Suratul Qasas, Aya ta 86-88 (Kashi na 715)
Suratul Qasas, Aya ta 86-88 (Kashi na 715)
Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.
------------------------------------
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 86 a cikin wannan sura ta Kasas:
وَمَا كُنتَ تَرْجُو أَن يُلْقَى إِلَيْكَ الْكِتَابُ إِلاَّ رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ فَلا تَكُونَنَّ ظَهِيرًا لِّلْكَافِرِينَ
86-Kuma ba ka kasance kana zaton an saukar maka da Littafi ba, sai dai (an yi haka ne) don rahama daga Ubangijinka. To kadda ka zamanto mai taimakon kafirai.
A cikin ayar da ta gabata Allah madaukakin sarki ya yiwa ma'aikinsa (s.a.w.a) alkarin cewa bayan yayi hijra zuwa garin Madina, zai sake dawo da shi zuwa garin Makka, kuma zai yi galaba a kan kafirai,wannan aya mai albarka na bayyanin cewa kamar yadda a baya, ba ka da fatan komawa garin Makka cikin izza da karfi, to saidai haka Ubangijinsa ya nufa, kamar yadda baya tunanin cewa ba za a tayar da kai a matsayin ma'aiki kuma za a saukar maka da littafi daga sama, to amma Allah madaukakin sarki bisa hikimarsa, ya sanya ka cikin rahamarsa, ya kuma tayar da kai a matsayin ma'aikinsa. Domin kadda ka meka wuya ga bukatun kafirai da mushrikai, wanda hakan na iya zama taimaka musu. Ka kasance mai adawa da su kuma ka bayyana wa al'umma hakan.
A cikin ayoyin da suka gabata cikin wannan sura mun bayyana cewa Annabi Musa (a.s) ya je dutsun Duri domin kawowa iyalansa garwashin wuta, kuma a can ne ya samu matsayin ma'aikin Allah, a bangaren Annabin Rahama Muhamadu dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya zo cikin litattafan tarihi cewa, domin bauta ya na zuwa cikin kogon Hirra dake dutsan Noor, kuma a can mala'ika jibrilu ya sauka a gare shi sannan kuma ya bashin sakon Ubangiji madaukakin sarki, (watau Alkur'ani mai tsarki)
Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda biyu kamar haka:
1-daya daga cikin uzurin da kafirai suke bayarwa, menene ya sanya ba a saukar musu da wahayi ba, alkur'ani na cewa duk da irin tsarki da kamala na annabawa ba su tunani da shirin cewa ba wahayi sai sauka a gare su, ba ranta ma su kafirai!
2- A makarantar Annabawa da ma'aika, duk wani aiki ko wani abu da zai karfafa kafirai da Azzalimai, an haramta shi.
Yanzu kuma lokaci yayi da za mu sauraru karatun aya ta 87 cikin wannan sura ta kasas.
وَلا يَصُدُّنَّكَ عَنْ آيَاتِ اللَّهِ بَعْدَ إِذْ أُنزِلَتْ إِلَيْكَ وَادْعُ إِلَى رَبِّكَ وَلا تَكُونَنَّ مِنَ الْمُشْرِكِينَ
87-kuma lallai kada su hana ka (isar da) ayoyin Allah bayan an riga an saukar maka da su, kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma lallai kada ka zamanto daga mushrikai.
Wannan daya daga cikin misdakin ayar da ta gabata ce da take cewa kada kada ka goyi bayan kafirai, domin barin da'awa da kuma kira zuwa ga ayoyin alkur'ani, da kuma sako sako wajen kiran mutane zuwa tauhidi da kuma kadaita Allah, zai yi sanadiyar karfafa kafirai da mushrikai, a cikin litattafan tarihi ya zo cewa, duk lokacin da ma'aikan suka karantawa mutane ayoyin ubangiji kuma suka kira su zuwa sauraren kalaman Allah madaukakin sarki, sai ka ga makiya da kafirai suna kiran su da kuma zarkin cewa su mawaka ne, bokaye da kuma masu fadar tatsuniya, wannan aya na cewa ya kai annabi kadda ka shi tsoron tuhuma da kuma cin mutunci na makiya wajen isar da sakon ubangiji, idan kayi hakan, to z aka kasance kamar su kuma babu babbanci tsakanin ka da mushrikai a wajen ubangiji.
