Oct 20, 2017 14:22 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 70-75 (Kashi na 711)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

-------------------------------------------

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 70 cikin wannan suratu ta Kasas.

 


وَهُوَ اللَّهُ لا إِلَهَ إِلاَّ هُوَ لَهُ الْحَمْدُ فِي الأُولَى وَالآخِرَةِ وَلَهُ الْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

 

70-Kuma shi Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai Shi, yabo ya tabbata a gare shi a Duniya da Lahira,hukunci kuma nasa ne, kuma zuwa gare shi ne kawai za a komar da ku.

A shirye-shiryen da suka gaba ta, ayoyin alkur'ani da suka gabata sun kore yiwa Allah kishiya, ko kishiya a halitta, ko kuma kishiya a bauta, wannan aya tana ishara ne a kan tauhidi na rububiya tana mai cewa wani abin bauta  ya tara da ubangiji wajen saukar muku na ni'imarsa? Dukkanin ni'ima na zo muku ne daga gare shi, domin haka shi wanda ya caccanci ayi masa godiya, shi kadai ne mamallaki da mai hukunci a wannan Duniya da kuma lahira, bayansa wanene mai karfin bayar da umarni ga wannan halittu ko kuma mai irin wannan girma? A karshen rayuwa kuma a gare shi za a koma, bag a wasu abinda wasunku suka rika abinda bautawa bisa wani gurbataccen tunani.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:

1-Bauta ga shugaban da farko gami da karshen mutum da duniya a hanunsa yake kawai ta caccanta.

2-Hukuncin ubangiji na Takwini ga dukkanin halittu ne, kuma hukuncinsa na shari'a ga rayuwar dan adam ne,hakan kuma ya samo asali ne daga halitta, ko mallakarsa ga dukkanin halittu.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun ayoyi daga na71 na 73 cikin wannan sura ta kasas.

 

قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِن جَعَلَ اللَّهُ عَلَيْكُمُ اللَّيْلَ سَرْمَدًا إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَنْ إِلَهٌ غَيْرُ اللَّهِ يَأْتِيكُم بِضِيَاء أَفَلا تَسْمَعُونَ

 

71-Ka ce:" ku bani labari,(yanzu)Idan Allah ya sanya muku dare tutar har zuwa ranar alkiyama, wani sarki ne in ba Allah ba zai zo muku, da wani haske? To me ya sa ba kwa ji?

 

قُلْ أَرَأَيْتُمْ إِن جَعَلَ اللَّهُ عَلَيْكُمُ النَّهَارَ سَرْمَدًا إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ مَنْ إِلَهٌ غَيْرُ اللَّهِ يَأْتِيكُم بِلَيْلٍ تَسْكُنُونَ فِيهِ أَفَلا تُبْصِرُونَ
 

 

72- Ka ce:" ku bani labari,(yanzu)Idan Allah ya sanya muku rana tutar har zuwa ranar alkiyama, wani sarki ne in ba Allah ba zai zo muku da dare da za ku samu nutsuwa a cikinsa? To me ya sa ba kwa lura?

 

وَمِن رَّحْمَتِهِ جَعَلَ لَكُمُ اللَّيْلَ وَالنَّهَارَ لِتَسْكُنُوا فِيهِ وَلِتَبْتَغُوا مِن فَضْلِهِ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

 

73-Daga rahamarsa ne kuma ya sanya muku dare da rana don ku samu nutsiwa a cikinsa (watau dare)kuma don ku nema daga falalarsa (da rana), don kuma ku rika yin godiya.

Wadannan ayoyi suna ishara ne kan cikekken hukuncin Allah madaukakin sarki a kan halittu, suna masu cewa: idan Allah madaukakin sarki ya hana kasa juyawa, ta yadda muke yini a yanzu, har zuwa karshen Duniya haka za ta tsaya, kuma duk inda yake dare haka zai tsaya har zuwa karshen duniya, shin daga cikin ababen bautar da kuke bautawa akwai wanda zai iya sanya kasa ta juya, ya kuma raba Dare da Rana ga yankuna daban daban na Duniya?

Shin kun fahimci cewa juyawar Dare da rana babbar ni'ima ce a gareku da sauran halittu ma gaba daya? Idan haske da zafin rana, rabinsa ba isa zuwa ga kasa, yaya rayuwa za ta kasance, shakka babu rayuwar rabin kasa zai kai ga hallaka, kuma idan rabin doron kasa ya fuskanci matsalar haske da zafin rana, da dama daga cikin rayayyun halittu ba za su iya jurewa ba, za su hallaka, juyawa kasa shi ke sanadiyar jujuyawar Dare da Rana cikin tsarinsa na musaman kuma cikin gajeran lokaci, ko wane daga cikin sun a daukan wurin dan uwansa.

