Suratul Qasas, Aya ta 59-63 (Kashi na 709)
Suratul Qasas, Aya ta 59-63 (Kashi na 709)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
----------------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 59 cikin wannan suratu ta Kasas.
وَمَا كَانَ رَبُّكَ مُهْلِكَ الْقُرَى حَتَّى يَبْعَثَ فِي أُمِّهَا رَسُولا يَتْلُو عَلَيْهِمْ آيَاتِنَا وَمَا كُنَّا مُهْلِكِي الْقُرَى إِلاَّ وَأَهْلُهَا ظَالِمُونَ
59-Kuma Ubangijinka bai zamanto Mai hallakar da alkaryu ba har sai ya aiko da Manzon a cikin manyan biranansu,yana karanta musu ayoyinmu. Kuma ba mu kasance Masu hallaka alkaryu ba, sai idan mutanansu sun zama azzalimai.
A shirin da ya gabata, cikin amsar da aka bawa wadanda saboda kare dukiyarsu da jin dadi Duniya ba shirye suke suyi Imani ba, Allah madaukakin sarki ya ce musu, ku dubi gidaje da suka lalace da mutanan da suka gabata, wadanda mutane kiyar milki ta kama su, kuma sun girman da dagawa a doron kasa, sai muka hallakar da su.
Wannan aya a matsayin sunar ubangiji a tsahon tarihi tana cewa, Allah ba ya hallakar da wata al'umma face ya aiko musu ma'aiki ya fada musu sakon Allah, idan suka ki binsa sai ya hallakar da su, duk al'ummar da aka aiko mana Ma'aiki, ya fada mata wahayi da sakon ubangiji, ta kalubanci ma'aikin Allah da addinin da ya zo da shi cikin zalinci, to tun a nan Duniya za ta fuskanci azabar ubangiji kuma za a hallaka ta.
Daga wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:
1-Idan Allah madaukakin sarki bai cika hujjarsa ba a kan mutane, to ba ya azabtar da su.
2-Karyata Ma'aika da Annabawa, da kuma kalubalantar gaskiya, babban zalinci ne da tun a nan Duniya ake sakawa.
Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun ayoyi na 60 da 61 cikin wannan aya ta kasas.
وَمَا أُوتِيتُم مِّن شَيْءٍ فَمَتَاعُ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَزِينَتُهَا وَمَا عِندَ اللَّهِ خَيْرٌ وَأَبْقَى أَفَلا تَعْقِلُونَ
60-Abin da kuma aka ba kun a kowane irin abu, to jin dadin rayuwar duniya ne da adonta, Abin da yake wurin Allah kuwa (shi) ya fi alhairi da kuma wanzuwa, Me ya sa ne ba kwa hankalta?
أَفَمَن وَعَدْنَاهُ وَعْدًا حَسَنًا فَهُوَ لاقِيهِ كَمَن مَّتَّعْنَاهُ مَتَاعَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ثُمَّ هُوَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنَ الْمُحْضَرِينَ
61-Yanzu wanda muka yi wa alakawari kyakkyawa sannan zai same shi, zai zama kamar wanda Muka jiyar dadin rayuwar duniya, sannan kuma shi yana daga wadanda za a kai wuta(a'a ba za su yi daidai ba).
Wadannan ayoyi suna bayyani ne kan amsar da Allah madaukakin sarki ya baiwa wadanda suka ki bada gaskiya da Imani saboda kare dukiyoyinsu da kuma jin dadin duniya, Allah madaukakin sarki na cewa shin kuna kallon abinda ke wurin Allah da abinda ke cikin wannan Duniya mai karewa abu guda ne da ba a shirye kuke ba ku neman abinda ke wurin Allah ta hanyar barin abinda ke cikin wannan Duniya mai karewa ba? Shin arziki da kuma ni'imomin duniya ya rufe muku ido da har ba za ku iya kokari ba wajen neman lahira ba?
