Oct 20, 2017 14:32 UTC

Suratul Qasas, Aya ta 76-78 (Kashi na 712)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

-------------------------------------

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 76 cikin wannan suratu ta Kasas.

 

إِنَّ قَارُونَ كَانَ مِن قَوْمِ مُوسَى فَبَغَى عَلَيْهِمْ وَآتَيْنَاهُ مِنَ الْكُنُوزِ مَا إِنَّ مَفَاتِحَهُ لَتَنُوأُ بِالْعُصْبَةِ أُولِي الْقُوَّةِ إِذْ قَالَ لَهُ قَوْمُهُ لا تَفْرَحْ إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ الْفَرِحِينَ
 

76-Hakika Karuna yana daga mutanan Musa, sai ya yi musu dagawa, muka kuma  ba shi daga taskoki(na dukiya), abin da makullansu suka zama kaya niki-niki ga tarin jama'a karfafa, yayin da mutanensa suka ce da shi: kada ka yi homa, hakika Allah ba ya son masu fariya.

A baya, ayoyin da suka gabata sun yi bayyani kan abinda ya wakana tsakanin annabi Musa (a.s) da Fur'auna,wannan aya kuwa tana ishara ne kan makomar Karuna da ya kasance daya daga cikin manyan masu kudi na zamanin annabi Musa (a.s), kamar yadda ya zo cikin tarihi Karuna ya kasance daga makusantan Annabi Musa (a.s) kuma da farko yayi Imani, amma daga baya sai dagawa da girman kai ya same shi sakamakon dukiyar da yake da ita, har zuwa wurin da ya tsaya a gaban Annabi Musa  ya kuma juya masa baya.

Fir'auna shi ne alama da kuma abin misali na mai karfin milki da ya kasance ya zalinci al'ummarsa, shi kuma Karuna shi ne abin misali na masu kudi da ya kasance mai alfahari kuma mai dagawa da ya tsaya da yake ganin kansa babba , ya kuma juyawa koyarwar gaskiya baya, shi kuma Samiri shi ne abin misali na fusaha, da yayi amfani da wannan fusaha wajen batar da mutane daga hanyar gaskiya, ya kuma kaisu zuwa bautar wanin Allah da bata.

Ci gaban ayar na cewa, tushen dagawa da tawayen Karuna, ya biyo bayan girman kai da ji-ji da kansa ne, duk lokacin da dukiyarsa ta karu, gafalarsa da kuma mantuwar da Allah na kara karuwa, kuma tunaninsa na kara jibke, dukiyarsa kama daga zinarai, lu'u'lu'u da jawahiri ke kara karuwa, alhali kuwa kamata yayi dukiya ayi amfani da ita wajen yiwa mutane hidima, kuma a sanya hanun jari a ko ina domin habbakar tattalin arzikin al'umma, ba wai wasu kalilan ba, su tare dukiya saboda kawunansu.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:

1-Dukiya da kuma kokari wajen tara dukiya ba laifi ba ne, amma kirman kai saboda duniya da kuma yiwa Allah da ma'aika gami mutane tawaye saboda dukiya, mumunan aiki ne.

2-maye kawai ba saboda shan kiya ba ne, wani lokaci mutanan da bas u da shi, da zarar sun samu kudi, ko kuma sun tara dukiya, sai maye da kirman kai ya same su, su manta komai,irin wadannan mutane da zarar da rabu da wani karfi na milki da dukiya, za su fice iyaka a kan hakkokin wasunsu.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun aya ta 77 cikin wannan sura ta kasas.

 

وَابْتَغِ فِيمَا آتَاكَ اللَّهُ الدَّارَ الآخِرَةَ وَلا تَنسَ نَصِيبَكَ مِنَ الدُّنْيَا وَأَحْسِن كَمَا أَحْسَنَ اللَّهُ إِلَيْكَ وَلا تَبْغِ الْفَسَادَ فِي الأَرْضِ إِنَّ اللَّهَ لا يُحِبُّ الْمُفْسِدِينَ
 

 

77-"Kuma ka nemi gidan Lahira ta hanyar abin da Allah Ya ba ka, kada kuma ka manta rabonka na duniya, kuma ka kyautata kamar Allah ya kyautata maka,kada kuma ka nemi yin barna a bayan kasa, hakika Allah ba ya son masu barna.

Ayar da ta gabata ta yi ishara a kan cewa wani gungu daga mabiyan Annabi Musa (a.s) da suka kasance masu fahimta da kuma kyakkyawan fata, a maimakon su kaskantar da kansu su girmama karuna,ba tare da wani fargaba ba suna yi wa Karuna nasina suna ce masa ka kiyaye kadda dukiya ta rudeka ta sanya ka girman kai, da dagawa, ka zamanto daga cikin mutanan da Allah zai yi fishi da su, irin wadannan  mutane ba sa son masu kudin da kudiyarsu ta sanya su girman kai da dagawa.

