Suratul Qasas, Aya ta 43-46 (Kashi na 705)
Suratul Qasas, Aya ta 43-46 (Kashi na 705)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
-------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun Aya ta 43 cikin suratu Kasas.
وَلَقَدْ آتَيْنَا مُوسَى الْكِتَابَ مِن بَعْدِ مَا أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ الأُولَى بَصَائِرَ لِلنَّاسِ وَهُدًى وَرَحْمَةً لَّعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
43-Hakika kuma Mun baiwa Masu littafin (Attaura)bayan mun hallaka al'ummun na farko don izina ga mutane da shiriya da rahama ko sa wa'azantu.
A shirin da ya gabata, mun bayyana cewa bayan nutsewar da ruwan Nilu, an kawo karshe fir'auna da Sojojinsa, wannan aya kuwa na bayyanin cewa, bayan da muka tsiratar da al'ummar Bani-isra'ila daga kangin zalincin hukumar fir'auna, mun shiryar da su,mun daga tunani da basirar su, kuma mun saukar da Attaura ga Annabi Musa domin su amfana,dukkanin wadannan ababe sun kumshi tausayi da jin kan Ubangiji na musaman. Ko da yake Bani-Isra'ila da sun kafircewa Attaura, da sun kasance daga cikin wadanda suka kalubalanci gaskiya, kamar yadda al'ummar da ta gaba ce ta fada cikin azabar ubangiji tun a nan duniya, da su ma sun hallaka.
Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:
1-Bayyanar Annabawa da ma'aika, saukar da Litattafai daga sama, tushen rahamar Ubangiji ne, kuma babbar ni'imar Ubangiji ne domin shiryar da mutane zuwa facin ciki na gaskiya.
2-Sunnar Ubangiji a tsahon tarihi, tabbacecciya ce, duk al'ummar da ta kauce daga hanyar gaskiya, daga karshe za ta fada cikin hallaka.
Yanku kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun aya ta 44 da kuma ta 45 cikin wannan sura ta Kasas.
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ الْغَرْبِيِّ إِذْ قَضَيْنَا إِلَى مُوسَى الأَمْرَ وَمَا كُنتَ مِنَ الشَّاهِدِينَ
44-Kai kuma ba ka kasance a gefen (dutsen Duri) na yamma ba lokacin da Muka yo wahayin manzanci zuwa ga Musa, b aka kuma kasance cikin wadanda suke wurin ba.
وَلَكِنَّا أَنشَأْنَا قُرُونًا فَتَطَاوَلَ عَلَيْهِمُ الْعُمُرُ وَمَا كُنتَ ثَاوِيًا فِي أَهْلِ مَدْيَنَ تَتْلُو عَلَيْهِمْ آيَاتِنَا وَلَكِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ
45- Sai dai cewa Mu Mun halicci al'ummu sannan nisan zamani ya tsawaita a gare su, kuma ba kasance a zaune cikin mutanen Madayana ba kana karanta musu ayoyinmu, sai dai kuma Mu Mun kasance masu yi maka wahayi ne (da wadannan labarum).
Wadannan ayoyi suna tabbacin cewa duk abinda ya zo cikin Alkur'ani dangane da al'umma da kuma Annabawa da suka gabata, dalili ne a kan gaskiyar abinda Manzon Allah (s.a.w.a) ya zo da shi, saboda Ma'aiki (s.a.w.a) bai kasance da mutanan da suka gabata ba, kuma yana bayar da labarin kan hakikanin abinda ya kasance a wancan lokacin, kamar yadda ya bayar da cikekken labarin anabtar Annabi Musa (a.s), abinda ya kasance a dutsun Dur, karnoni da dama kafin haifuwar Manzon Allah (s.a.w.a), labarin abinda ya faru ya zo cikin Alkur'ani daki-daki.kamar yadda aka bayar da labarin abinda ya faru a garin Madayyana, yayin da Musa ya gudu daga garin Masar, ya isa zuwa can, bayan haka, sanayyarsu da Annabi Shu'aibu, auransa da diyar Annabi Shu'aibu.kamar yadda aka Ambato da labarin al'ummomin da suka gabata shekaru da dama.
Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:
1-Labarin tarihin da ya zo a cikin Alkur'ani,gaba dayan su labari ne na gaibi, saboda lokacin da Manzo ke cikin garin Makka, al'umma ba su san wannan labari ba.
2-Daya daga cikin dalilan Mu'ujizar alkur'ani da gaskiyar Ma'aikin Allah (s.a.w.a), shi ne labarin gaibi, da ayoyi da dama suka kebanta da shi.
Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun aya ta 46 cikin wannan sura ta kasas.
وَمَا كُنتَ بِجَانِبِ الطُّورِ إِذْ نَادَيْنَا وَلَكِن رَّحْمَةً مِّن رَّبِّكَ لِتُنذِرَ قَوْمًا مَّا أَتَاهُم مِّن نَّذِيرٍ مِّن قَبْلِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
46-Kuma ba ka kasance a gefen (dutse) Duri ba, lokacin da Muka kirawo (Musa), sai dai wata rahama daga Ubangijinka, don ka gargadi wasu mutane da mai gargadi bai zo musu ba gabaninka ko sa wa'azantu.
Ayoyin da suka gabata sun tabbatar da labarin gaibi na rayuwar annabi Musa (a.s), wannan aya kuma tana magana ne dangane da Ma'aiki (s.a.w.a): abinda muka saukar maka, lutufi ne na Ubangiji domin ka bayyana wa Al'umma abinda ya wakata ga mutanan bani-isra'ila, kuma ka gargadin al'ummar ka game da karshen ayyukansu.
Sanannan abu ne, mutanan da suka rayu a garin Makka, zamanin Ma'aikin Allah (s.a.w) ba su taba ganin wani Annabi ba da zai iya ba su labarin mutanan da sukla gabata ba,kamar yadda ya kasance cikin karni biyu zuwa uku kafin zuwan Manzon Allah (s.a.w.a), babu wani Annabi da aka tayar har ma ya bayar da wannan labara.ko da yake Annabawa kamar Hudu, Salih, da Shu'aibu an tayar da su ne a Jazerar larabawa da wasu kasashe na daban, to amma su lokacin ya fice sosai ta yadda to wani asari da suke shi ya kawar.
Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:
1-daya daga cikin manufar tayar da Annabawa gami da saukar da Litattafan sama, shi ne yiwa mutane gargadi a kan kadda su fada cikin gafala, su kuma manta da ranar Lahira.
2-Hankali da fitira sun shiryar da mutane zuwa gaskiya da ababen da suke na hakika da dama, to amma akwai abubuwa da dama da suke yin sanadin mutum ya gafala daga wannan kira, domin haka Annabawa suke tunanar da mutane kuma suna gargadinsu, kan mai yiyuwa ko sun tuna su kuma koma zuwa ga hanyar gaskiya.
*************************Musuc****************************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..