Suratul Qasas, Aya ta 33-37 (Kashi na 703)
Suratul Qasas, Aya ta 33-37 (Kashi na 703)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
----------------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 33 da kuma ta 34 cikin suratu Kasas.
قَالَ رَبِّ إِنِّي قَتَلْتُ مِنْهُمْ نَفْسًا فَأَخَافُ أَن يَقْتُلُونِ
33-(Musa) ya ce:Ya Ubangijina, hakika ni na kashe musu wani mutum, to ina tsoron su kashe ni.
وَأَخِي هَارُونُ هُوَ أَفْصَحُ مِنِّي لِسَانًا فَأَرْسِلْهُ مَعِيَ رِدْءًا يُصَدِّقُنِي إِنِّي أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ
34-Kuma dan'uwana Haruna shi ya fi ni fusahar harshe,sai ka aike shi tare da ni ya taimaka min ya gaskanta ni, hakika ni ina jin tsoron su karyata ni.
A shirin da ya gabata, Allah madaukakin sarki a Dutsin Tur ya umarci Musa da ya tafi fadar fur'auna, ya kira shi da bautar Allah daya.
Wadannan Ayoyi, na bayyanin cewa, Musa ya gabatar da wasu matsaloli guda biyu a hanyar zartar da wannan umarni, na farko, shi ne taimakon da ya bawa wani bani isla'ila da hakan yayi sanadiyar kashe wani Bakibde, da kuma yadda jami'an tsaro Fir'auna suke neman sa domin zartar da hukuncin kisa a kansa. Matsala ta biyu kuwa, Musa (a.s) ya ce harshe Na ba fasihi ba ne ba na iya bayyani da kyau, domin haka me yiyuwa ni kadai ba za iya zartar da wannan umarni ba kamar yadda ake so, domin hakan ina neman izini a hada ni da Dan uwana Haruna domin ya taimaka min dangane da karyar fir'auna, saboda da iya maganarsa da bayyanansa zai kare gaskiya.
Daga cikin wannan Aya za mu ilmatu da ababe guda uku kamar haka:
1-a yayin karbar mukami, yana kyau mutum ya bayyana wuraren da yake da rauni da kuma matsalolinsa cikin gaskiya, kuma ya bayar da shawarwarin da yake ganin za su iya magance wadannan matsaloli da rauninsa
2-iya bayyani , na daga cikin ababen da suke tasiri wajen janyo hankalin Mutane, kuma na daga cikin ababen da suke sanya mai wa'azi ya samu nasara a da'awarsa.
3-A yayin gabatar da wani babban aiki,ana iya amfani da iyawar wani, duk wani karfi da za ka iya amfani da shi wajen cimma manufa, to kayi amfani da shi, bkuma ba wajibi ba ne ka ce ko wani aiki kai kadai za ka yi.
Yanzu kuma lokaci yayi da za su saurari karatun Aya ta 35 cikin wannan Sura ta kasas.
قَالَ سَنَشُدُّ عَضُدَكَ بِأَخِيكَ وَنَجْعَلُ لَكُمَا سُلْطَانًا فَلا يَصِلُونَ إِلَيْكُمَا بِآيَاتِنَا أَنتُمَا وَمَنِ اتَّبَعَكُمَا الْغَالِبُونَ
35-(sai Allah) Ya ce: "Za Mu karfafa dantsenka da dan'uwanka kuma Mu sanya muku nasara, ba za su isa gare ku (da wata cuta) ba.(To ku tafi) da ayoyina ku da wadanda suka bi ku, ku ne masu yin galaba.
Allah madaukakin sarki ya karba bukatar Musa (a.s), ya kuma bayar da izini ga dan'uwansa ya kasance a tare da shi a wannan hanya mai hadarin gaske, da wannan matsalolin da Musa ya gabatar sun kawar, da farko babu wanda zai iya karfin hali na kokarin cutar da Musa ko kuma kashe shi, na biyu kuma kasancewar dan'uwansa Musa Harun a majalisi ko fadar fir'auna, hakika da gaskiya za ta bayyana, kuma iya bayani na Harun da kuma gaskiyar da suke dauke da shi, za su galaba a kan karyayyakin Fir'auna da Fir'auniyawa.
Duk da cewa Harun shi ne babba da Musa, a bangaren bayyani ya fi Musa iya bayyani, amma Musa ya nada kamalar da ya sanya, Allah madaukakin sarki ya bashi annabta, Littafi na shari'a, duk da cewa dan'uwan Musa, shi ma annabi ne, to amma ya zama wajibi ya kasance mataimakin Musa, kuma ya zamanto a tare da shi, domin ya taikama masa, daya daga cikin mu'ijizarsa kuma kaskantar da fur'auna, da bayanansa ya yi galaba a kan karyace-karyacen fir'auna.