Wannan aya, a cikin gaban ayar da ta gabata, ta Ambato nasihohi guda hudu daga bakin muminai masu tunanin karshen al'amura, muhimiya daga cikinsu ita ce duniya manomar Lahira ce, idan a nan ka shibka abu mai kyau, z aka girbe shi a Lahira,wannan tarin dukiya da arziki, tana a matsayin misalin kwaya, da dole ka shibkata a cikin wannan duniya idan kana so ka girba a can,nasiha ta biyu kuwa, idan aka ce ayi guzirin lahira da dukiyar da ake da ita a nan duniya, ba a na nufin ka manta da rayuwar duniya ba ne, ka rabe dukkanin dukiyarka ta hanyar Allah, a'a ka yi amfani da dukiyarka domin yin rayuwa mai kyau kai da iyalanka, saidai abinda ake nufi shi ne, ka kasance mai tunanin Duniya da Lahira, dukkanin abinda kaka ya dace da kuma wurin da kaka ya dace wajen amfani da dukiyarka wajen ci gaban rayuwarka ta Duniya da kuma rayuwar lahira ka yi amfani da ita.

Nasiha ta uku, ita ce kadda kayi tunanin cewa wannan dukiya dake gare ka, karfin ka ne ya baka, ka yi tunanin cewa dukkanin wannan dukiya ta Allah ce kuma amana ce ya baka, domin haka ka kasance wakilin ubangiji wajen rabawa mabukata.

Nasiha ta hudu kuma ita ce masu Imani suka gyayawa Karuna, idan ba ka dauki wadannan nasihohi ba, dukiyarka ta zamanto sanadiyar fasadi a tsakanin al'umma, a maimakon ta kasance sanadiyar gyaran al'umma to ka sani cewa hakan zai sanya ka zamanto makiyin wannan al'umma, kamar yadda yake a yanzu masu kudi su kan sanya hannu jari a bangunan, wasu suna wahala su kuma suna kara zama masu kudi.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:

1-manufar mutum ga dukkanin ayyukansa, da kuma fanin tattalin arzikinsa, wajibi ne ya kasance bisa samun yardar Allah a ranar Lahira, duk da cewa rayuwar mutum a wannan Duniya ya kamata ya tabbatar ta ita.

2-Wajibi ne mutum ya kasance ya yi tunanin Lahirarsa, a daidai lokacin da yake amfana da Duniya, ma'ana mutum ya ware bukatunsa na rayuwa shi da iyalansa, abinda ya rage yayi amfani wajen Tarawa a Lahira.

3-Kudi da Dukiya,idan an yi amfani da su domin neman lahira, kamar ayyuka masu da kyautatawa, na iya zama fage na samun farin ciki da rayuwa mai kyau ga mutum na har abada.

Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun aya ta 78 cikin wannan sura ta kasas.

 

قَالَ إِنَّمَا أُوتِيتُهُ عَلَى عِلْمٍ عِندِي أَوَلَمْ يَعْلَمْ أَنَّ اللَّهَ قَدْ أَهْلَكَ مِن قَبْلِهِ مِنَ الْقُرُونِ مَنْ هُوَ أَشَدُّ مِنْهُ قُوَّةً وَأَكْثَرُ جَمْعًا وَلا يُسْأَلُ عَن ذُنُوبِهِمُ الْمُجْرِمُونَ
 

 

78-Ya ce:Ai ni an ba ni ita (watau dukiyar) ta hanyar ilimin da nake da shi ne Shin yanzu bai sani ba ne cewa hakika Allah ya hallaka wasu al'ummun da suke a gabaninsa wadanda suka fi shi karfi da kuma yawan tarin (dukiya)?Ba kuwa za a tambayi kafirai game da laifukansu ba.

Wannan aya na ishara kan amsar da Karuna ya bawa muminai, a maimakon ya karbi nasihohin da suka yi masa, cikin tagawa da girman kai sai ya ce: wannan kudi da dukiya da kuke gani, na same ta ne saboda ilimi na da kokarina, domin haka, ni ke da hakki in yi abinda naga dama da ita ba ku ba,da za ku zo kuce min ka yadda zan yi da ita, ni da kaina na san yadda ya kamata in kashe ta kuma na san wurin da zan boye ta, idan Ubangiji ya bani wannan dukiya, ya bani ne saboda ilimi da kuma kokarina kuma ya gay a dace ya bani ne domin haka ne ya bani.

Alkur'ani ya bayar da amsa game da wannan gurbatacen tunani ya ce: shin wai bai karanta tarihin mutanan da suka gabata ba ne, bai san cewa mutanan da suka fi shi karfin milki ba da kuma yawan dukiya saboda ba saboda sun juyawa gaskiya baya, sun yi dagawa,mun hallaka su, su da dukiyarsu tun a nan duniya.

Daga wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:

1-Dukiya, ko da kuwa kokarin da ilimin mutum  ya sanya ya same ta, to kadda ta sanya shi dagawa da girman kai gami da gafala, kuma wajibi ne mutum ya san cewa kyatatawar Ubangiji ne.

2-Girman kai saboda ilimi, milki, ko dukiya yak an sanya mutum ya hallaka tun a nan Duniya.

*************************************Musuc***********************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..