Suratul Qasas, Aya ta 51-55 (Kashi na 707)
Suratul Qasas, Aya ta 51-55 (Kashi na 707)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
----------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 51 da 52 cikin suratu Kasas.
وَلَقَدْ وَصَّلْنَا لَهُمُ الْقَوْلَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ
51- Hakika kuma mun sadar musu da fadi (na bin wani na Alkur'ani) don su wa'azantu.
الَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ مِن قَبْلِهِ هُم بِهِ يُؤْمِنُونَ
52- (Wasu daga) cikin wadanda Muka bai wa Littafi a gabaninsa (Alkur'ani) su suna bada gaskiya da shi.
Wadannan ayoyi da farko sun yi ishara a kan kafirci gami irin jayayya ta kafirai, Allah tabaraka wa ta'ala na cewa Mu mun saukar da ayoyin alkur'ani ne sannu-sannu, kuma a hankali, domin zukatan mushrikai su tasirantu, to amma duk da hakan tunatarwar da ake yi musu ba ta yi amfani gare sub a,kuma bas u karbi kalaman gaskiya ba,a yayin da wasu ma'abuta littafi suka yi Imani da Annabin musulinci gami da Littafin da ya zo da shi,a yayin da suka fahimci gaskiyar Annabin musulinci sai suka yi Imani da shi suka kasance daga cikin masu goyon bayansa.a matsayin misali, mailman tarihi sun ruwaito wani hadisi, inda a cikin sa aka bayyana cewa sarkin kasar Habasha da ya kasance mabiyin kirista ne ya aike da wasu manyan mailman kirista zuwa birnin Makka domin gudanar da bincike game da Annabin musulinci da kuma addininsa,a yayin da suka saurari kalamai masu sanyaya zukata sai suka yi Imani da shi sannan kuma suka kasance daga cikin manyan sahabansa masu kira zuwa ga addinin islama.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-Tarbiya, almari ne na sanu-sanu kuma a hankali, tare da amfani da tunatarwa gami da shiryarwa, ba wai amfani da karfi ko tailastawa ba.
2-manufar Litattafan da aka saukar daga sama gami da shugabanin Addini abu guda ne kuma fadar su ma abu guda ne.
3-Ma'abuta Littafi na gaskiya, su ne wadanda bayan zuwan Annabin musulinci suka kuma san shi gami da addinin da ya zo da shi sai suka yi Imani da shi, kuma ba su kasance masu kabilancin addini da kuma akidar da suke kanta a bay aba.
Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karantun Ayoyi na 53 da na 54 cikin wannan sura ta kasas.
وَإِذَا يُتْلَى عَلَيْهِمْ قَالُوا آمَنَّا بِهِ إِنَّهُ الْحَقُّ مِن رَّبِّنَا إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلِهِ مُسْلِمِينَ
53- Idan kuma an karanta musu (Alkur'anin) sai su ce:"Mun ba da gaskiya da shi, ba shakka shi gaskiya ne daga Ubangijinmu, Hakika mu mun kasance musulmi tun gabaninsa".
أُوْلَئِكَ يُؤْتَوْنَ أَجْرَهُم مَّرَّتَيْنِ بِمَا صَبَرُوا وَيَدْرَؤُونَ بِالْحَسَنَةِ السَّيِّئَةَ وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ
54-Wadanda za a ba su ladansu ninki biyu saboda hakurin da suka yi, kuma suna kawar da mummunan aiki da kyakkyawa, suna kuma ciyarwa daga abin da Muka arzuta su (da shi).
A ci gaban ayoyin da suka gabata, wadannan ayoyi na cewa wadannan gungu na ma'abuta littafi wadanda suka yi Imani da annabin musulinci, su nada tsarkakan zukata, kuma sun rausayawa gaskiya, ta yadda a yayin da Annabi (s.a.w.a) yake karanta musu ayoyin alkur'ani suna fadar cewa hakika mun shaida wannan daga Allah ne kuma mun yi Imani da shi, kamar yadda ya kasance a baya sun meka wuya da kuma Imani ga ma'aikin Allah (s.a.w.a).
