Suratul Qasas, Aya ta 47-50 (Kashi na 706)
Suratul Qasas, Aya ta 47-50 (Kashi na 706)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
-------------------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 47 da 48 cikin suratu Kasas.
وَلَوْلا أَن تُصِيبَهُم مُّصِيبَةٌ بِمَا قَدَّمَتْ أَيْدِيهِمْ فَيَقُولُوا رَبَّنَا لَوْلا أَرْسَلْتَ إِلَيْنَا رَسُولا فَنَتَّبِعَ آيَاتِكَ وَنَكُونَ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ
47-Kuma ba don haka wata masifa ta same su ba saboda abin da suka aikata da kansu sannan su ce:"Ya Ubangijinmu, ina ma da kai aiko mana da wani manzo, sannan mu bi ayoyinka mu kuma kasance cikin muminai?
فَلَمَّا جَاءَهُمُ الْحَقُّ مِنْ عِندِنَا قَالُوا لَوْلا أُوتِيَ مِثْلَ مَا أُوتِيَ مُوسَى أَوَلَمْ يَكْفُرُوا بِمَا أُوتِيَ مُوسَى مِن قَبْلُ قَالُوا سِحْرَانِ تَظَاهَرَا وَقَالُوا إِنَّا بِكُلٍّ كَافِرُونَ
48-Sannan lokacin da gaskiya ta zo musu daga wajenmu sai suka ce: Ina ma da an bas hi irin abin da aka bai wa Musa? Yanzu ashe tun da can ba su kafirce da abin da aka bai wa Musan ba, suka ce: Su biyun shiri ne (Alkur'ani da Attaura) da suke taimakon juna? "Suka kuma ce:"Hakika mu mun kafirce da su gaba daya."
Wadannan ayoyi suna ishara ne a kan sunar Ubangiji tsahon tarihi,suna cewa Allah madaukakin sarki ya bawa mutune hankali, su kuma su yi amfani da hankalinsu wajen babbance ayyuka masu kyau, da marassa kyau,akida ta gaskiya da ta karya, kuma su fahimci al'adu masu kyau da marassa kyau. Duk da haka, sunar Ubangiji ce matukar bai aikowa wata al'umma ma'aiki ba, ba ya hukunta su game da ayyukan da suka aikata ba. Duk da hakan, masu sabo za su so da uzirin cewa da Manzo da ya zo mana da mun kasance daga cikin shiryaryyu.
Ci gaban ayoyin na cewa bayan da aka aiko da Manzo wani bangare da mutane za su zo da wani uziri na daban suna masu cewa me ya sanya Annabi Muhamadu (s.a.w.a) bai zo da mu'uzija irin ta Annabi Musa (a.s)? me ya sanya sandar hanunsa ba ta zama macijiya ba, ko kuma teku bai tsage gida biyu ya fice, su kuma makiya su hallaka ba?
Game da wannan uzuri, Alkur'ani mai girma ya bayar da amsa ya ce: shi kuna tunanin dukkanin Mutanan da suka rayu a zamanin Annabi Musa (a.s) suka yi Imani da shi duk da irin mu'ujizar da suka gani? Shinda Annabi Muhamadu (s.a.w.a) ya zo da irin wannan mu'ujiza, akwai wanda yake da uzuri na rashin yin Imani? A hakikanin gaskiya masu kawo uzuri,a ko wani zamani, idan suka ga mu'ujizar ubangiji, sai su kira ta da sihiri ko tsafi, kuma ba shirye suke bas u karbi gaskiya. Kamar yadda masu adawa da Annabi Musa suka kira shi a matsafi, ko kuma boka, kamar yadda masu adawa da Ma'aikin Allah (s.a.w.a) suka kira shi da mai sihiri.wani banga. Wani gungu sun ganin cewa sandar Annabi Musa da ta koma macijiya, tsafi ne, wasu gungu kuma na ganin ayoyin Alkur'ani mai girma da aka aiko Annabi Muhamadu (s.a.w.a) da su, sihiri ne.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-Ubangiji da ya aiko Manzanni, ya cika hujja a kan al'umma, ya toshe duk wata hanya da neman uzuri.