1-A fagen yaki da karya, ba wajibi ba ne, bangaren karya da gaskiya su kasance daidai, wani lokaci mutum biyu idan su nada kwararen hujjoji mabayyana, suke yin galafa a kan babbar tawagar karya.
2-wajibi ne a goyawa mutunan Allah , da kuma mabiya gaskiya, don kadda su fada hanun azzalimai, kuma kadda azzalimai su yi galaba a kan su.
3-domin isar da sakon gaskiya da yaki da azzalimai, ko Annabawa suna bukatar fata gami da nutsuwa dangane da abinda zai faru nan gaba.Allah madaukakin sarki ya yiwa Annabi Musa da da'unwa Haruna gami da magoya bayansu alkawarin samun nasara, da hakan ya basu karfin gwiwa na kyakkyawan fata nan gaba.
Yanzu kuma lokaci ya yi da za mu saurari karatun Ayoyi na 36 da ta 37 a cikin wannan sura ta kasas.
فَلَمَّا جَاءَهُم مُّوسَى بِآيَاتِنَا بَيِّنَاتٍ قَالُوا مَا هَذَا إِلاَّ سِحْرٌ مُّفْتَرًى وَمَا سَمِعْنَا بِهَذَا فِي آبَائِنَا الأَوَّلِينَ
36-To lokacin da Musa ya zo musu da ayoyinmu mabayyani sai suka ce:'Ai wannan ba wani abu ba ne face kagaggen shiri, mu kuma ba mu taba jin wannan ba a wurin iyayenmu na farko.
وَقَالَ مُوسَى رَبِّي أَعْلَمُ بِمَن جَاءَ بِالْهُدَى مِنْ عِندِهِ وَمَن تَكُونُ لَهُ عَاقِبَةُ الدَّارِ إِنَّهُ لا يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ
37-Musa kuma ya ce: "Ubangijina (shi ne) ya fi sanin wanda ya zo da shiri daga wurinsa, da kuma wanda kyakkyawan karshe zai kasance a gare shi, hakika shi dai(al'amarin) kafurai ba sa rabauta.
Annabi Musa da dan'unsa haruna sun yi kokari wajen bin hanyoyin da suka dace har sai da suka isa fadar Fur'auna inda suka kasance a tsakanin manya manyan fadawa, da farko sun fara kirar Fur'auna zuwa ga bautar Allah daya, sannan kuma suka gwada masa irin mu'ijizar da suke dauke da ita, ya jefa sandar sa ta koma macijiya, sannan kuma hanunsa da ya fitar da bangaren wuyansa ya zamanto mai haske kuma yana haskakawa.
Dangane da wannan bayyani na gaskiya gami da kwararen hujjoji da kuma mu'uzijoji da Musa da dan'uwansa suka zo da shi, martanin da fir'auniyawa suka mayar , shi ne zarki da kuma karyatawa, farkon martini da suka mayar shi ne bata al'umma da ta gabata wacce take bautar Allah daya,domin haka wannan bayyani da Annabi Musa ya zo ta it aba abu ba be da za a amince da shi, ma biyu kuma suka ce mu'izijar da ya zo da ita, tsafi ne da shi kansa musa ya zo da shi , amma ya danganta shi ga Ubangiji.
Amsar da ya bayar a nan shi ne, Annabi Musa ya ce, idan har wadannan bayyanai da na yi daga ni ne ba daga Allah ba, to Ubangiji ya fiku sani game da wannan al'amari,Allah k aba ni karfin gwiwa ka kuma kare ni daga danganta mata wani abu da b aka fada ba, ko kuma kirkirar annabci daga gare ni, a maimakon shiryar da mutane, ya kasance sanadi na hallakar su. Saidai ni abinda na fada gaskiya ne, kuma na zo muku da cikekkiyar hujja, domin haka idan kuna so milkinku ya dore to ku bada gaskiya da abinda na zo da shi, idan kuma ba haka ba to zakka babu za ku yi hasara Duniya da Lahira.
Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-a yayin karbar koyarwar Addinni, hankali, tunani da hujjoji, su ne ma'auni, ba magana da tafarkin wadanda suka gabata ba.
2-zarki da karyatawa, shi ne babban makami na masu adawa da Annabawa gami da masu gyara a tsahon tarihi.
3-Biyayya ga shiriyar Annabawan Allah, sanadi ne na samun farin ciki, ceto, kubuta da kyakkyawar makoma.
*************************Musuc****************************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..