Suratul Qasas, Aya ta 79-82 (Kashi na 713)
Suratul Qasas, Aya ta 79-82 (Kashi na 713)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
-------------------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 79 da na 80 cikin wannan suratu ta Kasas.
فَخَرَجَ عَلَى قَوْمِهِ فِي زِينَتِهِ قَالَ الَّذِينَ يُرِيدُونَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا يَا لَيْتَ لَنَا مِثْلَ مَا أُوتِيَ قَارُونُ إِنَّهُ لَذُو حَظٍّ عَظِيمٍ
79-Sai ya fito wa mutanensa a cikin adonsa, sai wadanda suka burin rayuwar duniya suka ce:Ina ma da za mu mallaki irin abin da aka bai wa karuna? Hakika shi mai babban rabo ne."
وَقَالَ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ وَيْلَكُمْ ثَوَابُ اللَّهِ خَيْرٌ لِّمَنْ آمَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا وَلا يُلَقَّاهَا إِلاَّ الصَّابِرُونَ
80-Wadanda kuwa aka bai wa ilimi (mai amfani) sai suka ce Kaiconku, ai ladan Allah shi ya fi alheri ga wanda ya ba da gaskiya, ya kuma yi aiki na gari. Ba kuwa wanda ake yi wa katari da shi sai masu hakuri.
A shirin da ya gabata mun bayyana cewa Karuna na daga cikin mabiya Annabi Musa (a.s), amma tarin dukiyarsa ya sanya shi girman kai da dagawa, ya juyawa gaskiya baya, ya kuma fita daga cikin wadanda suka yi Imani.
Wannan aya tana ishara ne game mumunar mu'amalar Karuna, mumunar mu'amalar da ake ganin irin ta a rayuwarmu ta yanzu, kaskantar da mutane saboda kudi da dukiya,irin wannan rayuwa nada matsaloli mababbanta, wani lokaci gina babban gida na alfarma zai kasance abin ban mamaki ga mutane, wani lokaci shiga babbar mota mai tsada, ana yawo da ita cikin burane , wani lokaci kuma shirya katafaran biki da za a kashe biyoyin kudi domin nuna kai, yak an zamanto israfi da sauransu.
Iran wadannan ayyuka shi ne masu kudi ke yi domin nuna kansu, irin wannan barna da israfi, shi ke sanya masu karamin karfi suna ganin kansu a matsayin wadanda suka rako mutane Duniya kuma suna yanke kauna daga wajen ubangiji, ko da ya yake masu ganewa daga cikin marasa karfi, sun san cewa rashin dukiya ba rashin wadata ba ne ba, kuma dukiya ita kadai ba ta kawo faricin ciki na hakika, da dama daga masu kudi suna fuskantar matsalolin da iyalansu, kuma dukiyarsa ba ta magance musu wadannan matsaloli ba, sai ma ta kasance musu sanadiyar tashin hanhali da ciyon zuciya.
Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:
1-tara dukiya ba matsala ba ne, to amma alfahari, nuna kai, da kuma yin adon da zai sanya wulakanta wasu da kaskantar da su, shi ne ba shi da kyau.
2-idan ya kasance mahunta su jarrabtu da irin zuciyar Karuna, hakan zai yi tasiri ga al'adun al'umma kuma ya kasance tana bautawa dukiya da kyalkyali.
3-bautar duniya, fatan mutane masu karamin tunani ne, ban a masu dogon tunani masu ganewa ba ne.
4-Dukkunin dukiyar duniya dangane da gidan Aljanna da ya kasance ladan tsarkakku da salihai ne ba komai ba ne, domin haka ya kamata mutane masu hankali da ganewa sun fadakar da mutane cewa su kuji kwallafawa ransu Duniya da kuma bautar kudi.
Yanzu kuma lokaci yayi da za mu saurari karatun ayoyi na 81 da 82 cikin wannan sura ta kasas.
فَخَسَفْنَا بِهِ وَبِدَارِهِ الأَرْضَ فَمَا كَانَ لَهُ مِن فِئَةٍ يَنصُرُونَهُ مِن دُونِ اللَّهِ وَمَا كَانَ مِنَ المُنتَصِرِينَ
81-Sannan Muka kifar da shi (Karuna) tare da gidansa cikin kasa, kuma ba shi da wata jama'a da za su taimake shi in ba Allah ba,kuma bai kasance daga masu cin nasara ba.
وَأَصْبَحَ الَّذِينَ تَمَنَّوْا مَكَانَهُ بِالأَمْسِ يَقُولُونَ وَيْكَأَنَّ اللَّهَ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاء مِنْ عِبَادِهِ وَيَقْدِرُ لَوْلا أَن مَّنَّ اللَّهُ عَلَيْنَا لَخَسَفَ بِنَا وَيْكَأَنَّهُ لا يُفْلِحُ الْكَافِرُونَ
82-Kuma wadanda suka yi burin matsayinsa a jiya suka wayi gari suna cewa :"wai yau mun ga abin al'ajabi!Allah yana yalwata arziki ga wanda yake so daga bayinsa, yana kuma kuntatawa ga wanda ya so, ba don Allah ya bamu sa'a ba da mu ma ya kifar da mu. Abin mamaki, hakika Kafurai ba sa rabauta."
Kaskanta mutane da kuma gwada masu shi mai dukiya ne, da kuma juyawa ma'aikin Allah baya bisa dalilinsa na cewa shi ba ya da wata bukata da lahira, aikin karuna ya kai wajen da Allah madaukakin sarki ya aiko da girgizar kasa mai tsanani wacce ta tafi da dukkanin abinda ya mallaka gami da shi Kasa, babu wani sakamako daga gare shi, ko da yake ayoyin kur'ani mai girma sun baya da labarin hallakar mutanan da suka gabata ta hanyar girgizar kasa.amma a wannan wuri, ana nufin Karuna da kuma gidansa gami da abinda ya mallaka suka hallaka karkashin kasa, ba tare da sauran mutane yayin aukuwar girgizar kasar.wannan kuma wata mu'izija ce ta daban da Allah madaukakin sarki ya gwadawa Bani-isra'ila kamar yadda aka hallaka Fir'auna wanda yake ganin kansa a matsayin mamallakin Masar da kuma ruwan Nilu, aka nutsar da shi a cikin ruwan, karfin sa da kuma milkinsa suka tafi a banza.
Mutanan gari da suka ga wannan mu'ujiza sai suka farka daga barci, kuma suka yarda cewa babu wani amfani ga masu fatan samun dukiya irin ta Karuna, domin komai a hanun Allah yake,kuma bisa ilimi da hikimarsa ne yake raba arziki a tsakanin al'umma.
Daga wadannan ayoyi za mu ilmantu da ababe guda hudu kamar haka:
1-karshen girman kai da dagawa, hallaka ce.
2-Dukiya, komin yawanta, ba wasila ba ce ta tsiratar da mutum daga azabar ubangiji.
3-da ganin wasu abubuwa, kadda mutum yayi saukin yanke hukunci, wadancan mutane da ganin dukiyar fir'auna sai suka yi fatan kasancewa kamar shi,amma bayan ganin karshen al'amarinsa, sai suka ce gaskiya hakan yayi kyau, da ba mu kasance kamar shi ba.
4-a maimakon muyi fatan samun dukiyar da aka baiwa wasunmu, mu wadatu da abinda Allah ya bamu, mu kuma san cewa abinda Allah ya bamu shi ne maslaha a garemu.
*************************************Musuc***********************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..