Karshen aya ta 60 ta yi isharar cewa wannan aiki ne na marassa hankali, inda take aza aya tambaya shin ba za ku hankalta ba? Na'am wannan wani dan kwatamce ne ga duk wani mutum mai hankali bai kamata ya bar ni'ima dawammamiya ba, ya kama mai kare wa. Ci gaban ayar na kwatamta yanayin mutune na zahiri da kuma mutane na hakika wadanda suka yi Imani, ayar na cewa:wadanda a yau suka samu tabbaci da yakini da alkawarin ubangiji, suka kuma yi aiki saboda Allah,a ranar Alkiyama za su samu lada mai kyau daga wajen ubangiji.amma wadanda suka kwallafa zuciyarsu da wannan duniya mai karewa, ranar alkiyama, maimakon su samu ladan tsoron Allah, sai a dora musu zunubansu sannan kuma a kora su cikin wuta.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe uku kamar haka:
1-Ni'imar Duniya da lahira na Allah ne, mu kiyaye kadda ni'imar wannan duniya mai karewa ta zamanto sanadiyar haramta mana samun ni'imar lahira maras karewa
2-Alamar mai hankali shi ne kada a yi nutsu cikin wannan mai karewa kuma a seda lahira madawwamiya da duniya mai karewa, a maimakon mu yaudarun da rayuwar duniya ta zahiri, mu yi kokari wajen tunanin karshenmu, kadda mu yaudaru da dadin Duniya mu yi sakaci da rashin kula a neman Lahira.
3-amfani da kwatamce, tambayoyi a almari na kiran addini, da kuma isar da sako yana tayar da zukata kuma ya nada tasiri sosai.
Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun ayoyi na 62 da 63 cikin wannan sura ta kasas.
وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَائِيَ الَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ
62-Kuma (ka tuna) ranar da (Allah) zai kirawo su sannan Ya ce:"Idan abokan tarayya nawa wadanda kuka kasance kuna riyawa?
قَالَ الَّذِينَ حَقَّ عَلَيْهِمُ الْقَوْلُ رَبَّنَا هَؤُلاء الَّذِينَ أَغْوَيْنَا أَغْوَيْنَاهُمْ كَمَا غَوَيْنَا تَبَرَّأْنَا إِلَيْكَ مَا كَانُوا إِيَّانَا يَعْبُدُونَ
63-Sai wadanda fadar (alkawarin Allah na azaba) ya tabbata a kansu suka ce: 'Ya Ubangijinmu, wadannan da muka batar, mun batar da su ne kamar yadda mu ma muka bata, muna neman kubuta zuwa gare ka, don kuwa bas u kasance suna bauta mana ba.
Wadannan ayoyi suna ishara ne a kan yanayin mushirikai a ranar Lahira, suna cewa wadannan za su tashi ranar lahira ba tare da wani taimako ko mai taimako ba da kuma wani wurin buya ba, a wannan khidabi na Allah madaukakin sarki, an ce wadanda kuka sanya su abinda bauta a Duniya kuma suna tafiyar da al'amuran rayunku yanzu ina suke su tsuratar da ku? Ci gaban ayoyin na cewa shugabanin kafirai da mushirikai da suka kasance abin koyi da bautar mutane a duniya za a zo da su a lahira, su kuma za su bayar da amsa kamar haka, wadannan suna da'awar cewa sun meka wuya a garemu kuma suna bauta mana, a hakikanin gaskiya ba haka ba ne, sun kasance suna bin son ransu ne kawai, kuma domin cimma bukatun ransu, sai suka bi bayanmu saboda mu mun bata, domin haka mu ba abin bautarsu ba ne, muna neman tsari da su.
Yadda wadannan ayoyi suka siffanta kotun Alkiyama, tana kama da kotun Duniya a yayin da aka kamo mai laifi da abokanin satarsa ko ta'addancinsa, ko wane daga cikin su zai yi kokarin dora laifin bisa dan'uwansa, ya kuma nuna shi bas hi da laifi,masu laifi na cewa wasu ne suka yaudare mu har muka fada cikin wannan hanya, wadanda ake zarkin su ma suna cewa kada ku dora mana laifi, saboda ku da kanku ne kuka yi dagawa da girman kai har kuka bata, a bayyane yake wannan da'awa ba za ta samu karbuwa ba a kotun adalci ta ubangiji, masu laifi za su hadu da sakamakon ayyukansu.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu Kaman haka:
1-Tunani na samuwar wasu da suke a matsayin ubangiji ko abin bauta,rageggen tunani ne da kuma hasashe da ya nisanta daga hakika.
2-Duk wanda ya riki abin bauta koma bayan Ubangiji, a ranar Alkiyama zai hadu da azaba mai tsanani.
3-Mutanan da suka yaudari kansu kuma suka bata, to nema suke su batar da wasunsu.
4-Ranar Alkiyama, Shugabanin bata da mabiyansu, ko wane nema daga cikin su nema yake ya wanke kansa to amma hakan babu wani amfani da zai yi musu, dukkaninsu za a hada a kora su cikin wuta.
*************************Musuc****************************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..