Oct 22, 2017 07:03 UTC

Suratur Rum, Aya ta 1-8 (Kashi na 730)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

---------------------------------

To madallah to masu za mu fara shirin na yau tare da sauraren ayoyin farko a cikin suratun Rum bayan da a makon jiya muka kawo karshen ayoyin da ke cikin suratun ankabut kuma a yau za mu fara da sauraren aya ta 1 zuwa aya ta 5.

 

الم

1. ALIF LAM MIM. Allah ne Ya san abin da Yake nufi da wannan.

غُلِبَتِ الرُّومُ

2. An yi galaba a kan Rumawa.

في أَدْنَى الأَرْضِ وَهُم مِّن بَعْدِ غَلَبِهِمْ سَيَغْلِبُونَ

3. A cikin kasa mafi kusa da su ,su kuma da sannu za su yi galaba a kan Farisa bayan galabar a kansu.

 

فِي بِضْعِ سِنِينَ لِلَّهِ الأَمْرُ مِن قَبْلُ وَمِن بَعْدُ وَيَوْمَئِذٍ يَفْرَحُ الْمُؤْمِنُونَ

 

4. A cikin yan tsirarin shekarun da bas u kai goma ba.Al'amari gaba da baya na Allah ne,a wannan ranar ne muminai za su yi farin ciki.

 

بِنَصْرِ اللَّهِ يَنصُرُ مَن يَشَاء وَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ

 

5. Da samun nasarar Allah a kan Farisa, Shi Yake taimakon wanda yake so ,domin kuwa Shi ne Mabuwayi Mai rahama.

 

Ya zo a cikin littafan tari daulolin Roma da Na Iran sun yi ta gabza fada da yake yake da gaba mai tsawo har zuwa lokacin da manzon Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa a birnin Makka sun ci gaba da yake yake a tsakaninsu.A wani yaki da suka gobza wato daular Roma da daular Farisa a yankin  Jazirar larabawa kuma a wannan yaki Romawa sun sha kasha a hannun Farisawa. Bayan wannan nasara kan Romawa ,Allah ya bawa manzonsa labarin cewa;bayan wannan kasha da romawa sun sha  a yakin da za a gobza a gaba za su yi nasar tabbas.Wannan wani labara da ya shafi  wani abu na boye da zai wakana a nan gaba kuma ya tabbata.don haka muminai sun samu nucuwa alkawalin yin nasara kan matsaloli da takurawa da manzon Allah (SWA) zai tabbata saboda komi da kowa yana hannun Allah ne kuma duk abin da yake so ne ke tabbata da zartarwa kuma rahama da daukaka tasa ce.

Wadannan ayoyi na koyar da mu wasu abubuwa guda uku kamar haka:

Na farko:labarin abin da yake boye da wakana a nan gaba da kuma tabbatar wannan lamari na nuni da mu'ijizar wannan littafi mai girma da daukaka.

Na biyu: mu sani da fahimtar cewa: idan yau an yi nasara a kanmu wata rana za mu yi nasar da neman taimakon Allah.

Na uku:Duk wani aiki da Allah ya zartar yana karkashin hikima ne.Nasara ko akasin ta ga ma'abuta imani yana karkashin hikima ne ta Allah.a kullum mumini yayi aiki da nauyin da ya rataya a kansa amma sakamako yana gurin Allah ne.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 6 da ta 7 a cikin wannan sura ta rumu.

 

وَعْدَ اللَّهِ لا يُخْلِفُ اللَّهُ وَعْدَهُ وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لا يَعْلَمُونَ

6- Wannan alkawarin Allah ne. Allah ba Ya saba alkawarinsa ,sai dai kuma yawancin mutane bas u san haka ba.

 

يَعْلَمُونَ ظَاهِرًا مِّنَ الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَهُمْ عَنِ الآخِرَةِ هُمْ غَافِلُونَ
 

7- Suna sanin abin da yake a sarari na rayiwar duniya ne,alhali kuwa su marafkana ne game da lahira.

