wanda zabinka da dukkanin halittu ke hanunsa.

A hakikanin gaskiya, Allah madaukakin sarki ya samar da wannan Magana ce da ta hanyarta ce yayi Magana da Musa. Wannan magana da Allah madaukakin sarki sarki ya hallita yayi zance da Annabi Musa (a.s) da ita, ita ta babbanta Musa da sauran Annabawa har ma ya samu wannan lakabi na Kalimullahi.

A cikin wannan Aya muna iya ilamtuwa da abubuwa guda biyu kamar haka:

1-A cikin al'adar Addini, wuraren da aka jinkina su da Ubangiji, wurare ne masu tsarki, ko da kuwa Duwatsu ne ko Daji.

2-Domin kawowa iyalansa wuta da kuma neman hanya, Musa (a.s) ya tafi Dutsen Tur, to amma Allah madaukakin sarki a can ya dora masa yaunin shiryar da Al'umma, ma'ana abin da ya rata kanmu, tashi da kokari, amma sakamako ba a hanunmu yake ba.

Yanzu kuma lokaci yayi da zamu saurare karatun Ayoyi na 31 da 32 cikin suratu Kasasi.

 

وَأَنْ أَلْقِ عَصَاكَ فَلَمَّا رَآهَا تَهْتَزُّ كَأَنَّهَا جَانٌّ وَلَّى مُدْبِرًا وَلَمْ يُعَقِّبْ يَا مُوسَى أَقْبِلْ وَلا تَخَفْ إِنَّكَ مِنَ الآمِنِينَ
 

 

31-Kuma ka jefar da sandarka, to lokacin da ya gan tana mirgina kamar majici sai ya ba da baya a guje, bai ko waiwaya ba.(aka ce da shi) Ya Musa dawo, kuma kada ka ji tsoro, hakika kai kana cikin amintattu.

 

اسْلُكْ يَدَكَ فِي جَيْبِكَ تَخْرُجْ بَيْضَاء مِنْ غَيْرِ سُوءٍ وَاضْمُمْ إِلَيْكَ جَنَاحَكَ مِنَ الرَّهْبِ فَذَانِكَ بُرْهَانَانِ مِن رَّبِّكَ إِلَى فِرْعَوْنَ وَمَلَئِهِ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَ
 

 

32-Ka sanya hannunka a cikin wuyan rigarka, zai fito fari fat ba tare da wata cut aba, kuma ka mayar da hannunka (cikin hamatarka), saboda tsoron (farin),To biyu din nan hujjoji ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da mutanensa, hakika su sun kasance mutane ne fasikai.

Kamar yadda yake a dabi'ance, yayin da Musa ya ji wannan magana, wacce bait aba jin irinta ba, kuma bai santa ba, dole ne a rude kuma yayi mamaki, tare da dora ayar tambaya, wannan mine ne, me kuma ake nufi da hakan? Domin Musa ya samu nutsuwa da abinda ya ji, sai Allah madaukakin sarki ya cika hujjarsa a gare shi ya ce Ya Musa daga bangaren Allah madaukakin sarki ne, sannan kuma ya gwada masu mu'uzuzoji guda biyu, na farko ita sandar dake hanun Musa ta koma Maciji, na biyu kuma hanun sa yake haskakawa, bayan ganin wadannan mu'uzuzoji guda biyu sai samu tabbaci da nutsuwa game da abinda ya ji, sannan aka umarce shi da wadannan mu'uzuzoji guda biyu ya koma kasar Masar, abinda aikin da aka umarce shi,zuwa fadar Fir'auna, wurin a can ya gudanar da rayuwarsa, a can ne ya girma, amma a wannan karo domin ya kira fur'auni da bautar Allah daya, kuma ya dakatar da zalincin da yake yiwa Bani-isra'ila.

 A cikin wannan Aya muna iya ilamtuwa da abubuwa guda uku kamar haka:

1-Duk wanda zai iya shiryar da wasu, to ya kamata ya samu nutsuwa na cewa hanyar da shi yake bi gaskiya ce.

2-Domin shiryar da Al'umma, da farko ya kamata a gano tushen zalinci da barna a kawar da su.

3-tsoro da kuma gujewa hadari, al'adar dan Adam ce, babu babbanci tsakanin Annabawa da sauran mutane.

****************************Musuc*********************************

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..