2-da dama daga cikin matsaloli da masifofin da muke fuskanta, sakamakon ayyukanmu ne, ayyuka na gari, da marassa kyau nada tasiri tun a nan duniya.
3-Sihiri da tsafi, su ne zarkin da kafirai suka fi yiwa Annabawan Allah, munkirai sun yi da'awar cewa Attaura da Alkur'ani litattafai ne guda biyu na sihiri, da daya daga cikinsu ke goyon bayan dayansa.
Yanzu kuma, lokaci yayi da za mu saurari karantun ayoyi na 49 da na 50 a cikin wannan sura ta Kasas.
قُلْ فَأْتُوا بِكِتَابٍ مِّنْ عِندِ اللَّهِ هُوَ أَهْدَى مِنْهُمَا أَتَّبِعْهُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ
49-Ka ce (da su)."To ku zo da wani littafin daga wajen Allah wanda ya fi su nuna hanyar shiriya(watau Alkur'ani da Attaura), zan bi shi idan kuna kasance masu gaskiya.
فَإِن لَّمْ يَسْتَجِيبُوا لَكَ فَاعْلَمْ أَنَّمَا يَتَّبِعُونَ أَهْوَاءهُمْ وَمَنْ أَضَلُّ مِمَّنِ اتَّبَعَ هَوَاهُ بِغَيْرِ هُدًى مِّنَ اللَّهِ إِنَّ اللَّهَ لا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ
50-To idan ba su amsa maka ba, sai ka tabbatar da cewa ba abin da suke bi sai soye-soyen ransu kawai,ba kuwa wanda ya fi bacewa kamar wanda ya bi son ransa ba tare da wata shiriya daga Allah ba, hakika Allah ba ya shiryar da mutane kafurai.
A cikin ayoyin da suka gabata, kafirai sun kasance suna zarkin Annabawan Allah da bokaye ko kuma masu tsafi,wadannan ayoyi suna magana da ma'aiki (s.a.w.a) sun ce ka fada masu adawa da kai cewa, idan kun kasance masu inkari da Attaura da Alkur'ani da suke a matsayin Littatafan Ubangiji biyu da aka saukar daga sama, to ku zo da wani Littafi da ya fi wadannan litattafai shiryarwa, ku tabbatar da cewa idan ku ka zo da wannan Littafi zan yi biyayya da shi. Wato Manzo ya ce manufar wadannan litattafai isa zuwa ga shiriyar Ubangiji, idan kuma Allah ya tayar da ku, to ku zo mana da Littafi, za mu amince da shi kuma mu bi ku.
Sannanan abu ne, wadanda ba zo da wani littafi daga wajen ubagiji ba, kuma ma ba su san wani littafin da ya fi Alkur'ani kamala ba, saidai kawai suna bayan cimma wasu bukatunsu ne, ganin cewa Alku'ani da litattafan shiriyar da aka saukar daga masa sun sabawa son zuciyarsu, domin haka suke dora wannan ayar tambaya.
A hakikan gaskiya, masu bin son zuciya na hana karbar gaskiya, kuma suna jan mutane zuwa ga bata, inda suke bayyana kansu a matsayin shiryayyu, su kuma ma'aika a matsayin wadanda suka bata, a ganin su su shiryayyu ne.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-Domin tabbatar da gaskiya, wani lokaci akwai bukatar bin hanyoyi na munazara da kuma kalubantar bangaren a kan abida ya yi dawa'a, kamar yadda daya daga cikin dalilan tabbatar da gaskiyar ma'aiki da kur'ani, shi ne bin wannan hanya ta munazara da Tahhadi
2-Mutum ya kamata ya kasance yana bayan gaskiya, ko da kuwa daga bakin dan adawarsa gaskiyar ta fito ya amince da ita.
3-Shiriya ta gaskiya, ita ce shiriyar da ta fito daga ilimi da kuma hikimar marar iyaka ta Ubangiji madaukakin sarki, ba wacce ta fito daga rageggen ilimi, da kuma wacce aka koya da son zuciyar dana dam.
*************************Musuc****************************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..