 

Ayoyin da suka gabata suna Magana ne kan alkawalin cin nasara da muminai za su yi kan mushrikai to wadannan ayoyi da muka saurara na cewa ne:yak u mutane kar ku yi shaku a cikin alkawalin Allah domin tabbas Allah mai cika alkawalinsa ne da zartar da abin da yak e so. Amma wadanda bas u yi imani da Shi b aba su dogaro da alkawalin Allahko samin nucuwa saboda bas u da masani da ilimi cikin kudura da hikimar allahkawai su abin da suke gani zahirin lamari da cin nasara ko aksin hakan ta hanay ma'aunin zahirin rayuwa ,dalili sun shagaltu da rayuwar lahira da takaita gani da tunaninsu a wannan duniya da haramtawa kansu sanin hakikanin rayuwa.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

 

Na farko:tunanin Allah ya saba alkawalinsa yana daga cikin raunin imani da jahilci.

 

Na biyu:rungumar wannan duniya da rayuwar cikinta alama ce da karamcin tunani na mutum.

 

Na uku:Tushen shagaltuwa da wannan duniya da kuma sha'afa da ranar lahirayana daga cikin mika wuya da rayuwar wannan duniya ne.

 

To madallah daga karshe za mu rufe shirin na yau ne da sauraren karatun Aya ta 8 a cikin wannan sura ta Rumu.

 

أَوَلَمْ يَتَفَكَّرُوا فِي أَنفُسِهِمْ مَا خَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلاَّ بِالْحَقِّ وَأَجَلٍ مُّسَمًّى وَإِنَّ كَثِيرًا مِّنَ النَّاسِ بِلِقَاء رَبِّهِمْ لَكَافِرُونَ
 

 

8- Yanzu ba su yin tunani a kan kansu? Allah bai halicci sammai da kassai da abin da yake tsakaninsu ba sai a kan gaskiya da kuma zuwa lokaci kayyadajje,Hakika mafi yawan  mutane masu kafurcewa ne da haduwa da Ubangijinsu.

Wannan ayar kamar sauran ayoyi da daman a kur'ani da ke kiran mutum da yay i tunani da nazari a cikin tsarin halitta da tafiyar da lamarin wannan duniya  da kuma yin lissafi da nazari a cikin halittar shi kansa da tambayar kansa wane ne a hakika ya halicci sammai da kassai? Shin haka kawai babu wani haddafi aka halicci wannan duniya? Shin wannan duniya ba ta da farko da karshe ne? Ko kuwa shi mutum kominsa yana tafiya cikin tsari da lissafi amma ita wannan duniya an samar da ita haka kwacam  babu tsari duk girmanta amma shi mutum yana da tsari?. Shin za mu amince rayuwar mutum a wannan duniya tana da karshe amma ita wannan duniya ba ta da karshe ko wata duniyar ba wannan ba?.  Haka ne da dama daga cikin mutane  da suka rungumi rayuwar wannan duniya  sun sha'afa da ranar kiyama da yadda za mu samu kanmu a gaban babbar kotu da alkalinta Allah ne mafi adalci da hukumci kan gaskiya ba tare da an tauyewa wani hakkinsa ba ko fargabar hakan.Amma su wadanda suka yi imani da hangen nesa  da zurfafa tunani  na rayuwa a wannan duniya cikin tsari da tafarkin gaskiya domin sun san wannan duniya tana karkashin tsari da buri ne kuma Allah ya halicci wannan duniya da abin da ke cikinta cikin hikima da tsari.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da fahimtar abubuwa uku kamar haka:

Na farko:addinin musulunci na gayyatar mutane zuwa ga yin tunani da nazari a cikin halittar wannan duniya domin imaninsu ya kasance karkashin ilimi da masaniya da hujja.

Na biyu; duk halitta tana karshin tsari da buri da lokaci na faraway da na karshenta.

Na uku: Musanta ranar kiyama bay a karkashin  nazari da hujja ta hankali sai dai bakar jayayya.

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags