Oct 20, 2017 14:07 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 64-69 (Kashi na 710)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

----------------------------------------

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 64 cikin wannan suratu ta Kasas.

 

وَقِيلَ ادْعُوا شُرَكَاءَكُمْ فَدَعَوْهُمْ فَلَمْ يَسْتَجِيبُوا لَهُمْ وَرَأَوُا الْعَذَابَ لَوْ أَنَّهُمْ كَانُوا يَهْتَدُونَ
 

 

64 Kuma aka ce "ku kirawo abokan tarayyar naku" sannan suka kirawo su, sai ba su amsa musu ba, suka kuma ga azaba (suka rika burin) ina ma sun kasance shiryayyu.

A shirin da ya gabata, mun bayyana cewa a ranar Lahira Shugabanin kafirci da shirka za su juyawa mabiyansu baya, tare da cewa ba su suka batar da sub a, saidai kawai sun kira su , su kuma suka amsa, domin su bi su ne domin biyayya ga zukatansu, wannan aya na cewa ganin cewa mushirikai sun kasa ganin wadanda suke bautawa a duniya, sai a ce musu ku kira wadanda dangantasu da ubangiji ko kuma wanda kuke ganin sa a matsayin abin bauta domin su taimake ku, kuma su tsiratar da ku daga azabar wannan rana, saidai a bayyane yake, babu wata amsa da za su iya bayarwa, sai su kasance masu nadama suna cewa kaiconmu da mun yi Imani da shiriyar Ubangiji a Duniya, da ba mu kasance cikin wannan hali da kadaitaka ba a yau, da kuma ba mu kasance marassa kariya daga wutar jahannama ba.

Daga wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:

1-Duk wanda ya kasance yana bayan wani koma bayan Allah a nan Duniya, zai haramtu daga taimakon Allah a ranar Lahira.

2-Ranar Alkiyama ranar ce ta kaico da hasara ga wadanda suka kaucewa hanya da masu sabo, to amma minene amfanin hakan?

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun Ayoyoi na 65 zuwa na 67 a cikin wannan sura ta kasas.

 

وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ مَاذَا أَجَبْتُمُ الْمُرْسَلِينَ

 

65- (Ka tuna) kuma ranar da (Allah) zai kirawo su sannan Ya ce: Me kuka amsa wa manzanni (da shi ne)?

 

فَعَمِيَتْ عَلَيْهِمُ الأَنبَاء يَوْمَئِذٍ فَهُمْ لا يَتَسَاءَلُونَ

 

66-Sai abubuwan da za su fada suka bace musu a wannan rana, sannan (kuma) su ba sa tambayar ( juna).

 

فَأَمَّا مَن تَابَ وَآمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا فَعَسَى أَن يَكُونَ مِنَ الْمُفْلِحِينَ

 

67-Ta amma wanda ya tuba ya ba da gaskiya ya kuma yi aiki na gari, to ana kaunar ya zama cikin marabauta.

A cikin gaban ayoyin da suka gabata da suke bayyani kan halin Mushirikai da kafirai a ranar alkiyama, wadannan ayoyi na cewa: za a tamabayi mushrikai da kafirai ranar alkiyama, dangane da kiran annabawa da ma'aika wata amsa suka bayar? Shin annabawa da ma'aika bas u kira ku ba zuwa ga bautar Allah guda da kuma aikata ayyuka na gari? Wata amsa kuka basu? Sanannan abu ne mushirikai da kafirai bas u da wata amsa da za su iya bayarwa dangane da wannan tambaya, idan suka ce mun amsa kiran Annabawa da ma'aika, kuma mun yi Imani, wannan karya ce babba,kuma a ranar alkiyama karya ba ta da masaya, idan kuma suka ce mun karyata su, mun kuma kira su da bokaye, masu tsafi, mahaukata,mun kalubalance su har ma mun yake su, to kaka da bakunansu, sun amince da laifinsu, kuma sun sayar da kansu, duk dai abinda za su fada, hasara ce a gare su,domin ba za su iya tserewa wadannan tambayoyi ba, kuma ba za su iya bayar da amsar tambayoyin ba ko kuma su z o da wani uzuri ba, wata babbar matsala a nan kuma ita ce a wannan rana bas u iya kebewa wurin guda ba domin yin shawara domin bayar da amsar wadannan tambayoyin ba.