Alkur'ani mai girma na cewa: domin haka wadannan mutane su nada lada ninki biyu, daya saboda imanin da suka yi ga Littafi da kuma Annabin da ya gabata, na biyu kuma saboda imanin da suka yi da annabin musulinci da kuma littafin da ya zo da shi.bayan haka Ubangiji yake siffanta su kamar haka, wadannan sune masu mayar da mumuna da kyakkyawa, kuma dangane da munanan kalamai suna mayar da kyakkyawar magana, dangane kuma da mumunar mu'amala, sun kasance masu hakuri da juriya, game da rashin tausayi kuma suna nuna soyassa da tausayi, wadannan su ahlin infaki da bayarwa kuma su ne masu binciken halin da tallakawa ke ciki domin taimaka musu, ba kuma sa manta wasunsu.
Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-Masoya gaskiya, su a ko yaushe suna bayan gaskiya, ba ruwan daga wajen wanda ta fito, ko daga wani baki ta fito, tushen ma'auninsu shi ne gaskiya, kuma it ace mai mahimanci a gare su, domin haka duk wanda ya fi gaskiya, wajibi ne su amince da ita.
2-Karbar gaskiya, tana bukatar hakuri da juriya game da duk wani nau'in matsaloli, da kuma irin sabanin da za a fuskanta.
3-Alakar zamantakewa da kuma mu'amala tare da mutane, tushensa shi ne yafiya, ko da yake akwai abinda ya fi hakan, shi ne mayar da kyakkyawa ga mumuna.
Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun ayar ta 55 cikin wannan sura ta kasas.
وَإِذَا سَمِعُوا اللَّغْوَ أَعْرَضُوا عَنْهُ وَقَالُوا لَنَا أَعْمَالُنَا وَلَكُمْ أَعْمَالُكُمْ سَلامٌ عَلَيْكُمْ لا نَبْتَغِي الْجَاهِلِينَ
55-Idan kuma suka ji maganar banza sai su kau da kai daga gare ta, su kuma ce (sakamakon) ayyukanmu yana gare mu, ku kuma na ayyukanku yana gare ku,Mun kubuta daga gare ku, ba ruwanmu da wawaye.
A ci gaban ayoyin da suka gabata, wannan aya na daga cikin misdaki da kuma tabbacin hakuri game da munanan kalamai gami da mumunar mu'amala na wasu, ayar na cewa mumini na gaskiya shi ne wanda za a fadama munanan kalamai, shi kuma ya bayar da martani da makamantansu watau bay a fadar munanan kalamai ga waninsa, saidai ma yayi kyakkyawar mu'amala da wadanda suka yi masa ba daidai ba, kuma cikin aminci da girmama yace musu: idan ayyukansu sun kasance ban a kirki ba ne, to tasirinsa yana koma gare mu ne, ba gareku ba, haka kuma idan naku ayyukan sun kasance ban a kirki ba, to tasirin sa yana komawa gareku, ba garemu ba.domin haka ku kasanci cikin alheri, mu kuma mu kasance cikin aminci, ba ma neman fitina da ayyukan jahilci.
Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-Sharadin Imani, shi ne nisanta da kalaman wasa da marassa amfani ko kuma munana, kadda mu fadawa wasunmu kalaman banza, kuma kada mu mayar da martani da mumuna ga wadanda suka ci mutuncinmu ko kuma suka fada mana maganar banza, domin shi mumini na gaskiya na kauracewa duk wata magana da ba ta da amfani.
2-Kauracewa abinda ba shi da amfani a bangaren magana ne ko kallo, ko a mu'amala, siffa ce da dukkanin addinan Ubangiji suka yaba.
3-Idan mun san cewa yin hani na abin ki ba zai yi tasiri ba, to akkala abinda ya kamata mu yi shi ne, kauracewa wannan abin ki, domin wanda ke aikata shi ya san cewa ba ma tare da wannan mumunan aikin da yake aikatawa kuma ba mu amince da shi ba.
*************************Musuc****************************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..