Suratul Qasas, Aya ta 38-42 (Kashi na 704)
Suratul Qasas, Aya ta 38-42 (Kashi na 704)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
-------------------------------------------/
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 38 cikin suratu Kasas.
وَقَالَ فِرْعَوْنُ يَا أَيُّهَا الْمَلَأُ مَا عَلِمْتُ لَكُم مِّنْ إِلَهٍ غَيْرِي فَأَوْقِدْ لِي يَا هَامَانُ عَلَى الطِّينِ فَاجْعَل لِّي صَرْحًا لَّعَلِّي أَطَّلِعُ إِلَى إِلَهِ مُوسَى وَإِنِّي لَأَظُنُّهُ مِنَ الْكَاذِبِينَ
38-Fir'auna kuma ya ce: "Ya ku jama'a, ban san kuna da wani Ubangiji ba in ba nib a, kai ko Hamana shirya min konannen birki, sannan ka yi min dogon gini don in hango Ubangijin Musa, ba shakka ni ina tsammanin cewa shi yana cikin makaryata.
A shirin da ya gabata, mun bayyana cewa fir'auna da fadawansa sun karyata sakon da Annabi Musa ya zo musu da shi, sannan sun bayyama mu'ujizar da ya zo da ita a matsayin tsafi, sannan kuma suka ce mutanan da suka gabata bas u san Allah Musa ba kuma ba sa bauta masa.
Wannan Aya na cewa, daya daga cikin hanyoyin da fir'auna ya bi domin kalubalantar Musa da kuma hana maganar gaskiya ta samu karbuwa a wajen mutane, shi ne ya bayar da umarni da a shirya masa konannun birki sannan ya gida masa dogon gini, shi da manyan fadawansa su hau domin su hango Ubangijin da Musa yake fada, shin ana ganin sa ko kuma a'a?
A hakikanin gaskiya fir'auna ya bayar da wannan umarni ne domin ya yaudari mutanan gari da suka taru a fada,ya na so ya fada musu cewa shi ne Ubangiji, kuma bai san wani ubangijinsu ba bayansa, amma don kadda su yi tsamanin cewa yana adawa da Annabi Musa, sai yayi amfani ta wannan hanya wajen watsi da bayyanan annabi Musa, ka ga idan ya ce shi kadai zai hau ginin, to yana isa sanya shakku a zukatan al'umma domin haka yayi amfani da manyan gari su ma su hau dogon ginin domin su hango Allah da Musa yake fada, saboda ya san ba a hango Allah a sama, su fahimci cewa maganar da Musa yake fad aba gaskiya ba ne.
Daga cikin wannan Aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-girman kai gami da jiji da kai, sanadi ne na hana karbar gaskiya.
2-Masu girman kai suna amfani da hanyoyi mababbanta domin yaudarar al'umma na hana su karbar gaskiya.
3-Ma'abota girman kai na ganin cewa su ne tushen komai, kuma su ne mamallaka da masu milkin doron kasa, babu wani mai hakki da wadannan ababe idan ba su ba, a nan ma fir'auna na ganin cewa shi ne mamallakin komai, duk abinda ke cikin Duniya na karkashin milkinsa ne.
Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari ayoyi na 39 da 40 cikin wannan sura ta kasas.
وَاسْتَكْبَرَ هُوَ وَجُنُودُهُ فِي الأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَظَنُّوا أَنَّهُمْ إِلَيْنَا لا يُرْجَعُونَ
39-Ya kuma yi girman kai shi da rundunoninsa a bayan kasa ba da wata hujja ba ba, suka kuma yi tsamamanin cewa su ba za a komar da su zuwa gare Mu ba.
فَأَخَذْنَاهُ وَجُنُودَهُ فَنَبَذْنَاهُمْ فِي الْيَمِّ فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الظَّالِمِينَ
40-Sai Muka kama shi tare da rundunoninsa, sannan Muka watsa su a cikin kogi, to ka duba ka ga yadda karshen kafurai ya kasance.
Wadannan ayoyi suna ishara ke game da wasu ababe guda biyu da suka yi sanadiyar faduwar hukumar fur'auna. Na farko girman kai, da kuma ganin fifiko a kan wani, fir'auna na ganin cewa ya fi kowa kuma shi ne sama da kowa, na biyu kuma shi ne zalinci ga masu karamin karfi, tare kuma da haramta musu hakkokin su.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:
1-kadda mu kalubalanci gaskiya da hakan zai yi sanadiyar hallakar mu.
2-rashin Imani da ranar lahira, hisabi, da littafin lahira, shi ke sanya mutum girman kai. Kuma wannan shi ne abinda ya haifar da zalinci, ta'addanci da kuma girman kai.
3-Azabar Ubangiji ba ta kebbanta da ranar lahira ba, Allah madaukakin sarki tun a nan Duniya yake kaskantar da masu girman kai.
4- a tsahon tarihi, makomar masu girman kai iri daya ce.
Yanzu kuma lokaci yayi da zamu saurari karatun ayoyi na 41 da 42 cikin wannan sura ta Kasas.
وَجَعَلْنَاهُمْ أَئِمَّةً يَدْعُونَ إِلَى النَّارِ وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ لا يُنصَرُونَ
41-Muka kuma mayar da su shugabanni masu kira zuwa ga wuta, ranar alkiyama kuma ba za a taimake su ba.
وَأَتْبَعْنَاهُمْ فِي هَذِهِ الدُّنْيَا لَعْنَةً وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ هُم مِّنَ الْمَقْبُوحِينَ
42-Muka kuma bi su da la'anta a wannan duniyar, ranar alkiyama kuma suna cikin wadanda za a jefa cikin mumuman hali.
A ci gaban ayoyin da suka gabata, da suke bayyani kan karshen fir'auniyawa a wannan Duniya, wadannan ayoyi kuwa na bayyanin cewa a ranar lahira Za a sanya masu sabo a wuta, fur'auniya za su kasance a tare da su, kamar yadda suka kasance a nan Duniya su ne shugabaninsu , a lahira ma su ne shugabani wajen shiga wuta.
Sun kasance a nan Duniya cikin tsinuwa da la'ana na wadanda suka zalinta, kuma daga wannan lokaci har zuwa karshen Duniya suna cikin tsinuwa da la'anta ta muminai, wannan mumunar sunna dake tare da su, a ranar lahira za a tashe su cikin wulakanta, kuma a gane su da munanan fuskoki.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:
1-wadanda a yau su keda karfi , kuma suna jin dadi da irin wadatar da suke da ita na komai da komai, a ranar alkiyama za a tayar da su tare da mataimaka ba, ko karfin ceton kansu bas u da shi, to ina ga ceton wasunsu.
2-La'anta da tsinuwa ga Azzalimai, da kuma yin alawadai gare su,al'amari ne da Allah madaukakin sarki ya hallita.
3-A nan Duniya wadanda suke taimakawa kafirci da bata, a ranar Lahira za a tashe su tare da kafirai da batattu kuma za a sanya su wuta tare.
4-Munanan ayyukan mutum a nan Duniya, za su sanya ya tashi da muni a ranar Lahira.
*************************Musuc****************************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..