Ci gaban ayoyin na cewa mushirikai da kafirai a wannan rana sun kai makura, bas u da mafuta, domin a duniya ba a rufe musu hanya ba, saboda a ko wani lokaci suna iya tuba, su kuma Imani da Ma'aikan Allah madaukakin sarki, su kuma aiki na gari su kasance daga cikin masu rabo, wanda kuma da sun aikata hakan da ba su jarabtu da wannan azaba ba.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:

1-A Kotun Lahira, mushirikai da kafirai ba, ba su da amsa dangane da dalilan da ya sanya su riki goma bayan Allah wajen bauta a nan duniya, kuma ba su da amsar da za su bayar a kan dalilin da ya sanya suka karyata Ma'aika da annaban Allah.

2-A ranar Lahira babu wata hanya da isar da sako, kuma mutane ba za su iya yin shawara da kuma tambayar juna tsakaninsu da masu irin tunaninsu, ta yadda za su iya shirya amsar tambayoyi na kotun adalci ta ubangiji.

3-Addinin musulinci bai rufe kofar tuba ba ga masu sabo da mushirikai, duk lokacin da suka niyar tuba, kofar musulinci a bude take, duk lokacin da mushirikai da kafirai suka so shiga da kuma komawa a kan fitiransu, to kofar musulinci  a bude take.

4- Gaskiyar mutum tana tabbatuwa ne wajen barin sabo da munanan ayyuka tare da aikata kyawawen ayyuka.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun ayoyi na 68 da na 69 cikin wannan sura ta Kasas.

 

وَرَبُّكَ يَخْلُقُ مَا يَشَاء وَيَخْتَارُ مَا كَانَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ سُبْحَانَ اللَّهِ وَتَعَالَى عَمَّا يُشْرِكُونَ

68-Kuma Ubangijnka Yana halittar abin da yake so, yana kuma zabar (abin da yake so), ba su suke da zabi ba.Tsarki ya tabbata ga Allah, ya kuma daukaka daga abin da suke tara (shi da shi).

 

وَرَبُّكَ يَعْلَمُ مَا تُكِنُّ صُدُورُهُمْ وَمَا يُعْلِنُونَ

 

69- Kuma Ubangijinka Ya san abin da zukatansu suke boyewa da kuma abin da suke bayyanawa.

A karshen wannan bangare na wadannan ayoyi, cikin amsar da kur'ani ya baiwa mushirikai dangane da cewa shin sun taka wata rawa game da hallitar Ubangiji, ko samar da duniya, yana mai cewa,Ubangiji shi ne yake hallitar abinda yake so, kuma ta yaya yake halittunsa, shin wanene ya tayar da Annabawa, kuma wanene ya sanya dokoki na shara'a ga mutane? Babu wani mutum ko wani da zai iya sanya ubangiji yayi wani aiki, ko kuma ya hana shi aikata abinda yake so ba. A cikin iradar ubangiji ya halicci mutum mai 'yanci a kan hanyar da yake so ya bi, amma mafi yawa zabin mutane ya sabawa zabin ubangiji, saboda halittu iradar ubangiji ne.a cikin al'amuran rayuwa, babu wani mutum da yake da hannu a halittarsa da kuma halittar wani, haka zalika a al'amuran shari'a, da Ubangiji ya bukaci mutum aikata wani aiki ko barin wani aiki, da kuma hakan ya saba da bukatunsu, da sun kasance babu da wani zabi da suka aikata wani abu sabanin shari'arsa kamar yadda ya zo cikin suratu Ahzabi aya ta 36 :A yayin da Allah da ma'aikinsa ya zartar da wata doka, ga maza da mata muminai, ba su da wani zabi na aikata sabanin haka.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:

1-Halittar halittu, da kuma tadbirin al'amuransu, har ila yau sanya musu dokoki, da zaben Annabawa, Ma'aika da shugabani na shari'a, dukkanin wadannan ababe na hanun ubangiji.

2- Duk wanda ya tsaya a gaban dokokin mahalicci, ya zabi dokokin mutum mutum ya bar na mahalicci, a hakikanin gaskiya ya sanya dan adam abokin tarayyar ubangiji a bangaren dokoki.

*************************Musuc****************************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..