Oct 20, 2017 06:30 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 56-58 (Kashi na 708)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

-----------------------------------------

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 56 cikin wannan suratu ta Kasas.

 


إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللَّهَ يَهْدِي مَن يَشَاء وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ

 

56-Hakika kai ba ka shiryar da wanda kake so,sai dai Allah yana shiryar da wanda yake so,Shi kuma ne ya san masu shiryuwa.

A shirin da ya gabata mun bayyana cewa dukkanin mushirikai ba a shirye suke bas u bar bautar gumakai da ababen da suke bautawa ba, amma wani gungu daga cikin mabiya kirista ko ma'abota littafi, da jin ayoyin alkur'ani mai girma daga bakin annabin musulinci (s.a.w.a) sun yi Imani sannan suka bayyana cewa wannan shi ne abinda annabi Isa (a.s) yayi bushara da zuwansa.a ci gaban wadannan ayoyi,, wannan aya na cewa nauyin da ya rataya a kan ma'aika shi ne isar da sakon Ubangiji tare da kiran mutane zuwa ga bautar Allah shi kadai, amma dangane da amincewa ko rashin amincewa mutane ba su da wani shugabanci kansa,su suna shiryar da mutane ne zuwa ga hanyar Allah, amma dangane da wanda zai bi wannan hanya har ya kai ga gaci, to wannan al'amari na hanunsa.domin shi ma'aiki yana son dukkanin al'umma su yi Imani su bautawa Allah daya, to amma bas hi da hakkin tilastawa mutane domin su amince da abinda suka fada musu, ko kuma su bi wannan hanya. Annabawa ba za su iya tilastawa zukatan mutane ba su amince da wannan hanya,Allah ne kawai yake da iko shiryar da mai neman gaskiya da kuma ya caccanci yin Imani, ya amince da wannan hanya, kuma yayi Imani, domin haka baa bin mamaki ba ne a samu wani gungu daga cikin zuriyar Annabi (s.a.w.a) su ki yin Imani da  shi suka kasance mushirikai, kuma a samu wani gungu daga cikin ma'abuta Littafi su yi watsi da duk wani kabilanci na addini da akida su yi Imani da Annabin musulinci (s.a.w.a)

Daga cikin wannan aya, za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:

1-Nauyin da ya rataya ga ma'aika (a.s) shi ne isar da sako tare da kiran mutane zuwa ga bautar Allah daya, ba tilastawa ba, amincewa ko rashin amincewa na hanun mutane.

2-Bukatu da shiriyar ubangiji ya ginu ne a kan ilimi da kuma hikimar sa, Allah madaukakin sarki bisa tushen hikimarsa, duk wanda ya gani ya dace yake bashi taufiki na shiriya.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun aya ta 57 cikin wannan sura ta kasas:

 

وَقَالُوا إِن نَّتَّبِعِ الْهُدَى مَعَكَ نُتَخَطَّفْ مِنْ أَرْضِنَا أَوَلَمْ نُمَكِّن لَّهُمْ حَرَمًا آمِنًا يُجْبَى إِلَيْهِ ثَمَرَاتُ كُلِّ شَيْءٍ رِزْقًا مِن لَّدُنَّا وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لا يَعْلَمُونَ

 

57-Suka ce:"idan muka bi shiriyar tare da kai, to za a kame mu(ribatattu) daga kasarmu" (ka ce da su)" Yanzu ashe ba mu ne Muka tanadar muru harami amintacce ba da ake kawo kowane irin (nau'i) na 'ya'yan itace gare shi don arzutawa daga gare Mu? Sai dai kuma yawaicinsu bas a sanin (haka).

Wannan aya na magana ne a kan wadanda suke rayuwa a garin Makka, duk da cewa sun fahimci gaskiyar ma'aikin Allah (s.a.w.a), amma domin kare amfanin kansu da iyalan sub a a shirye suke ba su ba gaskiya da Imani ba, abinda suke fakewa da shi kuma shi ne, manyan garin makka wadanda iko da kuma dukiya ke hanunsu, za su fitar da su daga cikin garin Makka su da iyalan su matukar dai suka yi Imani da annabin rahama (s.a.w.a). shi ne alkur'ani yake basu amsa: Shin karfin ikon ubangiji shi ne ya fi ko kuma na shugabanin kuraishawa? Ubangijin da ya hore muku ni'imarsa mababbanta kuma ya sanya muku tsaro a garin Makka, shin ba shi da karbin da zai kare ku a game da mushrikai? Duk da cewa a farko musulinci, wadanda suka bada gaskiya suka kuma Imani da ma'aikin Allah (s.a.w.a) sun fuskanci cin mutunci da azabar mushirkai, amma da iradar Ubangiji, ko wata rana musulincin kara karfi yake har lokacin da suke iya buda garin Makka, suka kuma tabbatar da hukuncin musulinci a cikinsa.

Daga wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:

1-Da dama daga cikin wadanda suka ki yin Imani, saboda dadin Duniya ne kawai, ba wai don ba su fahimci gaskiya ba ne.

2-farko tsaro na ko wani irin al'amari, na karkashin tsaro da kwanciyar hankalin zamantakewa ne da kuma hakan yake samar da tattalin arziki, rayuwa da kuma ni'imomi, da kuma hakan ke tabbatuwa ta hanyar nema da aiki.

Yanzu kuma lokaci ne da za mu saurari aya ta 58 a cikin wannan sura ta kasas:

 

وَكَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ بَطِرَتْ مَعِيشَتَهَا فَتِلْكَ مَسَاكِنُهُمْ لَمْ تُسْكَن مِّن بَعْدِهِمْ إِلاَّ قَلِيلا وَكُنَّا نَحْنُ الْوَارِثِينَ

 

58-kuma da yawa al'umma da Muka hallakar wadda ta butulcewa rayuwarta. To ga gidajensu can ba a zaune sub a a bayansu saidai kadan,Muka kuma kasance Mu ne Magadan.

A cikin gaban ayoyin da suka gabata, wannan aya tana magana ne da mushrikan Makka tana cewa: ku saboda kare dukiya da jin dadin rayuwa, ba a shirye kuke ba ku bada gaskiya da Imani? Shi kun manta tahirin wasu mutane da suka gabace saboda yawan dukiya da kuma jin dadin duniya suka kaucewa hanya suka kuma hallaka? Shin a dauka ma kun samu dadin Duniyar to wani tabbaci kuke da shin a cewa ba za ku fada cikin ukubar Ubangiji ba? Kasashen Mutanan Aad da samud na kan hanyar tawagar 'yan kasuwan larabawa daga Makka zuwa birnin Sham, kuma wadannan mutane sun ga yadda gidajen wadannan al'umma da suka gabata yadda suka rushe, shin duk wannan bai isheku darasi ba?

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:

1-Dukiya da jin dadi, ba shi ke nuna farin cikin mutum ba, mai yiyuwa ma su kasance sanadin girman kai, dagawa da kuma hallakar mutum.

2-Barin al'adun mutanan da suka gabata, koyarwa ne ga mutum, domin haka, ya nada kyau, a kiyaye kayan tarihi na mutanan da suka gabata domin ya zamanto darasi da koyarwa ga masu zuwa.

3-Duniya mai karewa ce, kadda mu dubi rayuwar masu arziki, domin su ma za su bar dukiyarsu su fice.

*************************Musuc****************************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..