Daga wannan aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-makiyan addini suna kula makirci da makarkashiya ga addini har ma da annabawa da ma'aika, kuma ba sa sako-sako wajen watsa kafirci da shirka a tsakanin al'umma domin haka,ya zama wajibi mu iya namu kokari wajen kare addininmu da kuma kiran wasunmu zuwa ga addinin islama.
2-Ma'aikan Ubangiji suna karkashin tarbiyar ubangiji ne, kuma Allah madaukakin sarki na tunatar da su gami da umarni ko haninsa, ta yadda za su iya isar da sakon Ubangiji kamar yadda ya dace.
3-Ma'aika suna kiran mutane ne zuwa bautar Allah, ba zuwa gare su ba, domin haka ya kasance fada da shirka gami da kafirci shi ne sahun a shirin su.
Yanzu Lokaci yayi da za mu saurari karatun aya ta 88 cikin wannan sura ta Kasas
وَلا تَدْعُ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آخَرَ لا إِلَهَ إِلاَّ هُوَ كُلُّ شَيْءٍ هَالِكٌ إِلاَّ وَجْهَهُ لَهُ الْحُكْمُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
88-kuma kada ka bauta wa wani abin bauta daban tare da Allah, babu wani abin bauta wa da gaskiya sai shi,kowane abu mai hallaka ne sai zatin sa kawai(watau Allah) Hukunci (duk) Nasa ne, domin kuwa gare shi za a komar da ku.
A cikin ayar da ta gabata Allah madaukakin sarki ya umarni annabawansa da kadda su yi sanya wajen kiran mutane zuwa ga gaskiya da kuma addinin musulinci, ci gaban wannan aya kuwa na cewa kada ko wani mutum dake kiran kansa a matsayin mai addini ya yiwa Allah kishiya wajen bauta, domin komai na duniya koma bayan Allah mai karewa ne,Allah ne kawai zai yi saura, kuma duk wani aiki da za ayi cikin ikhlasi saboda Allah, kuma bayan haka komai na Duniya da hallitu na karkashin milkinsa ne, domin haka bautar wanin Allah ba ta da wata ma'ana. A cikin wannan aya an bayyana cewa duk wata hallita ta duniya mai karewa ce, da wannan dalili komai na duniya kusa ko nesa zai kawar, da wannan dalili,a halin da ake cikin duk wanda yake same to samuwarsa ba daga gare shi ba ne, yana karkashin rahamar ubangiji ne, kuma duk lokacin da ta gushe a gare shi zai kawar.
Ayar da ta gabata tayi ishara game da shirka, ita kuma wannan aya ta bayyana shirka da wannan ma'ana, duk wanda ya kira wani a matsayin ubangiji,sabanin akidar wahabiya dake cewa tawasalli da annabawa ga waliyan ubangiji shirka ne,a hakikanin gaskiya tawassali da annabawa gami da waliyan Allah ba shirka ba ne, domin babu wani mutum da ke ganin cewa Annabawa da waliyan Allah msu tsarki su nada wani karfi ko kudira kabebbiya ba daga Allah ba,saidai wadannan bayin Allah mutane masu girma da suka bayar da rayuwarsu wajen yada addinin islama da kuma jihadi.
Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da ababe guda uku kamar haka:
1-mai bautar Allah na gaskiya, 'yantattu ne daga shawarwaru na halittu, kuma game da daguru, da masu milkin da suke ganin sune masu milki a doron kasa, kuma suna so su mallaki kowa da kowa a doron kasa masu gwagwarmaya ne da juriya.
2-Duniya da abinda ke cikin ta mai karewa ne a gaban Allah da kuma addinin Allah .
3-mutuwa, ba ta nufin hallaka da karshen rayuwa, saidai komawa ce zuwa ga farkon halitta.
*************************************Musuc***********************************
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..