Duk da cewa Haske da zafin rana, wajibi ne ga rayuwar mutum da dukkanin halittu, duhun Dare, ragewar yanayin zafi ma, sare fage ne na futawar mutane da ma halittu da dama, wannan babbar ni'ima ce da mutane kadan suke hankalta da shi.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:

1-Kira zuwa ga karatun tsarin halitta da kuma Tsari gami da lissafin da tunani yadda aka yi halitta, na daga cikin mafi mahimancin hanyoyin sanin Allah da tauhidi, jujuwar kasa, da zuwa dare da rana na daga cikin alamomin kudirar Ubangiji.

2-An halicci Dare domin hutawa, ita kuma Rana saboda aiki da kokari.

3-A kokarin na shiryar da mutane, yin amfani da tambayoyi masu zaburar da mutum ya farka, ya nada kyau, ta yadda mutum zai farka yayi tunani game da gaskiyar musulinci.

4-Sanin ni'imomin, yak an sanya mutum ya godewa mahaliccinsa, mu yi kokarin sanar da ni'imomin ubangiji ga yaranmu da matasanmu, wanda ta hakan ne za mu kadaitar da su zuwa ga bautar Allah.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun ayoyi na 74 da 75 cikin wannan sura ta kasas.

 

وَيَوْمَ يُنَادِيهِمْ فَيَقُولُ أَيْنَ شُرَكَائِيَ الَّذِينَ كُنتُمْ تَزْعُمُونَ

 

74-Kuma ka tuna ranar da (Allah) zai kirawo su sannan ya ce:" Ina abokan tarayyar nawa wadanda kuka kasance kuna riyawa?

 

وَنَزَعْنَا مِن كُلِّ أُمَّةٍ شَهِيدًا فَقُلْنَا هَاتُوا بُرْهَانَكُمْ فَعَلِمُوا أَنَّ الْحَقَّ لِلَّهِ وَضَلَّ عَنْهُم مَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ

 

75-Muka kuma ware wani shaida daga kowacce al'umma (watau annabinsu) sannan Muka ce:"To ku kawo dalilinku (na yin tarayya da Allah) sannan Muka ce: "To ku kawo dalilinku (na yin tarayya da Allah), sannan suka san  cewa lallai gaskiya tana ga Allah, kuma abin da suka suka kasance suna kirkira ya bace musu.

Har ila yau Alkur'ani mai girma ya koma a kan tambayoyin da suka gabata cikin aya ta 62, yana cewa: wadannan da a duniya maimakon su bautawa Ubangiji suka bi bayan wasu mutane ko wasu halittu da suke tsamanin makomarsu da al'amuran rayuwarsu suna hannunsu, a Kotun lahira, za a yi musu tambayoyi dangane da dalilin da ya sanya suka ki amsa kirar ma'aikan Allah, dole suka kawo dalili mai gamsarwa da ya sanya suka yi Imani duk da cewa an aike musu Annabawa da Ma'aika wadanda suka sanar da su mahaliccin Duniya, amma duk da hakan suka yi watsi da su, suka bi,wasu ababe da suka kirkiro sannan suka bar gaskiya.

A cikin gaban ayoyin na cewa, a lokacin da kuka riki 'yar tsana a matsayin abin bautarku, alhali kun san cewa babu abinda za su iya muku, kuma gaskiya kawai na wurin Allah da ma'aikansa ne.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:

1-Tunatarwa ga ababen da su wakana ranar tashin alkiyama, gargadi ne ga mutane masu Imani a kan cewa hadari shirka abu na gaskiya, idan kuma baku kiyaye ba to kuna iya fadawa cikin wannan ibtila'I na hada wani da Allah.

2-Ma'aika da waliyan Allah na daga cikin shaidun kotun ranar Alkiyama, domin haka mu kiyaye a wannan kotu, kadda Ma'aikin Allah (s.a.w.a) yayi kuka da mu, saidai ya kasance mai cetonmu.

3-yin shirk aba ya shi da wani dalili mai karfi gami da irin dalilai da hujjojin da Annabawa suka gabatar.

4-A ranar Lahira, Bauta za ta koma bangare guda, gaskiya za ta bayyana da daukaka.

*************************************Musuc***********************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..